Getting your Trinity Audio player ready...
|
Zargi: Tsohon shugaban kasar Najeriya Olusegun Obasanjo ya riga mu gidan gaskiya
Sakamakon bincike: Karya! Bincikenmu da ma mai magana a madadin tsohon shugaban duk sun karyata zargon.
Cikakken bayani
Tsohon shugaban kasar Najeriya wanda ya yi mulki sau biyu a kujerar shugabancin kasar, da farko a matsayin shugaba na mulkin sohi daga shekarar 1976 zuwa 1979 sa’anan daga baya ya yi wa’adi biyu a mulin farar hula daga shekarar 1999 zuwa 2007.
Mr Obasanjo, wanda a ko da yaushe ya ke tsokaci dangane da mulkin dimokiradiyya a Najeriya da ma yadda shugabanin da suka zo a bayan shi ke mulki ya kasance a labarai kwanan nan yana sukar gwamnatin da ta shude, ta tsohon shugaba Muhammadu Buhari.
Ranar Talata biyar ga watan Satumban 2023, wani bidiyo wanda ke zargin tsohon shugban ya mutu ya bulla a kafofin sadarwa musamman a WhatsApp da taken da aka rubuta a harshen Faransanci.
“DÉCÈS DE L’ANCIEN PRÉSIDENT DU NIGERIA OLUSHEGUN OBASANJO” taken ya bayyana
A bidiyon mai tsawon dakiku 12, an sanya RIP ma’ana Allah sa ya huta, bacon haka kuma aka sanya hotunan Obasanjo daban-daban a jikin labarin.
Yadda bidiyon ya shiga ko’ina cikin dan lokaci kalilan ne ya sa muka sami sakonni da dama daga masu amfani da WhatsApp suna neman mu tantance musu gaskiya, kuma a namu bangaren mutumin da ake a tsakiyar zargin ne ya sa muka ga ya kamata mu tantance gaskiya..
Tantancewa
Mun fara da kura da kuskuren da aka yi wajen rubuta sunan tsohon shugaban kasar.
Domin samun ma’anar abun da aka rubuta da harshen Faransancin, mun yi amfani da manhajar fassara ta google translate wanda ya fassara mana da turanci kamar haka “DEATH OF FORMER PRESIDENT OF NIGERIA OLUSEGUN OBASANJO”. Wato “MUTUWAR TSOHON SHUGABAN NAJERIYA OLUSEGUN OBASANJO.
Mun kuma lura cewa an hada bidiyon a shafin TikTok ne kuma yana dauke da sunan shafin (Wazobia.fma), mun ziyarci TikTok inda muka nemi mai shafin. Daga nan sai muka ga cewa bidiyon da wazobia.fm din ta raba ranar Talata 5 ga watan Satumba 2023 ya sami alamar Like guda 158 kuma an raba har sau 202.
Sai muka lura kuma an kashe wurin yin tsokaci a karkashin labarin da ke shafin na TikTok
Da muka duba sashen da ke dauke da bayanan mai shafin nan kuma mun ga cewa yana da mabiya 1000, kuma daga sauran bidiyoyin da ya wallafa mun lura cewa yana yawan sanya hotunan mutuwar sananun mutane, kama daga mawaka, ‘yan fim da ma fastoci a Najeriya.
Mun yi binciken mahimman kalmomi domin gano ko akwai rahotanni daga kafafen yada labarai dangane da wannan batun amma ba mu ga komai ba.
Dan haka sai muka tuntubi mai magana a madadin tsohon shugaban, Kehinde Akinyemi ta hanyar sakonnin tes da waya inda ya tabbatar mana cewa babu abun da ya sami tsohon shugaban kasar yana cikin koshin lafiya kuma a halin yanzu ma yana kasar waje.
“Ya na kasar waje! Da safen nan ma ya na tsakanin Tanzania da Kenya.” a cewar Akinyemi.
A karshe
Bincikenmu ya nuna mana cewa wannan bayanin karya ne. Mai magana a madadin tsohon shugaban ya karyata zargin.