African LanguagesFact CheckHausa

Tsohon bidiyo daga Afirka ta Kudu ne ake amfani da shi a sunan tashin hankali a Najeriya.

Getting your Trinity Audio player ready...

Zargi: A wani bidiyon da ke nuna wasu ‘yan daba na dukar wata mata, ana zargi ‘yan daban na da alaka da wata kungiyar ‘yan fashi.

<strong>Tsohon bidiyo daga Afirka ta Kudu ne ake amfani da shi a sunan tashin hankali a Najeriya.</strong>

Sakamakon Bincike: Babu cikakkiyar gaskiya! Bidiyon tsoho ne daga shekarar 2018 wanda kuma abu ne da ya faru a Afirka ta Kudu ba Najeriya ba. Haka nan kuma babu wata majiya mai sahihanci da ta goyi bayan labarin da aka wallafa a shafin twitter tare da bidiyon.

Cikakken bayani

Bidiyon wasu mutane yawancinsu maza suna cin zarafin wata mata ya bayyana a shafukan soshiyal mediya a dandaloli irin su X da taskokin blogs

Daniel Marven ya wallafa wani budiyo mai tsawon dakiku 48 a shafinsa na X. Bidiyon ya nuna wasu mutane suna dukar wata mata, sa’annan daga karkashin bidiyon aka yi mi shi taken “Ta na aiki a banki. Kuma duk sadda ake je cire kudi mai yawan gaske, sai ta sanar da ‘yan fashi. Ba’a san yadda aka yi ba yau dau dubu ya cika. An kama ‘yan fashin kuma sadda ake mu su tambayoyi suka tona mata asiri a matsayin mai ba su bayanai.”

Mutane miliyan shida suka kalli bidiyon an yi tsokaci 5,640 wasu 5,102 sun ajiye shi dan sake dubawa nan gaba tun bayan da aka wallafa labarin ranar biyu ga watan Oktoban 2023.

Real Mugie, wanda ya yi tsokaci ya ce: Mutane sun daina daraja mata. Wannan ya yi yawa.”

A wurin tsokacin dai, wani mai amfani da shafin  @Petite Human, ya rubuta: “Me ya sa ba su mika ta ga mahukunta ba? Ta yaya kuka sami wadannan bayanan? Kun yi wa ‘yan fashin tambayoyi da kan ku ne ko dai jita-jita ce kawai? Ko da ma me ta yi, babu dalilin da zai sa ku yi ma ta irin wannan cin mutuncin.

DUBAWA ta dauki nauyin fayyace wannan zargin saboda wadannan ra’ayoyin mabanbanta, yadda batun ya dauki hankali da ma mahimmancin wasu daga cikin tambayoyin da aka yi wajen tsokacin da ke bukatar amsoshi.

Tantancewa

Mun yi nazarin bidiyon da kyau dan samii karin bayanai. Mun ji wasau daga cikin mutanen da suka yi dadanzo suna cewa “obeah,” wani abu ne da aka yi imani da shi a irin addinan gargajiya na Afirka wanda ke da nasaba da tsafi, kuma ana samun shi a kasar West Indies da ke yankin kaibiyan da ma wasu yankunan kasashen da ke Kudancin Amurka. Wannan na nufin abun bai faru a Najeriya ba.

Mun kuma yi amfani da mahimman kalmomi muka yi bincike inda mu ka sa “Matar da aka tube aka yi duka yayin da wasu ke ihu Obeah.” Daga nan sai bibiyon ya sake bayyana amma da kwanan watan tara ga watan Oktoban 2019, (kusan shekaru biyar da suka gabata) tare da taken “‘yan daba a Afirka ta Kudu sun yi wa wata mata tsirara dan ta na fita da ‘yan Najeriya da sauran baki.” mun kuma sake gano wannan bidiyon dai a wani shafin inda can kuma ya na dauke da kwanan watan sha tara ga watan Afrilun 2018, da wani taken na daban, mai cewa “maus bore sun duke wata mata har sai da suak yi mata tsirara.”

Wannan na nuna cewa bidiyon ya tsufa sosai kuma tun shekarar 2018 ake amfani da shi ana mi shi take daban a duk sadda ya bulla.

Mun yi kokarin gano mafarin bidiyon tun da babu wanda muka gani da take iri daya amma ba mu iya ganowa ba.

Daga nana mun yi kokarin yin wani binciken na mahimman kalmomi dan mu ga ko wata kafar yada labarai mai nagarta ta wallafa labarin ki kuma dai wani abnki ko ofishin ‘yan sanda amma ba mu sami wani abu haka. 

A Karshe

Labarin da ake yada wa tsohon bidiyo ne daga shekarar 2018. Wannan na nufin labarin da mai amfani da shafin X din ya wallafa yaudara ce kawai.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button