Zargi: Wasu masu amfani da shafukan Facebook da Tiwita na zargin wai Asusun Ba Da Lamuni na Duniya (IMF) ya dora karfin tattalin arzikin Najeriya a mataki na 25 cikin kasashe 195 a duniya.
A shekarar 1944 aka kirkiro Asusun Ba Da Lamuni na Duniya, wanda aka fi sani da IMF ko kuma International Monetary Fund a turance, wanda kungiyar kasa da kasa ce mai mambobi 190 –kusan dukkan kasashen duniya mambobin kungiyar ne. Hedikwatar asusun na birnin Washington D.C. da ke Amurka kuma makasudin kungiyar shi ne tabbatar da bunkasar tattalin arziki a duniya, daidata lamuran da suka shafi kudi, da saukake kasuwanci a matakin kasa da kasa da kuma rage talauci tsakanin mambobinta.
Sakamakon sanya idon da kungiyar ta IMF ke yi, ta kan tara bayanai dangane da tattalin arzikin kasashe da ma na duniya baki daya. Bacin haka, ta na yin hasashen yanayin tattalin arzikin kasashe (da na duniya) akai-akai. A kan wallafa wadannan hasashen a kundin da ake kira World Economic Outlook a turance, wanda ke nufin Hangen Yanayin Tattalin Arzikin Kasashen Duniya Nan Gaba. Hade da wannan, IMF ta kan tallafawa kasashe mambobi da bashi da kuma horaswa dan kowa musu makamai da dabarun aiki da kuma inganta wadanda suka riga suka iya.
Kwanan nan wani labarin da aka wallafa a shafin Facebook wanda kuma aka yada sosai a shafukan sada zumunta ya yi zargin cewa Asusun Bada Lamunin ya ce yanzu yanayin tattalin arzikin Najeriya na mataki na 25 cikin jerin kasashen da ke samun bunkasa a fannin tattalin arziki. A karkashin wannan labari an kuma kara da wani zargin me cewa a karkashin mulkin jam’iyyar hamayya ta PDP Najeriya ta kasance a mataki na 150 a wannan fannin.
Da DUBAWA ta kara yin bincike, ta gano cewa an wallafa wannan labarin sau da yawa ana yin amfani da tsari daban-daban. Wani ma har ya kara da cewa manyan gidajen talbijin na Channels da AIT ba za su kawo irin wannan “labarin mai dadi” ba
Labarin cewa ya yi:
“Labari da dumi-dumi! Najeriya ta zo mataki na 25 cikin kasashe 195 cikin jerin kasashen da ke da karfin tattalin arziki a duniya. Channels da AIT ba za su kawo irin wannan labadin mai dadi ba.”
Wannan labarin ba a shafin facebook kadai ya yi yawo ba, har ma a shafin tiwita wani mai suna Fortunate Ayoade ya maimaita batun a shafin shi.
Baya ga ayar tambayar da batun ya sanya dangane da sahihancin labarin, zargin ya kuma hadasa mahawara tsakanin ‘yan barandan siyasa a shafin Facebbok.
Zabukan 2023 na karatowa, kuma dama lokacin zabe kan zo da zarge-zarge marasa tushe, da yawa wadanda wata sa’a su kan kasance wani bangare na manyan takaddama tsakanin al’umma.
Tantancewa
Duk da irin daukar hankalin da labarin ke da shi, DUBAWA ta gano cewa babu kafar yada labaran da ta kawo wannan labarin.
Sai dai akwai wani labarin mai kama da shi da aka wallafa ranar 29 ga watan Disemban 2020 a jaridar Nigerian Tribune. Jaridar ta rawaito cewa IMF ta ce tattalin arzikin Najeriya ya kasance a mataki na 26.
Domin sake tabbatar da sahihancin wannan bayanin, DUBAWA ta tuntubi Dataphyte ta hanyar email. Dataphyte kungiya ce ta yada labarai wadda ke bincike da nazarin alkaluman da suka shafi bayanai da burin yin amfani da su da fasahohinta wajen bunkasa yanyin zamantakewa da tattalin arzikin Najeriya.”
Bisa bayanan alkaluman da aka samau daga IMF wadanda ke nuna yawan abin da kasashe ke samu kowace shekara wato GDP, Dataphyte ta tabbatar da cewa Najeriya ba ta mataki na 25 a jaddawalin da ke auna yanayin karfin tattalin arzikin kasashen duniya. Sai dai, kuma kungiyar ta kara da cewa ba’a taba sanya Najeriya a matakin da ya yi kasa da 50 ba a tsawon shekaru 16n da gwamnatin PDP ta yi mulki.
Dataphyte ta ce ta kai ga wannan sakamakon ne bisa hanyoyin biyu da IMF ke amfani da su wajen nazarin jaddawalin tattalin arzikin kasashen. (A) GDP – (ko kuma abin da kasa ke samu kowace shekara) bisa darajin kudin a billiyan (Dalan Amurka) da (B) GDP – bisa farashin kayayyakin masarufi da darajan takardun kudin kasar dan ganin ko kudin na da karfin sayen kayayyakin yadda ya kamata. Abin da ake kira da turanci Purchasing Power Parity (PPP).
Haka nan kuma kungiyar ta hada duk matsayin da IMF ta bai wa Najeriya da alkaluman GDPn da ta samu tsakanin 1999 zuwa 2022 dan bayar da karin bayani dangane da batun.
Wadannan bayanai da aka samu daga IMF ta hannun Dataphyte sun nuna cewa a maimakon mataki na 25 da ake zargi Najeriya na mataki na 27 cikin kasashen da suke da tattalin arziki mai karfi a duniya.
A karshe
Zargin cewa wai kwanan nan an sanar cewa na Najeriya na mataki na 25 cikin jerin kasashen da ke da karfin tattalin arziki ba gaskiya ba ne. Haka nan kuma batun cewa tattalin arzikin Najeriyar na mataki na 150 lokacin mulkin PDP shi ma karya ne. Bayanan da Daraphyte ta bayar sun nuna cewa tattalin arzikin Najeriya bai taba sauka kasa da 50 a tsakanin 1999 zuwa 2022.