|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Wani bidiyo da ke yawo a Facebook ya yi ikirarin cewa Ministan Tsaron Nijeriya, Christopher Musa, ya ce duk gwamnan jiha da ya shiga tattaunawa da ’yan bindiga to ɗan ta’adda ne, kuma za a janye sojoji daga wannan jiha.

Hukunci: Ƙarya ce. Bidiyon ƙirƙirar fasahar kwamfuta (AI) ne. Binciken DUBAWA bai samu wata shaida da ke nuna cewa Ministan Tsaro ya yi wannan magana ba.
Cikakken Bayani
A shekarar 2025, wasu gwamnonin jihohin Najeriya, musamman a Katsina da Kaduna, sun ƙulla yarjejeniyar sulhu da ƙungiyoyin ’yan bindiga, a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin dakile hare-haren ta’addanci, satar mutane, da matsalolin tsaro a yankunansu.
A lokaci guda kuma, hukumomin tarayya sun sha gargadin jihohi da ƙananan hukumomi kan yin yarjejeniyar sulhu da ’yan bindiga, suna cewa irin wadannan tattaunawa na iya ƙarfafa ƙungiyoyin ta’addanci, raunana ayyukan tsaro na ƙasa, da kuma kawo cikas ga ƙoƙarin kawar da ’yan ta’adda baki ɗaya.
A daidai lokacin da ake wannan muhawara kan amfani ko illar sulhu, wani mai amfani da Facebook ya wallafa wani gajeren bidiyo (wanda aka adana) yana nuna tamkar Ministan Tsaro, Christopher Musa, na yin kakkausar magana kan tattaunawa da ’yan bindiga.
A cewar bidiyon, Janar Musa ya ce “duk gwamnan jiha da ya shiga tattaunawa da ’yan bindiga ko ’yan ta’adda, to shi ma ɗan ta’adda ne; za mu janye sojoji daga waccan jiha.”
Zuwa ranar Talata, 20 ga Janairu, 2026, an kalli bidiyon fiye da sau 720,000, da martani 14,000, da kuma sharhi sama da 1,200.
Yayin da wasu masu amfani a Facebook suka yi watsi da bidiyon suna cewa ƙirƙirar fasahar AI ne, wasu kuma sun yarda da shi a matsayin na gaskiya.
Khalifa Ashiru Danlinan ya ce: “Wannan AI ne.”
“Ba sai an gaya maka ba, a bayyane yake aikin AI ne” in ji Samaila Adamu.
Sai kuma Alo Stephen Jnr. da ya ce: “Idan giwaye biyu na faɗa, ciyawa ce ke shan wahala.”
Saboda mahimmancin batun tsaro da kuma sabani a ra’ayoyin jama’a, DUBAWA ta yanke shawarar binciken sahihancin bidiyon.
Tantancewa
DUBAWA ta gudanar da nazari na ido, kan kowane hoton bidiyon. Mun gano matsalolin da ake yawan samu a bidiyoyin da fasahar AI ke ƙirƙira.
Misali, an lura da wani mutum da ke sanye da hular gargajiya a bayan wanda ake cewa Ministan Tsaro ne, amma daga baya ya ɓace a wasu sassan bidiyon ba tare da wani dalili ba.

Hoto: Hotunan da ke nuna sabani
Haka kuma, an lura cewa wani mutum a gefen dama na Janar yana saye da hula a farko, amma daga baya aka nuna shi babu hular a kansa har zuwa ƙarshen bidiyon.

Hoto: Hotunan da ke nuna sabani
DUBAWA ta kuma saka bidiyon a na’urorin tantance bidiyon AI da aka ƙirƙira da salon ɓadda sawu.
Na’urar Deepware ta nuna cewa akwai kashi 30 cikin 100 na nuna yiyuwar bidiyon ƙirƙirar AI ne. Seferbekov kuma ta nuna yiwuwar bidiyon kashi 84 cikin 100 na AI ne.

Hoto: Sakamakon binciken Deepware da Seferbekov.
Wata na’ura mai suna Hive AI ta nuna cewa akwai yiyuwar kashi 94 cikin 100 na bidiyon an ƙirƙire shi ne da fasahar AI.

Hoto: Sakamakon binciken Hive AI.
Baya ga haka, DUBAWA ta gudanar da bincike ta kalmomin nema (keyword search) a shafin Google, manyan kafafen labarai na Nijeriya, da kuma kafafen sadarwa na Hedikwatar Tsaro ta Nijeriya.
Babu wani tabbataccen rahoto daga wata kafar labarai da ya nuna cewa Ministan Tsaro ya yi wannan magana. Duk da cewa Janar Musa ya sha gargadin jihohi kan yin sulhu da ’yan ta’adda, bai taba bayyana cewa gwamnonin da suka yi sulhu ’yan ta’adda ne ba.
A Ƙarshe
Bidiyon da mai amfani da Facebook ya yada ƙirƙirar fasahar AI ne. Saboda haka, ikirarin cewa Ministan Tsaro ya ayyana gwamnonin da ke tattaunawa da ’yan bindiga a matsayin ’yan ta’adda ƙarya ce.




