African LanguagesHausa

Hotunan da aka wallafa a sunan wai birnin Abuja ne da daddare na bogi ne

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: ATP hausa ta wallafa hotuna na Birnin tarayya Abuja masu daukar ido sosai  da da’awar a cikin dare a dauke su bayan kammala ruwan sama.

Hotunan da aka wallafa a sunan wai birnin Abuja ne da daddare na bogi ne

Hukunci: Karya ce! Babu wata hujjar ta tabbatar mana da cewar hotunan da ake yadawa a kafafen yada zumunta hotunan hanyoyin birnin tarayya ne. Su kan su masu yadawa basu bayyana tushen hotunan ba kumaba su bayar da sahihiyar asalin in da suka samo hotunan. Sai dai bincikenmu ya nuna mana inda suka sami hotunan suka yi gamin gambiza dan yaudarar jama’a

Cikakken Bayani

Wani shafi na facebook mai suna ATP Hausa ya wallafa hotuna da da’awar cewa titin Abuja ne, birnin tarayyar Najeriya wanda suka dauka bayan an kammala ruwan sama a ranar Litini 3 ga watan Yuni 2024 da daddare.

Sai dai da muka fara karanta irin tsokacin da mabiya shafin suka yi, mun ga ra’ayoyi mabanbanta. Yayin da akwai wadanda suka yarda cewa da gaske ne, da yawa sun nuna shakkunsu. Misali Sahid Ibro cewa ya yi “double twale for the photographer,” ke nan hoto ya yi kyau ina jinjinawa wanda ya dauka. Haka nan ma wasu karin masu tsokacin irin su Muktar Bappah Dangaladima da Muhammad Bappah Biriy wadanda duk suka nuna gamsuwarsu da cewa “Masha Allah” 

To sai dai Abdulwahab Muhammed Aleeyu Zaria ya karyata wannan batun inda ya fito karara ya fara tun daga ruwan saman da suke da’awar an yi ya ce “babu inda aka yi ruwa yau a cikin Abuja.” Yayin da shi kuma Eddrees Isah ya ce “kuma fa wani sa’ar makaryata ne. Ya kamata yasin kuna tsayawa ku ji sai ku fada.

Tantancewa

Mun fara binciken wannan labarin da manharajar Google reverse image mai tantance hotuna sai muka gane da cewar kawai an hada hotuna ne daban daban na kasashe daban daban suka wallafa da da’awar birnin tarayya ne. 

Dan Kara tantance hotuna muka kara yi amfani da mahanrajar Yandex wadda ita ma ana amfani da ita wajen tantance hotuna da bidiyoyi, sai muka ga bayyanan cewa wadannan hotunan na wasu kasashe ne wadanda a cikin su akwai Japan da Indiya.

Bacin haka mun kuma ga wasu daga cikin hotunan wadanda ake amfani da su a shafukan daukar hotunan kyauta wadanda suka nuna mana cewa wadannan ne ainihin hotunan da aka kwafa aka hada aka sa a shafin a sunan wai Abuja. 

Ga wasu kadan daga cikin asalin hotunan da aka harhada suka zama da’awar da ATP Hausa ta wallafa.

Hatta ruwan saman da suka yi da’awar an yi ranar Litinin din ma ba gaskiya ba ne domin mun tantance hakan da wadanda ke zama a Abujan. 

Bacin haka, mun yi la’akari da cewa irin wannan hoton idan da Abuja ne da zai bulla a wata kafar yada labaran mai sahihanci amma da mu ka kara dudubawa dan bincikar hakan, sai muka lura ba wata sahihiyar kafar yada labarian da ta dauki 

DUBAWA tayi wannan binciken ne domin wayar da kan al’umma baki daya akan karyace-karyacen da yaudarar soshiyal media na yau da kullum da burin sa jama’a su zama a ankare da mayaudara yau da kullum.

Hotunan da aka wallafa a sunan wai birnin Abuja ne da daddare na bogi ne
Hotunan da aka wallafa a sunan wai birnin Abuja ne da daddare na bogi ne

A Karshe
Bincike ya tabbatar mana da cewar hotunan da ATP Hausa ta wallafa a shafin ta na Facebook da da’awar birnin tarraya ne da daddare bayan an kammala ruwan sama Karya ce!

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button