Zargi: Wani sakon da ke yawo a WhatsApp na zargin wai gwamnatin tarayyar Najeriya na bai wa ‘yan Najeriya wani tallafin kudi dan samun abin dogaro da kai a karkashin abin da ake kira Asusun Tallafwa Matasan Kasa ko kuma National Youth Empowerment Fund a turance.
A shekarun da suka gabata gwamnatin tarayyar Najeriya ta gabatar da shirye-shirye da yawa domin samar wa ‘yan kasa abin dogaro da kai, a wani mataki na rage talauci da habbaka yanyin tattalin arzikin kasa da na jama’a baki daya.
Misalan irin wadannan shirye-shiryen sun hada da shirin N-Power mai mayar da hankali kan matasan da ba su da aikin yi da kuma shirin ciyar da daluban makaranta wanda gwamnatin tarayyar a karkshin mulkin shugaba Muhammadu Buhari ta kaddamar a shekarar 2016.
Kwanan nan wani sakon da ke yawo a WhatsApp ya na zargin wai wani fam ko kuma takardar neman tallafin gwamnati a karkashin National Youth Empowerment Fund na shekarar 2022 ya fito.
Bisa bayanan da aka yi a sakon, asusun tallafin, wanda ke da saukin samu da zarar an cike takardun, duk cikakkun ‘yan kasa wadanda ke da bukatar tallafi wajen neman illimi ko kuma sana’o’in su na iya samun tallafi daga wannan asusun.
Wannan asusun a cewar sakon na da burin bayar da tallafin N150,000 zuwa N550,000 ga duk dan kasar da ke tsakanin shekaru 13 – 65 na haihuwa kama daga shekarar 2022 zuwa 2024.
Sakon ya kuma kara da cewa a yanzu haka, gwamnati na kan biyan kudin watan Afrilu. Bisa la’akari da yadda wannan zargi ya dauki hankali, babu shakka zai iya janyo matsala, shi ya sa muka dauki matakin gudanar da bincike dan gano gaskiyar lamarin.
Tantancewa
DUBAWA ta gudanar da binciken kalmomi inda ta fara da kalmomin “youth empowerment fund” wato asusun tallafin matsa, kamar yadda aka bayyana a sakon ba tare da samun nasara ba.
Daga nan ne sai muka ga abin da aka kira Presidential Youth Empowerment Scheme (P-YES) Wato shirin shugaban kasa na tallafawa matasa, to sai dai ba mu ga alamun an yi wata kira ga jama’a da su cika takardun samun tallafin ba.
Ainihin shirin na P-YES shiri ne da gwamnatin Buhari ta kaddamar a shekarar 2020 kamar yadda shafin Nairametrics ya bayyana a wannan rahoton. Kamar yadda kuma aka bayyana a shafin ofishin sakataren gwamnatin Najeriya, a hukumance ofishin ne ke lura da shirin wanda ke karkashin jagoranci mai bada shawarwari na musamman ga shugaban kasa kan harkokin da suka shafi matasa da dalubai.
Batutuwan da ke sanya alamar tambaya kan sahihancin labarin
Abin mamaki, wani nazarin da aka yi kan adireshin da ke dauke da sakon a Domainbigdata, wani shafin yanar gizo-gizon da ake amfani da shi wajen tantance sahihanci wadanda ke da shafi, ya bayyana cewa masu amfani da yanar gizo da yawa sun kai karan shafin da ya dauki wannan labarin bisa zargin shi da karya doka.
Kasancewar wasu bayanai marasa gaskiya daga shaidu shi ma ya sanya alamar tambaya kan sahihancin batun. Yawancin masu zamba a shafukar yanar gizo na yawan amfani da wannan dabarar wajen jan hankalin jama’a. Adiresoshin da aka yi amfani da su ba na kwarai ba ne amma kuma ana amfani da su wajen yaudarar wadanda ba su ji ba su gani ba.
DUBAWA ta kuma gano tutocin kasashen Afirka ta kudu, Cote d’Ivoire, Ghana, Gambiya, Najeriya da Uganda a shafin farko, wanda ke marabtar maziyarta zuwa shafin. Babu shakka wannan na nufin an kirkiro shafin da nufin yaudarar wadanda suka fito daga wadannan kasashen ke nan.
Adireshin ko kuma din da ke kai mutane shafin shi ma irin shafin da ake kira ‘Bitly URL’ ne. A shekarar 2008 aka kirkiro Bitly URL a matsayin wata hanya ta rage tsawon adiresohsin shafuka. Bitly kan takaita adiresoshi fiye da milliyan 600 a shafukan sadarwa, gajerun sakonni da wasikun email a kowani wata. Dama can an kirkiro shi ne da burin taimakawa ‘yan kasuwa wajen sanya adiresoshin shafukan kayayyakin da su ke saidawa cikin sauki, ta yadda za su ja hankalin jama’a.
To sai dai masu zamba na cigaba da amfani da Bitly URLs wajen raba bayanan karya domin kara yawan mutanen da ke ziyartar shafukansu. Hasali ma sakon ya sami yaduwa yadda ya yi sakamakon wadansu sharudda da umurnan da aka sanya a shafin ne.
Kamar yadda aka bayyana a cikin sakon, shafin ya kan bukaci duk wanda ke sha’awar ganin sakon da ya raba da wani ko wasu kafin a bayar da izinin shiga shafin. Yawancin masu zamba a shafukan sadarwa na yawan amfani da wannan dabarar don kara yawan mutane a shafukansu.
A Karshe
Bincikenmu ya nuna mana cewa babu wani tallafin N150,000 zuwa N550,000 da gwamnati ke baiwa matasan Najeriya da sunan wani Asusun Tallafa Wa Matasan Najeriya dan Dogaro-da-kai.