Getting your Trinity Audio player ready...
|
Ciakken bayani
Wulakanta takardun kudin naira ko da kuwa ta yaya ne babban laifi ne. Dokar Babban Bankin Najeriya 2007, ta hana liki, takawa, yin zane a kai, saidawa da ma lalata takardun kudin.
Bisa bayanan sashe na 21(1) Dokar CBN 2007, duk wanda aka kama ya na cin zarafin takardun kudin ko kuma la’anta sulalla da takardun zai iya samun hukuncin dauri a kurkuku na tsawon akalla watanni shida ko kuma biyan tara na N50,000 (Kwatankwacin dalar Amurka $37 a lokacin da aka yi wannan rahoton) ko kuma duka biyu.
Kwannan nan wasu sanannun ‘yan Najeriya sun yi fama da wata badakalar wulakanta kudaden wadda ta kai su kotu.
Daga cikinsu akwai dan daudun Najeriya Idris Okuneye, wanda aka fi sani da Bobrisky, da kuma Pascal Okechukwu, wanda shi kuma aka fi kirarsa Cubana Chief Priest.
Wannan batun dai ya janyo mahawarori da cece-kuce a yanar gizo. Da yawa sun fito sun bayyana ra’ayoyinsu dangane da dalilan da a ganinsu suka sa aka yanke wa Bobrisky hukuncin dauri na tsawon watanni shida ba tare da zabin biyan tara ba, yayin da shi kuma Cubana Chief Preist ya sami beli bayan da ya biya tara.
Da suke mayar da martani dangane da batun. Mai amfani da shafin X RSDX @SDX_Trades, ya rubuta, “Abin da kudin Bobrisky ba zai iya ba, kudin Cubana chief priest zai iya yi. Kurungus.”
Wani shi ma mai amfani da shafin na X Olawale Quadri @QualityQuadri, ya wallafa, “Labari da dumi-dumi kan cin zarafin takardun kudin Nairar da Cubana Chief Priest ya yi⤵️EFCC, Cubana Chief Priest za su wayne a wajen kotu, amma Bobrisky zai cigaba da kasancewa a daure duk da cewa laifi daya suka aikata.”
Cikin wani bidiyon TikTok da wani mai amfani da shafin X, @Aramideoflagos, ya wallafa, mai magana ya bayyana cewa shi Bobrisky an kai shi gidan mazan ne domin ya masa laifin da ya aikata. Yayin da shi kuma Cubana Chief Preist ya ku amsa laifin ya ce bai amince ya aikata ba.
Mai magana a cikin bidiyon ya bayyana cewa sakamakon shari’ar ya kasance haka ne saboda tasirin salon lauyoyin da masu laifin suka dauka. A cewarsa akwai mahimmanci a amincewa da rashin amincewa da aikata laifi bisa la’akari da maganar da ake yawan yi wai ba’a iya tabbatar da cewa wanda ake zargi ya aikata laifi har sai sadda aka gabatar da hujjojin da suka gamsar da kotu, ba tare da wata shakka ba cewa wanda ake zargin ya aikata laifin.
Sakamakon wannan mahawarar da kuma irin ra’ayoyin da suka bayyana dangane da sakamakon a shafukan soshiyal mediya, musamman shafin X, DUBAWA ta yanke hukuncin tantance wadannan shari’un da aka yi.
Fayyace hukuncin Bobrisky da na Cubana Chief Priest
Ranar 5 ga watan Afrilun 2024 Hukumar Yaki da Masu yi wa Tattalin Arzikin Kasa Zagon Kasa (EFCC) ta gurfanar da Bobrisky a wani kotun jihar Legas tana tuhumarsa da aikata laifuka hudu na cin zarafin takardun kudin naira da wasu biyu kan zargin wanke haramtattun kudade.
Daga baya, mai shari’a Abimbola Awogboro na kotun tarayyar da ke Legas ya yanke masa hukuncin dauri na tsawon watanni shida ba tare da zabin biyan tara ba.
Lokacin shari’ar, Bobrisky ya amsa laifukan da aka tuhumesa da su ya kuma fadawa kotun cewa bai san wai karya doka ya ke yi ba sadda ya aikata lafin, ya kuma kara da ce shi infuluwensa ne a soshiyal mediya.
“Ni infuluwensa ne a soshiyal mediya kuma ina da mabiya miliyan biyar; a kashin gaskitya ban san cewa na karya doka ba ne. Na so dan an yi mun afuwa dan in sami damar yin amfani da shafi na in ilimantar da mutane kan wulakanta takardun kudin Naira,” Bobrisky ya bayyana sadda ya ke neman afuwa.
Sai dai, Alkalin, Justice Awogboro ya sake tunatar da Bobrisky cewa bai kamata ya nemi uzuri kan rashin sanin dokar ba, abin da shi kansa Bobriskyn ya amince da shi.
