Zargi: A wata hira da aka yi da shi, Mataimakin shugaban kasa na musamman kan hulda da jama’a kuma babban mai magana da yawun majalisar yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC Ajuri Ngelale ya ce Najeriya ta zama kasar da ta fi noman shinkafa a nahiyar Afirka a karkashin wannan gwamnatin
Binciken DUBAWA ya tabbatar da gaskiyar wannan zargin kuma binciken da ta yi ya nuna cewa Najeriya ita ce ma a mataki na 14 a jerin kasashen da ke noman shinkafa a duniya
Cikakken bayani
Lokutan zabe kan zo da mahawarori inda kowa ya ke so ya tofa albarkacin bakin shi ko kuma ma ya nuna gwaninta. Ga wadanda ke jami’yya mai mulki, ma’aunin da ake amfani da shi wajen gwada ayyukan da suka yi ya fi na sauran domin masu zabe su kan yi amfani da wannan damar su duba irin abubuwan da gwamnatin ta yi a baya.
Yayin da ake shirin zaben watan fabrairun 2023, Ngelalen ya yi bayani a gidan talbijin na Channels a shirinsu na siyada mai suna Politics Today wanda Seun Okinbaloye ke jagoranta.
Yayin da ya ke kare matakin da jam’iyyar mai mulki ta dauka na tsayar da Bola Tinubu a matsayin dan takarar shugaban kasa Ajuri ya ce daga shekarar 2015 zuwa yanzu, Najeriya ta kasance kasar da ta fi noman shinkafa a nahiyar Afirka.
Mun gano wannan ne a shafin tiwita wajen wani mai suna David Offor, wanda ya yi wa labarin taken “Ko an hada Dino Melaye, Daniel Bwala da Dele Momodu, hikimarsu ba za ta taba kaiwa na Ajuri ba. Baba albarka ne ga yakin neman zaben Bola Tinubu.
Bidiyon da ya wallafa mai tsawon minti biyu da dakiku 19 ya nuna Ajuri yana yabawa yunkurin da gwamnati ta yi wajen gudanar da suaye-sauyi a fanin noman kasar. Bayan minti guda da dakiku 14 daidai ya ce “a daya hannun, idan kuka duba kudurorin shi (wato kudurorin Bola Tinubu) a shafi na 27 inda ya bayyana shirye-shiryen da ya tanadar wa fannin noma, ya bayyana cewa zai dora kan tushe mai kwarin da shugaba Buhari ya kafa wajen gyara fannin nomar kasar. “Mun tashi daga yanayin da mu ke a 2015 na kasar da ta fi shigar da shinkafa zuwa kasar da ta fi nomawa a Afirka.”
Lokacin da muka ga sakon an riga an karanta shi sau 9,554, mutane 840 suka nuna alamar amincewarsu da sakon wasu 375 sun sake rabawa yayin da wasu 102 suka yi tsokaci a karkashin labarin.
A halin da ake ciki dai farashin buhun shinkafa mai nauyin kilo 50 na kan Nera 35,000 kuma ganin cewa wannan farashi mai tsada ne ya sanya alamar tambaya dangane da sahihancin wannan furucin na Ngelale. Shi ya sa ma DUBAWA ta ce za ta tantance gaskiyar batun.
Tantancewa
Kafin zuwan gwamnatin Buhari a 2015, Najeriya ta kashe dalan Amurka billiyan 2.41 cikin shekaru 3 wajen shigar da shinkafa kawai, bisa bayanan da gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emefiele.
DUBAWA ta gano cewa babban bankin kasar wato CBN ta samar da shirye-shirye kamar bayar da bashi ga wadanda ke noma dan sayar da abin da suka noma da ma wane Nera biliyan 220 da ta ware a matsayin wani asusu taimakawa manoma masu kanana da matsakaitan sana’a’o’i dan taimaka musu a Najeriya.
Bacin haka, ranar 23 ga watan Yunin 2015 gwamnatin tarayya ta haramta shigar da shinkafa da ma wadansu kayayyakin da ke bata wa kananan masana’antu jari da kasuwancin su.
Idan kuma muka je watan Fabrairun 2022 wuraren gumin shinkafa sun karu daga 10 zuwa 68 duk a cewar gwamnan babban bankin.
Emefiele ya ce wannan karin da aka sami ni ya kara yawan abin da ake samu wajen noman shinkafa daga tonne 350,000 zuwa tonne miliyan uku.
Karin binciken da muka yi ya nuna cewa Najeriya ta kasance kan gaba a jerin kasashen da ke noman shinkafa a nahiyar Afirka. A cewar kungiyar kula da noma da abinci (FAO) na Majalisar Dinikin Duniya a shekarar 2020, Najeriya na mataki na 14 a duniya cikin jerin kasashen da ke noman shinkafa a yayin da China ke matakin farko. Kasashen Masar, Tanzaniya da Madagascar ne kadai suka kasance cikin jerin kasashe 20 na farko a duniya.
Ofishin kula da nomar da ta shafi kasashen ketare na Amurka ita ma ta goyi bayan karin da aka samu a noman shinkafa a Najeriya. A watan Nuwamban 2021 ofishin ya fitar da wata sanarwar da ta nuna cewa Najeriya ta yi noman tonne Miliyan 4.89 yayin da ta ke biye da Masar wadda ta yi noman tonne miliyan hudu.
A Karshe
Duk da cewa farashin shinkafa a yanzu ya fi abin da aka rika saye a shekarar 2015, zargin Ajuri na cewa Najeriya ta fi kasashen Afirka noman shinkafa gaskiya ne