African LanguagesHausaNewsletters & Updates

Dalibai masu koyon aikin binciken gaskiya a DUBAWA  karo na 2023 sun kammala karatu

Wadanda suka kammala karatu tare da tallafin gidauniyar Prof. Kwame Karikari, wani yunkurin DUBAWA , kungiyar da ke binciken gaskiyar batutuwa a yankin yammacin Afirka sun halarci bukin da aka shirya musu ranar 15 ga watan Nuwamban 2023.

Bukin wanda aka yi a Abuja Birnin Tarayya ya kawo karshen watanni shiddan da suka shafe ana ba su makaman aikin da za su taimaka mu su wajen gudanar da bincike mai sahihanci daura da aikinsu a fannin jarida. Daga cikin wadanda suka kasance a taron har da jakadan Spain a Najeriya Juan Sel, da shugaban cibiyar kula da sabbin dabaru a aikin harida da tabbatar da cigaba na CJID Akintunde Babatunde, sai kuma darektan gudanarwa na CJID Adebimpe Abodunde, da David Ajikobi editan Africa Check.

Tobi Oluwatola da Kemi Busari, CJID wato babban darekta da editan DUBAWA sun halarci taron su ma amma ta ytanar gizo, inda suka yaba wa daliban da suka kammala karatun saboda himmar da suka nuna da ma yadda suka daraja aikin jarida sadda su ke karatun.

An fara bukin ne da jawabi na maraba daga Mr Babatunde, wanda ya bayyana mahimmancin da bincike ua ke da sho a fagen aikin jarida da ma burin CJID na illimantar da mutane kan kafafen yada labarai a yankin yammacin Afirka baki daya.

Daya daga cikin abubuwan da suka fi daukar hankali lokacin bukin shi ne jawabin da jakadan Spain Mr Sel ya gabatar wanda ya jaddada mahimmancin da binciken gaskiya ke da shi wajen samun yardar al’umma. Ya bayyana irin nauyin da ke zuwa da damar yada bayanai, sa’annan ya kuma yaba wa CJID saboda yadda ya ke bayar da fifiko dan ganin labarai sun bayana gaskia an kuma yi su cikin adalci.

Kafin a gabatar mu su da satifiket, daliban wadand su ma akwai wadanda suka halarci bukin da kansu da kuma wadanda suka halarta ta yanar gizo daga wau kasashen zankin yammacin Afirka sun bayyana yadda shirin ya taimaka mu su wajen inganta kokarinsu a yadda ya shafi tantance bayanai kafin a wallafasu.

Lambobin yabsaboda ayuka masu tasiri

Bukin ya yi la’akari da dalibai uku saboda irin cigaban da suka samu.Ibrahim Adeyemi shi ne ya zo na farko saboda binciken da ya yi dangane da yadda ake samun labarai na bogi da marasa gaskiya lokacin zabe. Yayin da Kabir Yusuf ya zo na biyu, sai kuma Varney Dukuly, daga Laberiy, shi kuma ya zo na uku. A jawabinsa na karbar karramawar da aka yio masa, Ibrahim Adeyemi yta bayyana godiyarsa ga gidauniyar saboda jagorancinta a fagen aikin jarida wanda ke cigaba da sauyawa a cikin wannan zamanin.

Gidauniyar Kwame Karikari na DUBAWA yunkuri ne da ke nuna burin CJID na ilimantarwa da kuma karawa ‘yan jarida dabaru da kwarewa dan gudanar da aikinsu yadda ya kamata a yankin yammacin Afirka da ma koya mu su irin dabarin da su ke bukata wajen yaki da bayanan karya da wadanda ke yaudarar jama’a da na bogi.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button