Mai shari’ar ya bayyana a cikin hukuncinsa cewa “Wulakanta takardun kudin Naira ya zama ruwan dare, abin da ke cigaba da lalata kimar kasar a idanun duniya. Ya isa haka nan, ya kamata mutane su daina lalata kudin, kuma wannan hukuncin nasa zai zama abin zai hana na baya karya dokar.”
A wani yanayin mai kama da wannam, ranar 17 ga watan Afrilu, hukumar EFCC ta gurfanar da Cubana Chief Priest kan laifuka uku na wulakanta takardun kudin Nairar a gaban mai shari’a Justice Kehinde Ogundare a kotun tarayya da ke Ikoyi a jihar Legas.
Sadda aka gurfanar da shi Cubana Chief Priest bai amsa ko daya daga cikin laifukan da aka tuhume sa da shi ba, sa’annan aka ba shi damar biyan belin miliyan 10 na naira, da mutane biyu wadanda za su tsaya mi shi. Daga nan sai aka dage sauraron shari’ar zuwa biyu ga watan Mayun 20245, dan jin ta bakinsa.
Da suka koma kotu ranar 2 ga watan Mayun, wakilin Cubana chief priest sai ya fadawa mai shari’ar da ke sauraron karar cewa chief preist din ya bukaci da a daidata a wajen kotu. Wannan na nufin cewa akwai bukatar neman janye karar da aka fara shigarwa kafin a nemi yin sulhu.
A waje guda kuma yayin da ya ke cika wa’adinsa a kurkuku Bobrisky shi ma ya tura wasikar daukaka kara wanda ke kalubalantar wa’adin watanni shidan da kotun tarayyar da ke Legas ta yanke masa.
Ra’ayin masanin shari’a
Yayin da ya ke fayyace shari’un biyu, wani masanin shari’a, Ibrahim Abiola ya ce amsa laifi ba wai yana nufin yanke hukunci ba ne kuma idan har ana sa a fahimci komai dole a duba batutuwna da ke kewaye da shari’ar Bobrisky daban da na Cubana Chief Preist.
Ya ce, “A duk sadda mutun ya amsa laifi, ba nan da nan ne kotu za ta yanke hukunci ba. Dole sai masu shigar da kara sun bayar da hujjoji masu gamsarwa ba tare da barin wani hurumin shakka ba kafin a yanke hukunci, kuma abin da ya faru ke nan a shari’ar Bobrisky.
Ya kara da cewa, sai dai a shari’ar Cubana Chief Priest, dole sai an yi la’akari da sashi na 14 (2) na dokar EFCC. Wannan sashin ya bai wa hukumar ikon kara yawan laifukan ta kuma karbi daidai yawan kudin da ta ga ya dace ta karba, ba tare da ya wuce yawan kudin da aka tanadar a matsayin kudin da ya kamata a karba wajen wanda ya aikata irin wannan laifin ba.
A nan ba shakka hukumar ta yanke shawarar amfani da tanadin sashi na 14(2) dan haka bai kamata a kwatanta wannan da na Bobrisky ba, tunda shi kai tsaye ya amsa laifin dai nemi yin amfani da damar daidaita komai a wajen kotu ba.
Sashi na 14 (2) na dokar EFCC na cewa “bisa la’akari da tanadin sashi na 174 na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya na 1999 (Wanda ke da alaka da ikon Antoni janar na kasa ta girkawa, cigabawa, da dakatar da shari’ar miyagun laifukan wani a kowani irin kotun kasar), hukumar ta na iya hada duk laifukan da za’a iya hukuntawa a karkashin dokar ta karbi yawan kudin da ta ga ya dace a karba a madadin hukunci, ba tare da gota ainihin yawan kudin da aka kiyassa a matsayin darajar kudin da ya kamata mai laifin ya biya idan da an same shi da laifi.”
Sai dai ba kowani lokaci ba ne za’a iya amfani da sa sashe na 14 (2) na dokar EFCC, kuma sakamakon wannan shi ne shari’a sosai kamar yadda aka gani a na Biobrisky.
A karshe
Ya na da mahimmanci a san cewa sakamakon kowace shari’a na da dangantaka da yadda masu shigar da kara da lauyoyin wadanda abin ya shafa suka gabatar da hujjojinsu a gaban kotu. Wannan kuma ya zama abun la’akari da shi a laifuka irin wannan da za su faru nan gaba. Yayin da sakamakon shari’un ke nuna irin sarkakiyar da ke tattare da yanayin gudanar da shari’a da laifukan fararen hula, tilas ne mutane su san irin tasirin da maganganunsu za su iya yi yayin da shari’arsu ke kotu.
Wannan bincike an yi shine a shirin gano gaskiya na DUBAWA 2024 karkashin shirin kwararru na Kwame KariKari Fellowship da hadin gwiwar The Informant247, a kokari na fito da “gaskiya” a aikin jarida da inganta ilimin aikin jarida a fadin Najeriya.