African LanguagesHausa

Da Gaske Shugaba Buhari Ya Ce Bai San Da Yajin Aikin Malaman Jami’a Ba?

Zargi: Hoton wani shafi da aka dauka na cewa wai shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce bai san da yajin aikin da malaman jami’a ko kuma kungiyar ASUU ke yi ba

A bana, kungiyar malaman jami’a ta ASUU ta kaddamar da yajin aikinta ne a ranar 14 ga watan Fabrairun 2022 da sunan wai gargadi ga gwamnati, kuma a lokacin kungiyar ta ce yajin aikin na tsawon makonni hudu ne. Sai dai, daga nan ta kara wa’adin da watanni biyu don bai wa gwamnatin karin kwaniki na cimma bukatun da kungiyar ta gabatar mata.

Mahimman bukatun sun hada da sake tattauna yarjeniyar da suka kulla da gwamnatin tarayya a shekarar 2009 da kuma yin amfani da tsarin UTAS wato bayyana gaskiya da rikon amana a jami’a wajen biyan albashin ma’aikatan.

Ranar alhamis 5 ga watan Mayu 2022 aka fara yada hoton wadansu kalamai wadanda ake zargi na shugaba Buhari ne inda ya ke cewa wai shi bai ma san da batun yajin aikin ba. Wannan labarin an fara ganin shi a wani shafin da ake kira World of News wato duniyar labarai da turanci. A cewar rohoton, shugaban Najeriya ya yi bayani kamar haka 

“Ban san cewa ASUU na yajin aikin ba, kuma ban san tun yaushe ta fara ba, ba wanda ya fada mun cewa kungiyar ASUU na yajin aiki,” a cewar Buhari.

Tantancewa

Da farko dai babu wata kafar yada labarai mai suna”World of News.” Da muka yi wa labarin binciken kwa-kwaf mun gano cewa babu sunan dan jaridan da ya wallafa labarin kamar yadda aka saba rubutawa a duk wani labari mai sahihanci. Sai dai a maimakon sunan an sanya wadansu lambobi da harrufa kamar haka: kqce4

Binciken da muka yi ta yin amfani da mahimman kalmomi kuma bai nuna mana wani labarin da ke da dangantaka da wannan ba. Sai dai mun gano wadansu rahotannin da aka yi a jaridun The Guardian da Premium Times wadanda ke cewa ministan kwadago Chris Ngige ya fadawa shugaban kasa irin cigaba da kuma tattaunawar da su ke yi da wakilan kungiyar dangane da matakin yajin aikin malaman jami’a.

Wannan ya nuna cewa shugaban kasar na sane da labarin yajin aikin duk da cewa bai tofa albarkacin bakin shi dangane da batun ba. Ko a jawabin da ya gabatar a bukin tunawa da ranar ma’aikata na dunyia wanda aka yi ranar daya ga watan Mayun 2022 inda mataimakinshi Yemi Osinbajo ya wakilce shi, ba’a ji komai dangane da yajin aikin ba.

Haka nan kuma da mu ka yi nazarin hoton da aka yi amfani da shi wajen dora labarin mun gano cewa an gyara hoton ne ta yadda zai saje da irin labarin da ake so a bayar. Akwai inda wadansu rubutun suka hau kan wasu sa’annan kuma launukan da ke kan hoton sun nuna cewa an kwaskware abubuwa a jikin hoton.

A karshe 

Shugaba Muhammadu Buhari bai taba cewa bai san da maganan yajin aikin malaman jami’a ba domin bincikenmu ya nuna mana cewa babu wani labarin da ya fita dangane da wannan batun a duk kafafen yada labarai da ya karfafa wannan zargin. Bacin haka akwai rahotannin da aka yi a baya wadanda suka tabbatar da cewa shugaban na sane da yajin aikin kuma yana samun rahoton duk wata tattaunawa da aka yi da malaman.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button
Translate »