Zargi: Wani mai amfani da tiwita na zargin wai a jihar Adamawa, wasu magoya bayan Atiku, dan takarar shugabancin Najeriya a inuwar jam’iyyar PDP, sun kona tsintsiyoyi dan nuna goyon bayansu ga dan takarar
DUBAWA ta gano cewa an dauki bidiyon ne lokacin wani bukin al’adar gargajiya a Ghana, abun da su ke kira bukin wuta na Bugum Chugu. Wannan ba shi da wata alaka da Najeriya bare kuma jam’iyyar PDP
Cikakken bayani
Yayin da zaben 2023 ke karatowa a Najeriya, shafin sada zumunta na soshiyal mediya na cike mahawarori dangane da manyan ‘yan takaran mukamin shugaban kasa.
Ba da dadewan nan ba wadansu masu amfani da soshiyal mediyar suka fara yada wani bidiyon TikTok wanda ke zarhin wai matasa ne a jihar Adamawa suka fito kwansu da kwarkwatarsu su marawa dan takarar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar baya.
“Milliyoyin matasa sun kona tsintsiyoyi a Adamawa bayan da suka karbi Atiku, toh, wannan somin tabi ne. 2023 za ta haukace. #AtikuKawai a cewar wani marubuci a tiwita.
Bidiyon ya nuno dandazon mutane sun yi ayari a kan titi suna rike da sandunan da aka kunna wa wuta a hannayensu yayin da sauti ke bugawa.
Wannan bidiyon dai ya ruda masu amfani da soshiyal mediya. Yayin da wasu suka yarda wai matasar Adamawa ne ke kona tsintsiya dun una goyon bayansu ga dan takarar jam’iyyar PDP wadansu na zargin bidiyon ya fito ne daga kasar Ghana.
Shi ya sa DUBAWA ta ke so ta tantance gaskiyar labarin
Tantancewa
Bayan duba bidiyon da kyau, DUBAWA ta gano sunaye biyu daban-daban na shafukan da ake zargi su ne ainihin shafukan da suka fara wallafa bidiyon. Duk da cewa sunayen ba su fita da kyau ba, ta iya gane cewa sunayen na mutane daban-daban ne.
Da ma can shafin TikTok ya saba sanya sunan mai amfani da bidiyon a jikin bidiyo, to sai dai bai kamata a ce bidiyo na da sunaye biyo ba, abin da ke nuna cewa an gyara bidiyon ne, ba na gaskiyar ba ne.
Da DUBAWA ta cigaba ta gudanar da bincike tana yin amfani da mahimman kalmomi a manhajar TikiTok, shafuka da dama wadanda ke dauke da bidiyon suka bayyana.
Wanda ya fi dadewa bisa kwanan watan da ke kan bidiyoyin shi ne wanda ya bayyana cewa an nadi bidiyon ne yayin wani buki a kasar Ghana wanda aka yi ranar 9 ga watan Ogostan 2022 wannan ya dan banbanta da wanda ake yadawa. A na farkon an fi mayar da hankali ne kan kuwar da mahalarta ke yi ba a kan sautin da ake bugawa ba. Haka nan kuma, yawancin mutanen na fifita daurin ciyawar da aka kunna wa wuta ne ba tsintsiya kamar yadda ake zargi ba
Bukin wuta na Bugum Chugu
Kowace shekara ake gudanar da bukin Bugum Chugu a yankin arewacin Ghana. A kan karrama bukin ne da kunna wuta kan ‘yan kananan daurin ciyayi a kuma yi ayari a bi garin ta hanyoyin da mahukunta su ka amince da su ana wakokin yaki.
Da wannan bukin kuma ake shiga sabuwar shekara a watan gargajiya na Bugum Gori, wanda aka fi amfani da shi a jama’ar Dagomba wanda su ke kira ‘3iem.”
Bisa labaran da ake bayarwa, tun da dadewa mabiya wannan al’ada ke raya ta, bayan da aka gano daya daga cikin ‘ya’yan sarkinsu wanda ya bata yana baci a karkashin bishiya.
A Karshe
BIncikenmu ya nuna mana cewa bidiyon da ake yadawa na wani bukin shekara-shekara ne wanda aka saba gudanarwa a yankin arewacin Ghana. Ba shi da wata alaka da Najeriya bare ma dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar PDP. Dan haka zargin da aka yi hade da bidiyon karya ne.