African LanguagesHausa

Tauraruwar Super Falcons Michelle Alozie ba likita ba ce kamar yadda ake zargi

Zargi: Michelle Alozie ‘yar wasan tsakiyra da ke wa kungiyar kwallon kafar Najeriya Super Falcons wasa, likita ce

Tauraruwar Super Falcons Michelle Alozie ba likita ba ce kamar yadda ake zargi

Sakamakon bincike: Babu cikakkiyar gaskiya. Sakamakon wata hirar da muka gano tsakanin Alozie da FIFA mun fahimci cewa Alozie ma’aikaciyar bincike ce a fannin aikin likita ba wai likita ce ba. Bacin haka, ‘yar wasan baya ce ba na tsakiya ba kamar yadda wani mai amfani da shafin Facebook ya bayyana.

Cikakken bayani

Muhimmiyar rawar da Michelle Alozie ta taka a gasar cin kofin duniya na kwallon kafar matar da aka gudanar a Australiya da New Zealand ya kawo mata farin jini tsakanin ma’abota.

A cikin irin rubuce-rubucen yabon da ake wa ‘ya Amurka da Najeriyar ne wani mai amfani da shafin Facebook, Emmy Worldcalss, ya wallafa takaitaccen tarihinta a ciki har da tarihin aikin da take yi bayan da ta kammala karatun jami’a.

“Ga Dr Michelle Alozie mai shekaru 25 na haihuwa. Likita ce wadda ke kwallon kafa. Michelle tauraruwar Super Falcons ce mai wasan tsakiya,” wani banganre na bayanin ya bayyana.

Wannan labarin ya ja hankalin da dama a soshiyal media mutane samda da 51,000 suka latsa alamar like ta nuna gamsuwa da amincewa, tsokaci 1,600 sa’annan wasu 1,200 suka raba labaran a shafukanasu.

Wasu daga cikin tsokace-tsokacen da aka yi sun nuna amincewarsu da zargin wai ita likita ce saboda aikin da take yi a fannin. “Tabbas kin zama abun koyi da kika hada aikin likita da kwallon kafa…” wata mai amfani da shafin, Augustine Alogala, ta rubuta.

Ganin yadda batun ya dauki hankali ne muka ga ya dace mu fayyace labarin dan tantance gaskiyar aikin da Alozie ke yi.

Tantancewa

Mun yi kokarin gano ainihin aikin da Alozie ke yi da ma gurbin da take wasa a kungiyar kwallon kafar Najeriya. Daga shafinta na LinkedIn, shafin da ke bayyana aikin yi da kwarewar wadanda ke amfani da shi mun gano cewa tana da digirin farko a ilimin kananan kwayoyin hallitu (Bachelor of Science (BS) in Molecular Cellular Developmental Biology) daga jamu’ar Yale inda ta yi karatu daga shekarar 2015 zuwa 2019, daga nan kuma ta yi digiri na biyu a ilimin dan adam a wasannin motsa jiki da halayyar gabobin da ake amfani da su (Master of Science (MS) in Sports Psychology and Motor Behaviour) daga jami’ar Tennessee wanda ta kammala tsakanin 2019 da 2022.

Mun yi amfani da mahimman kalmomi wajen cigaba da binciken inda muka gano wata hirar da FIFA ta yi  da tauraruwa wanda aka wallafa ranar 23 ga watan Yulin 2023

A wannan labarin, Ms Alozie clarifies ta bayyana cewa ita ba likita ba ce, illa mai bincike a fannin ilimin likitar. Kowace safiya ta kan je horaswa da kungiyar kwallon kafar Housti Dasg wadda ke NWSL sa’annan da rana ta kan je aiki a asibitin yara na Texas Children’s Hospital inda ta ke aikin binciken da ke nazari kan kansar jini mai tsananin gaske da ma sauran nau’o’in cutar kansar.

Ta ma kara dacewa “bincike a fanin ilimin likitar ma yana da wahala sosai. Mutun zai shafe sa’o’i da dama yana karanta takardu masu yawan gaske.

“Na kan ji kamar a duk sadda wani abu ya faru, idan akwai dan kankanin rauni, idan aka turi wani ko kuma cikinsu ya fara ciwo sai su zo wuri na!” Ta yi dariya. “Sai in ce, guys, ni ba likita ba ce, ban san abun da ke faruwa a cikin jikinku ba!”

Haka nan kuma, sabanin abun da aka rubuta a shafin na Facebook, Alozie ba ‘yar wasar tsakiya ba ce a Super Falcons. ‘Yar wasar baya ce.

A Karshe

Duk da cewa gaskiya ne Michelle Alozie ta ha gada wasan kwallon kafa da aikinta da ke da alaka da ilimin kiwon lafiya ko kuma na likita, a zahiri, ita mai binciken cututtuka ne ba likita ce kamar yadda ake zargi ba. Haka nan kuma a wasan kwallon kafar, ita ‘yar wasar baya ce ba na tsakiya ba kamar yadda ake zargi.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button