Getting your Trinity Audio player ready...
|
A lura: A wannan labari akwai tarin hotuna masu motsa zuciya, mai kallo sai ya kula.
Wakili Abdu, dan shekaru 63, ya dawo daga gona da maraice a Sabon-Gida. Mintuna kalilan sai ya dauki buta da fatanyarsa ya zagaya bayan bukkarsa inda ciyayi suke nan fa ya durkusa da kwabe wandonsa.
A duk lokacin da Malam Abdu ya ji ya matsu ya gwammace ya je yayi bayan gida kamar yadda kakanninsa suka koya masa. Yayi amanna cewa amfani da bandaki ko masai ko shadda ko salga duk na mata ne, maza su yanki daji su yi kashinsu a ko’ina.
“Amfani da bandaki abune na mata, koda ace an gina bandaki akasari mata da yara ne suke amfani da su, mu mazaje mun fi zuwa daji, wannan shine abin da muka amince da shi a al’adance,” haka ya fadawa DUBAWA a lokacin da yake zaune a gaban gidansa.
Malam Abdu, yana zaune a gaban bukkarsa wanda ya dauki hoto: Sunday Awosoro/DUBAWA.
Yadda malam Abdu bai damu da amfani da bandaki ba, ba bakon abu ba ne a yankunan karkara a Najeriya, inda a tsawon lokaci al’ada ta karfafa wannan dabi’a ta yin kashi ko bahaya a waje, musamman a tsakanin mazaje. Wannan al’ada ita ke zama karan tsaye ga kokari da ake yi na kawar da dabi’ar yin kashi a waje a Najeriya.
A Sabon-Gida, yankin al’umma a karamar hukumar Kafin-Hausa a inda ya taso yin bayan gida /(kashi) a bainar jama’a abu ne da ke zama sananne duk da cewa akwai hadakar jami’ai da ke aikin hana wannan dabi’a da tsaftar gari ta kasa (NTGS) da ma Asusun kula da Yara na UNICEF sun bayyana jihar Jigawa a matsayin wacce aka dena samun masu yin bayan gida a waje wato Open Defecation Free (ODF) ya zuwa ranar 26 ga Oktoba,2022.
Bayyana jihar a wannan matsayi ya zama abin alfahari da ma yin biki inda asusun ya bayyana Gwamna Umar Namadi a matsayin jakadan yaki da bayan gida a bainar jama’a (UNICEF’s ODF ambassador.)
Kafin wannan sanarwa Ibrahim Hannungiwa, kwamishinan albarkatun ruwa a jihar ya bayyana cewa jihar Jigawa da tallafin asusun na UNICEF ta kashe kudade miliyan dari (N500 million) don gina bandakuna a wuraren taruwar jama’a.
Bayanai da aka tattaro daga ma’aikatar albarkatun ruwa ta tarayya (FMWR) sun bayyana cewa ‘yan Najeriya miliyan 48 akasari mazauna yankunan karkara na yin bahaya ko bayan gida ko kashi a bainar jama’a duk da gabatar da shirin ci gaba mai dorewa na SDG. A shekarar 2016 Asusun na UNICEF ya kaddamar da shirin kawo karshen yin bayan gida a bainar jama’a a Najeriya nan da shekarar 2025. Ya zuwa watan Disamba, 2023 kananan hukumomi 117 ne daga cikin 774 suka kasance wadanda ba a kashi a bainar jama’a (ODF).
A yayin da ta bayyana tafiyar hawainiya da shirin ke yi ma’aikatar albarkatun ruwan ta tarayya FMWR ta bayyana cewa “Najeriya na bukatar gina bandakuna miliyan uku da dubu 300 duk shekara, kafin ta iya samar da kananan hukumomi 224 da ba a kashin a bainar jama’a a duk shekara” kafin cika burinta a 2025.
Ta yaya Jigawa ta zamo wacce ba a bahaya a fili (ODF)?
Kamar yadda aka yi fashin baki karkashin shirin na (NTGS da ODF) abubuwa na farko da ake dubawa sun hadar da cewa “duk wasu iyalai su zama suna da bandaki da abubuwan wanke hannu” a mataki na gaba kuma a samar da tsaftataccen ruwa (WASH) a wuraren da al’umma ke taruwa kamar cibiyoyin kula da lafiya da makarantu da kasuwanni.
Bayan haka wata karamar hukuma an bayyanata a matsayin wacce babu masu yin bahaya a cikinta (ODF) lokacin da hadakar masu fafutukar ganin an sam ar da tsafta ta kasa NTGS suka ziyarci kaso 20 cikin dari na yankunan al’umma da suka ziyarta, inda suka tabbatar da cewa gidajen iyalai da makarantu da cibiyoyin lafiya da kasuwanni da tashoshin mota duka an tanadar masu da bandakuna da wuraren wanke hannaye.
