Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Santa Trump ya wallafa ( posted) wani bidiyo na Fafaroma Francis mai rasuwa shafin X inda ya nuna shi da hannye har guda uku abin da ke zama wani abu na daban.

Hukunci: KARYA CE! Asalin bidiyon a shafin Fadar Vatican ya nuna shi da hannu guda biyu ne kadai, dabarun gano asalin bidiyo ma ya nuna cewa an yi dabaru da fasahar AI an kirkirar masa karin hannu ne.
Cikakken Sakon
Fafaroma Francis shine shugaban Cocin Katolika da ke Fadar Vatikan tun daga watan Maris 2013 har zuwa lokacin da ya rasu a 2025. Shi ne (He) fafaroma na farko daga kungiyarsu ta (Jesuit pope), na farko daga Latin Amurka, na farko da aka haifa ya kuma girma a wajen Nahiyar Turai, tun a karni na 8 da aka samu Fafaroma Gregory III daga Siriya.
Santa Trump (@lovetocook12345) ya wallafa a shafin X wani bidiyo (video) na tsohon fafaroma da ya rasu yana zaune a kujerar masu larurar kafa yana daga hannu, hannunsa na uku a kan cinyarsa, an sanya taken bidiyon da cewa “An wallafa a shafin intanet na fadar Vatican, Shin akwai wanda zai yi bayani me yasa yake da hannaye uku? Babu wanda zai mayar da shi gefe?”
Yayin da wasu suka amince da wallafar wasu kuwa sun nuna tantamarsu ne ga sahihancin bidiyon. @Garebear588 ya rubuta cewa , “ Shin akwai wanda zai tantance min wannan. Shine abin da ake nunawa a TV?”.
Wani mai amfani da shafin, @earth_matter31, ya mayar da martani da cewa, “Yana da hannaye guda uku ne, abin da ba a nunawa a gidajen talabijin.”
The Raw Vegan (@RwVgnAdvice) ya mayar da martani da cewa , “Wannan ba makawa karya ce.” Wani mai amfani da shafin, Master Mattamous(@MMattamous), yayi tambaya ne, “ Shin da gaske an wallafa wannan bidiyo a shafin intanet na Fadar Vatican? Ko dai kawai kana samar da labarai ne don mutane su so ka?”
Bincike kan bidiyon a shafin Google ya nunar da cewa wannan wallafa ta bazu a Facebook da wasu kafofin kamar a wadannan wurare here da here da TikTok, da Instagram.
Wannan bidiyo da ya yadu kamar wutar daji a shafin na X, an kalle shi 3,100,000 (views), da masu nuna sha’awa 2,000 (likes), da masu sake yadawa 542 (reposts), da masu tsokaci 172 (comments), tun bayan da wallafar ta bayyana a ranar 9 ga Satumba,2025.
Duba da yadda ake samun mabanbantan tsokaci da yadda bidiyon ya yadu, DUBAWA ta ga dacewar gudanar da bincikenta.
Tantancewa
DUBAWA ta hanyar amfani da wasu muhimman kalmomi ta duba ko akwai wata kafar yada labarai sahihiya da ta yi wannan labari amma ba ta samu ba.
Sai kuma aka sa bidiyon a shafin google don tabbatar da shi, nan sai ya kai binciken ga shafin YouTube na New York Post wanda suka wallafa bidiyo a lokacin da Fafaroma Francis ke ban kwana da mutane a lokacin bikin Easter.
A wannan bidiyo mun lura cewa Fafaroma na da hannu ne guda biyu, wadanda ya daga yana bankwana da al’umma, wannan daga hannun yana jujjuyawa ya nunar da cewa bidiyon dabaru aka yi masa.
Mun nazarci bidiyon ta hanyar (Attestiv Video,) manhajar da ke gano bidiyo na bogi, don tabbatar da abin da muke zargi. Nazarin ya nunar da shakku mai karfi, abin da ke nuni da cewa an sauya asalin bidiyon.

Daga nan sai aka yi amfani da Deepware, wata kafar da ke gano amfani da fasahar ta AI, ita ma wannan kafar ta tabbatar da cewa akwai alamu na amfani da AI wajen hada bidiyon.
A Karshe
Binciken DUBAWA ya nunar da cewa bidiyon an yi amfani da fasahar AI ne wajen hada shi. Asalin bidiyon da aka samu daga New York Post ya tabbatar da cewa Fafaroma mai rasuwa hannunsa guda biyu ne.