Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Babbar kotun jihar Kano zata gurfanar da tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje da matarsa, da wasu mutane shida wadanda gwamnatin Jihar ta shigar da kararsu bisa zargin almundahana da dukiyar al’umma.
Hukunci: Gaskiya ce! Bincike ya tabbatar mana da cewar babbar kotun jihar Kano za ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar hade da matarsa da kuma wasu mutane shida.
Cikakken Bayani
Shafuka da dama a soshiyal mediya sun dauki labarin cewa ana zargin tsohon gwamnan jihar Kano tare da matarsa da wasu mutane shida da almundahana da yin sama da fadi da dukiyar al’umma. Kuma ma har an sa ranar 17 ga watan Afrilu a matsayin ranar da Babbar kotun jihar Kanon zata gurfanar da tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje, da matarsa, da wasu mutane shida wadda gwamnatin Jihar ta shigar da kara bisa zargin almundahana da dukiyar al’umma. Ana iya ganin labarin a wadannan shafukan: Leadership Hausa, DCL Hausa, legit.ng.
Wannan labarin ya dauki hankalin jama’a sosai inda mutane sama da miliyan daya suka latsa alamar Like, wasu 150 kuma suka yi tsokaci yayin da aka sake raba labarin sau 39. Wannan ya janyo ra’ayoyi mabanbanta a wajen tsokacin da ke karkashin labarin.
Daga cikin tsokacin da aka yi, mafi yawan wadanda suka bayyana ra’ayoyinsu dangane da batun, sun goyi bayan gurfanar da tsohon gwamnan a gaban kuliya tare da matarsa. Alal misali, Hayatu Muhammed cewa ya yi “Wannan ya yi kuma Allah ya sa hakan ya dore a Najeriya.” Sai dai kuma akwai wadanda ba su gamsu ba, da wadanda ke karyatawa suna cewa ba zai yiwu ba, Kamar Mal Awal wanda ke cewa “ba za ku iya ba”.
Ganin yadda wannan batun ke daukar hankali da mahimmancin da ya ke da shi ga yanayin siyasar kasar ya sa DUBAWA ta dauki nauyin tabbatar da sahihancin wannan batun.
Tantancewa
Dubawa ta fara da binciken mahimman kalmomi, a manhajar tantance labarai da hotuna na google domin samun tabbaci. Mun samu bayanin da ke cewar babban lauyan jihar Kano kuma Kwamishinan shari’a, Haruna Dederi ne, ya tabbatar da hakan, inda ya ce za a gurfanar da Ganduje ne tare da matarsa da wasu mutane shida.
Wadanda ake tuhumar sun hada da Abdullahi Umar Ganduje, Hafsat Umar, Abubakar Bawuro, Umar Abdullahi Umar, Jibrilla Muhammad, Lamash Properties Ltd, Safari Textiles Ltd, da Lesage General Enterprises. Gwamnatin Jihar Kano wadda ta fara tuhumar mutanen, ta bayyana shirinta na gabatar da shaidu 15 da za su tsaya a gaban mai shari’a Usman Na’aba na babbar kotun jihar.
“Gaskiya ne. Mun shigar da karar kuma za a fara zama a ranar 17 ga watan Afrilu, 2024,” in ji shi.
Dederi, ya bayyana muhimmancin rikon amana a harkokin mulki, inda ya ce, “Abin da shi (Ganduje) bai gane ba shi ne ba zai iya guje wa wanna rana ba,
tabbas za ta zo, kuma hakan zai zama izina ga kowa, har da mu da muke cikin gwamnati yanzu.”
“Yana cewa ba za mu iya gurfanar da shi ba, ya manta cewa laifin na karkashin nau’in laifukan jiha ne,” in ji shi.
“Ba batun laifin tarayya ba ne, kuma mun shigar da kara a gaban mai shari’a Liman kan hakan.”
A Karshe
Saka ranar da babban kotun jihar Kano ta yi domin gurfanar da tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje, da matarsa, da wasu mutane shida wadda gwamnatin Jihar ta shigar da kara bisa zargin almundahana da dukiyar al’umma Gaskiya NE.
Mai binciken ta yi wannan aiki ne karkashin shirin gano gaskiya na DUBAWA 2024, a shirin samun kwarrewa na Kwame KariKari da hadin gwiwar Debora Majingina Habu, a kokari na fito da “gaskiya” a aikin jarida da inganta ilimin aikin jarida a fadin kasar.