African LanguagesHausa

Bidiyon wani dan sandan da ke farautar wadanda ake zargi da ta’addanci, ba shi da dangantaka da kashe-kashen jihar Ondo

Zargi: Wani bidiyon da jama’a ke yadawa a soshiyal mediya na yadda wani dan sanda ya kayar da wani mutumin da ke rike da bindiga. Mutane da dama na zargin wai lamarin ya afku ne a garin Owo da ke jihar Ondo inda ‘yan bindigan da ba’a san ko su wane ne ba suka hallaka wadansu mabiya a Cocin Katolika.

Bidiyon wani dan sandan da ke farautar wadanda ake zargi da ta’addanci, ba shi da dangantaka da kashe-kashen jihar Ondo

Bidiyon an gyara shi dan a yaudari jama’a domin DUBAWA ta gano cewa ba a Najeriya aka nadi hoton bidiyon ba, kuma abin da ke ciki ba shi da wata alaka da Najeriyar.

Ranar 5 ga watan Yunin 2022 abin takaici ya afku a cocin Katolika na St. Francis da ke kan titin Owa-Luwa, a garin Owo, Karamar hukumar Owo da ke jihar Ondo lokacin da wadansu mahara suka kai harin da ya hallaka mabiya da dama a yayin da su ke sujada.

Shafukan soshiyal mediya sun cika da hotuna masu tayar da hankali na gawwakin wadanda suka hallaka a wurin.

Duk da cewa ‘yan sanda sun ce ba su kai ga tantance wadanda ke da alhakin tabka wannan ta’asar ba, masu amfani da shafukan sadarwar soshiyal mediya da yawa na zargin wai ‘yan Filani masu kai hari ne suka kai mummunar harin da ba’a kai ga tantance yawan mutanen da abin ya shafa ba.

Yayin da lamarin ya jefa ‘yan Najeriya cikin makoki wadansu masu amfani da soshiyal mediyar sun fara raba wani hoton bidiyo suna cewa an cafke maharan sa’o’i kadan bayan da suka kai harin.

A bidiyon, an kuma yi zargin wai wani dan sanda ya kama daya daga cikin maharan da suka kai hari a cocin na jihar Ondo

Wani mai amfani da shafin Facebook ya wallafa bidiyon a shafinsa da taken: “Jarumin dan sanda ya kama daya daga cikinsu. Ya yi kama da bako.”

A cikin sharhunan da suka biyo bayan hoton, an gano cewa akwai wadanda suka karyata afkuwan hakan a Owo duk da cewa akwai wadanda suka dauki labarin a matsayin gaskiya 

Misali, a tunanin Jide Fashakin, dan sandan “ya canci samun lambar yabo dan irin jaruntakar da ya nuna”, a yayin da shi kuma Ikechukwu Stanley ya ce bayanai sun nuna cewa abin ya faru ne a kasar Togo ba Najeriya ba.

“Wannan ba Najeriya ba ce bare ma garin Owo. Ana zargin hakan ya faru a kasar Togo ne,” a cewar Stanley.

DUBAWA ta yanke shawarar binciken gaskiyar wannan batu ne bisa dalilai na tsaro.

Tantancewa

DUBAWA ta fara da nazarin hoton bidiyon a manhajan InVid. Binciken ya nuna cewa hoton bidiyon ya bayyana a shafukan intanet da dadewa tun kafin kissan da aka yi a cocin Owo.

Hasali ma sigar farko na bidiyon ya bulla a shafin tiwita ne ranar 3 ga watan Yunin 2020 wanda wani mai suna Raissa  Nouradine Kassire ya wallafa tare da taken da aka rubuta da harshen faransanci.

Da aka fassara taken zuwa turanci ga abin da aka bayyana: “Wani dan kasuwan Chadi da ke zama a kasar Togo ya kashe wani jandarma ya kuma yi wa wani dan sanda rauni bayan da suka yi kokarin shawo kan shi. Hakan ya faru ne a wata kasuwa, inda daga baya jama’a suka afka mi shi, mun yi nadamar wannan aikin ashar da aka tabka. Gaisuwar ta’aziyya ta musamman ga iyalan wadanda abin ya shafa da ma al’ummar kasar Togo.”

Rigar da dan sandan ya sanya kuma ba irin na ‘yan sandan Najeriya ba ne. Da muka kara yin bincike, mun gano cewa rigar ta dace da rigunan ‘yan sandan Togo.

DUBAWA ta bi diddigin labarin inda ta gano rahoton da aka yi dangane da batun a wani shafin labaran kasar Togo, inda a kanun labarin aka sanya “Wani matashin Chadi ya daba wa jandarma wuka ya kuma yi wa dan sanda rauni.”

Rahoton ya kuma nuna mana cewa lamarin ya afku ne a babbar kasuwar Lomé.

A karshe 

Labari da ma hoton bidiyon da ke zargin wai wani dan sanda ya kama wani mai rike da bindiga a harin da aka kai a Owo ba gaskiya ba ne. DUBAWA ta gano cewa ba a Najeriya aka nadi bidiyon ba babu abin da ya hada bidiyon da harin Owo.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button
Translate »