African LanguagesHausa

Bidiyon yadda hedikwatar ofishin jam’iyya mai mulki ke cin wuta a Nijar ne ake amfani da shi a sunan ofishin jakadancin Najeriya

Getting your Trinity Audio player ready...

Zargi: Ana zargin wai ofishin jakadancin Najeriya da ke jamhuriyar Nijar ne ke cin wuta a wani bidiyo da ya shiga ko’ina yanzu.

<strong>Bidiyon yadda hedikwatar ofishin jam’iyya mai mulki ke cin wuta a Nijar ne ake amfani da shi a sunan ofishin jakadancin Najeriya</strong>

Sakamakon Bincike: KARYA. Bincikenmu ya nuna mana cewa ginin da ke cin wuta a bidiyon hedikwatar jam’iyya mai mulki ce ta PNDS tarayya. Kuma ma ma’aikatar harkokin wajen Najeriya ta karyata zargin.

Cikakken Bayani

Tun ranar 26 ga watan Yuli ake zaman dar-dar bayan da masu gadin shugaban kasa a birnin Yamai na jamhuriyar Nijar suka kama hambararren shugaban kasa Mohamed Bazoum suka tsare shi a cikin fadarsa da ke babban birnin kasar.

Duk da yunkurin sanya baki da kungiyar Ecowas ta yi, sojojin juyin mulin ba su tanka su ba, illa dai suka cigaba da rike madafun ikon kasar yayin da suke tsare da hambararren shugaba Mohamed Bazoum.

Sai dai, shugabannin kasashen Ecowas sun sha alwashin amfani da karfi wajen hambarar da sojojin juyin mulki Nijar idan har suka cigaba da rike mulki.

Yayin da duk wannan ke faruwa, a sanyin safiyar Asabar 11 ga watan Agustan 2023, wani bidiyo mai tsawon dakiku 45 mai zargin cewa ofishin jakadancin Najeriya da ke birnin Yamai ya kama da wuta ya faro yawo wanda kuma aka ba mu dan mu tantance gaskiyar lamarin.

Ganin cewa irin wannan zargin na da sarkakiya kuma bisa la’akari da yadda ya ke yaduwa cikin gaggawa kamar wutar daji ne muka dauki nauyin gudanar da bincike.

Tantancewa 

Da muka duba bidiyon da kyau, sai muka ga cewa ginin da ke konewar na dauke da wani tambari mai fuskar zaki da kuma kalmar “Bienvenue,” wanda ke nufin maraba da harshen Faransanci.

Mun yi kokarin mafani da manhajar fassara ta google domin fassara tsokacin da aka yi a harshen Faransanci na wasu ‘yan dakiku amma ba mu sami koami ba. Da muka yi kokarin gano mafarin bidiyon a cikin google ko za mu samu wasu alamun da za su kai mu ga samun gaskiya, ba mu sami komai ba. Bacin haka mun sake duba bayanai na musamman a bidiyon wadanda da za su banbanta shi da sauran, nan ma hakon mu bai cimma ruwa ba.

Daga nan muka yi binciken mahimman kalmomi a kan shafin Twitter, wanda ya kai mu ga batutuwa daban-daban, kamar wanda African Observatory (@AfricanWatchman) ya wallafa da bidiyon da aka yi amfani da shi aka yi zargin.

Sai muka yi binciken hoton ofishin jakadancin Najeriya a Yamai. Daga nan sai muka kwatanta shi da wanda muka gani a cikin bidiyon amma ba mu ga wani banbanci ba a launi ko tsarin ginin.

Da muka ga cewa binciken hotuna da ma mahimman kalmomin ba ya ba mu irin sakamako da mu ke so sai muka yi amgfani da alamun da muka samu daga binciken da muka yi muka gano ginin. Wannan ne ya kai mu ga wani labarin da kamfanin dillacin labaran Faransa na AFP da Reuters suka wallafa a ranakun 9 ga watan Agusta da 4 ga watan Agusta bi da bi. Wadannan bayanan ne suka fayyace mana cewa an taba amfani da hoton bidiyon dan nuna harin da aka kai kan ofishin jakadancin Faransa duk da cewa haaraai ne a kan babban ofihsin jam’iyya mai mulki a kasar.

Wani binciken da muka yi na mahimman kalmomi kuma ya kai mu ga hoton ginin da aka kai wa harin, wanda ke da wasu daga cikin alamun da aka bayyana tun farko. Wadannan sun hada da adireshin ginin 613 Avenue de l’OUA, BP 10894, Niamey.

Mun tuntubi mai magana da yawun ma’akatar kula da harkokin wajen Najeriya, Francisca Omoyuli, idan muka bukaci mu ji ta bakinta dangane da bidiyon amma mun gaza samun martani daga wajenta. 

Jim kadan bayan nan aka wallafa wata sanarwar manema labarai a shafin Twitter ma’aikatar kula da harkokin wajen Najeriya ( @NigeriaMFA) inda suka karyata wannan zargin.

A Karshe 

Bincikenmu ya nuna mana cewa ginin da ke cikin bidiyon, ofishin jam’iyyar da ke mulki a Nijar ne ba ofishin jakadancin Najeriya a kasar ba. Ma’aikatar kula da harkokin wajen Najeriya ta fitar da sanarwar da ta karyata labarin.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Translate »