Zargi: Wani mai amfani da shafin Tiwita ya yi zargin wai dan takarar mukamin shugaban kasa a zabukan 2023, Peter Obi, ya ce da ya karbi bashin kudi domin Najeriya ta kashe a kan gudanarwa na yau da kullun ya gwammace kowa ya zauna da yunwa
Peter Obi, tsohon gwamnan jihar Anambra na neman tsayawa takarar shugabancin Najeriya a karkashin inuwar jam’iyyar PDP. Tsohon gwamnan ya kasance dan takarar mukamin mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar a zabukan da aka gudanar a shekarar 2019.
Kwanan nan wani mai amfani da shafin Tiwita mai suna Jack (@Jack_ng01), ya wallafa wani zargin mai cewa Peter Obi ya ce gara a zauna da yunwa da ya karbi bashi dan a kashe kan gudanarwar yau da kullun.
“A karkashin jagoranci na, ba kwabon da za’a ara wai dan a lakume kan aiyukan yau da kullun, da haka gara mu zauna cikin matsanancin yunwa,” aka rawaito shi yana cewa.
Wanda ya wallafa wannan labarin ya hada da hoton wani bidiyo daga gidan talbijin na Arise inda ya ke zargi wai a nan ne Obin ya yi wanann furucin.
Da yawa daga cikin masu amfani da shafin sun bayyana ra’ayoyinsu dangane da batun a wurin yin tsokaci. Wani mai suna Comcombility (@A_zhed) ya ce babu kasar da ke rayuwa ba tare da cin bashi ba.
“Shi ne ya taba cewa babu kasar da ta taba rayuwa ba tare da cin bashi ba, bacin haka Najeriya ma za ta iya kara ciwo bashin. Sai dai abin da ya fi mahimmanci shi ne abin da ake kashe kudin a kai,” ya ce.
Wani mai suna Austyno (@AustynoUsh) kuwa cewa ya yi bangaren furucin da aka yi amfani da shi bai mi shi adalci ba tunda ba abin da ya ke nufi ke nan ba.
“Ka na magana kamar nufinsa shi i ne ya jefa jama’a cikin yunwa alhali kuma ba abin da ya ke nufi ke nan,” a cewar @AustynoUsh
Francis Eze (@francisneze) tambaya ya yi game da hikimar karbar aron kudi dan a cinye, inda ya ce dan takarar ba ya adawa da karbar bashi, kashe bashin kan abubuwan da ba za’a ga alfanun shi da ido ba ne ya ke adawa da shi.
“Ba ya adawa da bashi. Ya na adawa ne da sanya kudin a abubuwan da za su lakume shi ba tare da an ga wani tasirinsu a al’umma ko ma tattalin arzikin kasar baki daya ba. Ana karbar bashi dan kashewa a kan abinci ne kadai? idan aka yi haka, ta yaya za’a biya ke nan?
Shin Peter Obi ya yi wannan furucin da gaske ko dai an dauki maganar da ya yi ne an kara mi shi gishiri?
Tantancewa
Mun yi bincike mun gano ainihin bidiyon hirar da ya yi a gidan talbijin na Arise. An yi wa bidiyon taken “Muna bukatar wanda zai fitar da mu daga (APC) – Peter Obi” Lokacin da muka ga bidiyon, ranar 19 ga watan Afrilun 2022 mutane sama da 110,000 suka kala.
Da mu ka kalli bidiyon mai tsawon minti 38 da sakan 15 mun lura cewa wajen minti 13 da 16 na birar. Mr. Obi ya yi maganan kan yadda Najeriya ke ciyo bashi dan kashe wa kan ayyukan yau da kullun bayan da aka yi mi shi tambayar ko ya gamsu da yanayin bashin Najeriya.
“Ya kamata mu fayyace abin da mu ke ciyo wa bashi; ya yi mun tambaya, ya ce me zan yi? Ni zan yi abin da ya banbanta da abin da ake gani yanzu. Idan zan ciyo bashi, ‘yan Najeriya za su san dalilin cin bashin kuma tilas a yi amfani da shi wajen sarrafa abubuwa. Babu wanda zai kashe kwabo ko dala kan ayyukan yau da kullun, da a yi haka gara an zauna da yunwa. Shi ya sa na fada wa kowa cewa ba abin da za’a sake rabawa, dole mu sake gina kasarmu dan ‘ya’yanmu su sami kyakyawar makoma.”
A Karshe
Bincikenmu ya nuna mana cewa zargin wai dan takarar shugaban kasa Peter Obi ya ce da a ci bashi dan lakume shi a ayyukan yau da kullun gara an zauna da yunwa gaskiya ne. Dan takarar kuwa ya bayyana hakan ne domin ya jaddada adawarsa da cin bashi dan batarwar yau da kullun abin da a ra’ayinsa babbar matasal ce ga ci-gaban tattalin arziki.