Zargi: Wani mai amfani da shafin Tiwita ya wallafa hoton wani gidan kaji cike da ruwa ya na zargi wai lamarin ya afku a jihar Legas din Najeriya
Wannan hoton ya fara bulla ne a wani shafin intanet da ke kasar Bolivia ranar 26 ga watan Afrilun 2021. Dan haka ba shi da wata alaka da ambaliyar jihar Legas
A shafin Tiwita, TrackaNG ya wallafa hotunan titin Herbert Macauly da ke garin Yaba a Legas. Wannan ne ya yi sanadiyyar da wasu su ma suka fara raba hotunan yadda ambaliyar ta shafi yankunan su. Wani mai amfani da shafin da sunan Larry(@doplarry) ya wallafa wani hoton da ke nuna yadda ambaliyar ta shafi wani gidan kaji yana zargi wai gidan kajin a Legas ya ke.
“Gidan kajin wani a Legas” ya rubuta.
Wani mai amfani da shafin Tiwita TheDavidOyebode (_Daevids) korafi ya yi ya na cewa “Omooo wannan ko daya babu kyau,” ya ce
Wani kuma, I am_Grant (daikman_1) ce wa ya yi “Kai… wannan abun tausayi ne.”
Sai dai akwai wanda ya karyarta zargin cewa jihar Legas ne
“Wannan ba Legas ba ne, wannan tsohon hoto ne kuma ba a Legas abun ya faru ba,” a cewar Olarenwaju (@jimiroye1)
An sake sanya hoto makamancin wannan a shafin Facebook a wani shafi mai suna Senior Man, wanda shi ma ya ke zargin wai a Legas ne ruwa ya shiga gidan kajin. Wadannan bayanai mabanbanta da yadda hoton ya dauki hankali ne ya sa DUBAWA ke neman tantance labarin.
Tantancewa
DUBAWA ta fara da tantance hoton da manhajan tantance hotuna. Daga nan ne mu ka gano cewa hoton ya dade a yanar gizo, tun 2021 aka fara wallafa shi a wani shafin kasar Bolivia mai suna Los Tiempos. Shafin ya yi amfani da hoton a wani labarin da ya bayyana yadda dakarun Bolivia su ka kwashe iyalai 30 daga yankunan da ambaliyar ta shafa a yayin da wasu amfanin gona a hektoci dubu biyu kuma su ka lalace sakamakon yawan ruwan saman da ambaliya a kananan hukumomin Chimoré da Villaroel, a Bolivian ranar 26 ga watan Afrilun 2021.
Hoton ya sake bayyana a wani shafin na Facebok mai suna Konkosah GH inda nan kuma ake zargi wai wata gonar kajin ne a Kumasi Ghana, shi kuma wannan hoton ya bulla a shafin 25 ga watan Yuni 2021.
A Karshe
Hoton da ake magana a kai ya fara bulla ne a shekarar 2021 kuma yana nuna wadansu yankuna a kasar Bolivia ne inda aka yi fama da ambaliya. Wannan hoto ba shi da wani dangantaka da ambaliyar da aka yi a Legas, dan haka wannan zargin karya ne.