African LanguagesHausa

Babban Bankin Laberiya ba ta mayar da takardun kudin dalolin Laberiya na L$25 da L$30 sulalla ba

Zargi: Gwamnatin Laberiya ta babban bankin kasar ta mayar da takardun kudin dalolin Laberiya L$25 da L$30 zuwa sulalla, a cewar wani mai amfani da shafin Facebook

Babban Bankin Laberiya ba ta mayar da takardun kudin dalolin Laberiya na L$25 da L$30 sulalla ba

Babban bankin Laberiya ya ce dalolin kasar na L$5 da L$10 ne kadai ya mayar da su sulalla

Cikakken bayani

Da alama kasar Laberiya na yunkurin komawa zamanin da ta kasance kafin yaki lokacin da ta rika amfani da sulallu a matsayin kudin gudanar da saye da sayarwa. A shekarun 1847 da 1862 jan karfe ko tagulla ake bayarwa a matsayin senti 1 ko 2 kuma su ne suka kasance kudin Laberiya har zuwa 1869 lokacin da aka gabatar da wasu karin sulallun wadanda suka hada da senti 1, 2, 10, 25 da 50. An yi na karshen ne a shekarar 1906.

Bisa la’akari da doka mai lamba 34(d) na kundin tsarin mulin Laberiyar, majalisar dokokin kasar ce ta bai wa babban bankin izinin buga sabbin kudi da kuma yin sulallu a kasar.

Dokar ta 34(d) ta ce  majalisar dokoki ma da ikon, “sanya haraji kan kayayyakin da ake shigarwa, da sauran hanyoyin samun kudaden shiga, tana iya cin bashi , ta samar da takardun kudi, ta buga sulallu ta kuma yi kasafin kudin da gwamnatin jamhuriyar za ta yi amfani da shi.”

Da wannan dokar ne, majalisar dokokin Laberiyar ranar 6 ga watan Mayun 2021 ta sanya hannu kan wata kuduri ta hadin gwiwa (Resolution #001/2021) tana baiwa babban bankin ikon yin sabbin takardun kudin Laberiyar mai darajar dalar Laberiyar (L$) 48

Majalisar ta dauki wannan matakin ne domin yin amfani da shawarar da ta samu daga Kwamitin Kula da Tattalin Arzikin kasar wato EMT dangane da karancin takardun kudin a kasuwanni. Bacin haka, kudaden da suka lalace suna da yawan gaske kuma ana fama da karancin kananan takardun kudin irin su L$ 5, L$10, L$ 20.

Ana sa ran buga wadannan sabbin takardun kudin a cikin shekaru uku inda za’a fara a 2021, sai 2022 sa’annan 2024. Za’a tsallake 2023 saboda a cewar majalisar a wannan shekarar ce za’a a yi zabe.

Ana samun lokutan da masu ababen haya irinsu Babur da Tasi su kan shiga rigima da fasinjoji saboda karancin canji ko kuma ma takardar kudin ba ta da kyau duk ta lalace.

Majalisar dokokin tana fatan shawo kan ire-iren wannan kalubalen da kudurin da ta sanyawa hannu a watan Maris na 2021.

Bayan haka ne bankin ta buga kudin farko ta shigar da shi kasar a watan Disembar 2021 domin ta fara shawo kan matsalar a lokacin bukuwar karshen shekara

Ko da shi ke duk da shigowar kudaden, ba’a iya shawo kan matsalar yadda aka zata ba domin babban bankin ta bugo manyan takardun kudin ne a maimaikon kananan, wadanda talaka ke amfani da su yau da kullun.

Yanzu haka dai an sami labarin cewa an bugo wasu sabbin kudaden an shigar da su kasar abin da ya sanya wasu ‘yan Laberiyar shiga shafukan sada zumunta dan toda albarkacin bakin su tare da wani hoton da wasu ke zargi hoton kudin ne a ciki.

Daga cikin wadanda suka yi tsokacin har da Varney A Teah wani sannanen mai amfani da shafukan sada zumunta wanda ke zaune a kasar Kanada. Sunan sa a shafin Facebook shi ne “Strong Gbana Pekin” Wannan tsokacin na sa ya yadu sosai inda zuwa lokacin wannan rubutun an yi tsokaci sau 250.

Tantancewa

Ganin yadda batun takardun kudin ke da mahimmanci sosai a kasar, DUBAWA ta dauki matakin tantance gaskiyar batu dan gano abubuwan da su ke gaskiya a cikin irin zarge-zargen da su ka cika shafukan soshiyal mediyar.

DUBAWA ta fara da duba izinin da majalisar dokoki ta baiwa babban bankin inda ta gano cewa kudurin wato (Resolution #001/2021) a shafukan 18 da 19 na rahotan shekara-shekara na bankin wanda aka wallafa a 2021.

Daga nan DUBAWA ta tuntubi jami’ai a babban bankin Atty. Alphonso Zeon domin samun karin bayani dangane da zarge-zargen da aka yi a Facebook dangane da sabbin kudaden da ake zargi an buga wato dalar Laberiya 25 da 30.

Mr Alphonso ya hakikance cewa babu wani abu kamar sulallun 25 da 30 na dalar Laberiya wadanda aka buga a matsayin sulalla.

DUBAWA ta kuma tuntubi shugaban sadarwar babban bankin Mr. Cyrus Wleh Badio wanda ya karyara duka zarge-zargen da aka yi a Facebook.

Ma’aikatar Yada Labarai, Al’adu da Yawon Bude Idanu ta fitar da sanarwar da ta fayyace bayanai da zarge.zarge da aka rika gani a Facebook. Tuni aka wallafa wannan sanarwa a wasu daga cikin jaridu da kafofin yada labaran gwamnatiirin su The New Liber Newspaper da ma shafin Ma’aikatar Yada Labaran a Facebook.

A Karshe

Binciken da DUBAWA ta yi a shafin Facebook dangane da zargin ko babban bankin Laberiya ya buga sabbin sulallun L$25 da L$30 ya nuna cewa batun karya ce. Bankin kolin ya bayyana cewa ya buga L$ 5 da L$ 10 ne kadai wanda ya zo daidai da izinin da majalisar dokoki ta bayar bisa la’akari da tanadin kundin tsarin mulkin kasar.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button