African LanguagesHausa

KARYA NE! OAU bata ayyana hutu ba saboda wasannin  WAUG

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Jami’ar Obafemi Awolowo za ta fara hutun dole saboda za ta dauki bakuncin Wasannin Jami’oin Afurka ta Yamma (WAUG) a wannan shekara.

<strong>KARYA NE! OAU bata ayyana hutu ba saboda wasannin  WAUG</strong>

Sakamakon bincike: KARYA NE! A tattaunawa da jami’ai na jami’ar ta tabbatar da cewa makarantar ba ta bayyana tafiya hutun karatu ba.

Cikakken sako

A ranar Litinin 4 ga watan Disamba, 2023, wasu labarai da aka wallafa a kafofin sadarwa sun yi da’awar cewa zaa tafi hutun sabuwar shekara a Jami’ar Obafemi Awolowo University (OAU) daga ranar 15 ga watan Disamba, 2023 zuwa 8 ga watan Janairu 2024.

Sakon da aka watsa ya ce bayan wani zama na hukumar gudanarwar jami’ar (senate) a ranar Juma’a daya ga watan Disamba shugabancin jami’ar ya amince cewa za a fara hutun daga 15 ga watan Disamba,2023 zuwa 8 ga watan Janairu,2024.”

“Ba da bata lokaci ba za a shiga hutu saboda wasannin da jami’a za ta karba daga 15 ga watan Disamba zuwa 23, wannan ya sanya za a yi amfani da mazaunin dalibai ga wadanda za su shiga gasar.” Wannan sakon na nufin gasar jami’oi na kasashen Yammacin Afurka (WAUG) wanda jami’ar za ta karba  (hosted) a wannan shekara.

Mun ga dacewar gudanar da bincike kan wannan labari duba da yadda daliban jami’ar suka shiga rudani, wanda ke nuna masu cewa za su tafi hutu a yayin da hannu guda kuma ga hutu na watan Disamba.

Tantancewa

Wannan kafa mai bin kwakkwafi ta tuntubi jami’ar ta hanyar jin tabakin shugaban da ke kula da harkokin dalibai a jami’a (DSA), John Odediran, wanda ya tabbatar da cewa wannan labari karya ne kasancewar ba ra’ayin hukumar gudanarwar jami’ar ba ne.

Har ila yau mun ji ta bakin shugaban Tsangayar Fasaha a jami’ar Farfesa Olufemi Adebola Koya, wanda ke zama mamba na (senate) wanda ya sake tabbatar da cewa labarin karya ne. Ya ce jami’a za ta tafi hutu ne a a ranar 23 ga watan Disamba, 2023 saboda ai wasannin na WAUG wani bangare ne na harkokin rayuwar makaranta, saboda haka ana karatu ana wasanni tare.

Ya ce wadanda za su zo wasannin na WAUG yawansu ba zai kawo cikas ba ga zaman daliban.

Ya kara da cewa “Ko da anan ko a wani wajen ne za a yi wasannin na WAUG wadanda ke zuwa wasan wani adadi ne” idan ba haka ba ai dukkanin makarantun sai su rufe. Kazalika yawan adadin wadanda za su zo, ba za su sa ‘yan makaranta su ba su waje ba. Daliban ba za su bar makarantar ba, su  bar baki a wajen kwanansu ba.”

Farfesa Koya ya kara da cewa wannan labarin yayi ta yaduwa kwanaki ma kafin mu zauna tattaunawa a (senate)

“Labarin karyar ya rika yaduwa kwanaki kafin zaman (senate) na ranar Juma’a wanda zaman kawai ya mayar da hankali kan sakamakon jarrabawar dalibai.”

Omisore Elijah, jami’in hulda da jama’a na kungiyar dalibai shima ya tabbatar wa da DUBAWA cewa babu wani batun hutu a wannan lokaci da aka bayyana kamar yadda ya jiyo shima daga hukumar gudanarwar jami’a.

A Karshe

Bayanan da suka nunar da cewa za a tafi hutu daga ranar 15 ga watan Disamba, 2023 zuwa 8 ga watan Janairu 2024 saboda wasannin WAUG karya ne. Hukumar jami’ar ta nesanta kanta da wannan labari.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Translate »