A cewar hadakar yaki da yin ba haya barkatai a bainar jama’a ta NTGS dukkanin kananan hukumomi 27 na jihar ta Jigawa sun cika wadannan ka’idoji, kamar yadda rahoton Asusun kula da yara na UNICEF ya ba da rahoto, jihar ta fitar da tsari na kawo karshe bahaya a bainar jama’a (ODF) wanda ya hadar da samar da ci gaba a matakin kananan hukumomi da jiha inda aka kaddamar da dokar kar ta kwana da tabbatar da samar da kudade ga sashi kula da tsaftar na WASH a dukkanin matakan kananan hukumomi.
Gwamnan jihar ta Jigawa ya kaddamar da kamfe na yaki da bahaya a bainar jama’a tare da bayyana shirin ba da lambar yabo ga dukkanin mazauna wani yanki da suka kula, ya kuma karfafa hada kai da masu sarautun gargajiya don tabbatar da bin dokar da hada kai da ‘yansanda da sauram masu kayan sarki a kowace karamar hukuma tare da hukunta duk wadanda aka kama suna bahaya a bainar jama’a.
A watan Yuli 2024 kasa da shekaru biyu da kaddamar da dokar yaki da wannan dabi’a, DUBAWA ta ziyarci yankunan al’umma a kananan hukumomi a jihar ta Jigawa Birniwa da Hadejia da Malam-Madori da Gwaram da Kiri Kasama da Kafin Hausa da Guri don duba ina aka kwana game da bin dokar hana yin bahaya a bainar jama’a.
‘Muna bukatar abinci kafin bandakuna’
A garin Sabon-Gida shugaban al’umma ya bayyana cewa a bisa kiyasi magidanta 200 daga cikin 2,300 suna da shadda ta bahaya ko Masai na gargajiya wato wanda da ake gina rami da wasu 20 da ke da irin wannan shadda da aka rufewa da kankare, duk da cewa DUBAWA ba ta tabbatar da ganin hakan ba, Masai ko shadda da akan haka da hannu suna da saukin yi mazaunan kan samo murfi ko silaf na kankare 2 su rufe masan ko shaddar ko salga.
Sabanin mutanen Sabon-Gida inda a al’adance ba a karfafa gwiwar maza su yi amfani da masai kasancewar ana cewa bandaki na mata ne, mutanen da ke zaune a Taljare wani kauye a karamar hukumar Birniwa ko maza ko mata suna son amfani da bandakuna, sai dai abin takaici babu wani gida da ke da bandaki a Taljare.
Amadi Sule, shugaban al’umma a yankin ya danganta hakan da matsalar tattalin arziki, a baya suna amfani da masai na gargajiya sai dai suna rushuwa ne a lokacin damina, kasancewar kuma mutane na yankar daji su je bahaya sai mutane suka saduda da kokarin neman wata mafitar.
“ Tabbas a baya muna da bandakuna amma yanzu duk sun rushe saboda ruwan sama saboda ba a sanya masu siminti. Mun fi son amfani da bandakuna, matsalar dai ita ce bamu da kudin yin mai kyau, muna fafutuka ta ciyar da iyalanmu ba maganar bandaki ce a gabanmu ba, Ciyarwa ce a gabanmu,” a cewarsa.
Bandaki na Muhammed Bulama’. Wanda ya dauki hoton: Sunday Awosoro/DUBAWA.
Muhammed Bulama, shine mai garin Ando a karamar hukumar Kiri Kasama yace bandakuna 50 daga cikin 300 ne kawai ake amfani da su a tsakanin gidajen kauyen. Kayan da ake amfani da su wajen ginawa a wajen ne ake samu a bayanin da Bulama yayi wa DUBAWA yace mutane sun fi rungumar bandakuna na gargajiya don sun fi sauki domin na gargajiyar ana haka su a kudi kamar 10,000 yayin da na siminti ake ginawa akan 100.000.
“Kamar yadda ka sani ne gina bandaki na bukatar kudi. A yanzu mutane na fama da matsalar tattalin arziki mutane suna fama ne da abin da iyalansu za su ci ne, ba ta gina bandaki suke ba. Wadanda ke shiga daji su je kashi ko bahaya matalauta ne, amma akwai wasu da suke ginawa na kasa ko yumbu wanda a lokuta da dama suke rushewa saboda rashin kwari.” a cewarsa.
Ruwa ke rusa mana bandakuna
Dukkanin kananan hukumomi 7 da DUBAWA ta ziyarta sun bayyana cewa bandakunan gargajiya da suke ginawa suna ruftawa a lokacin damina hakan ya sanya dole sai sun sake ginawa a tsawon watanni shida. Wannan matsala ta fi gawurta a garin Karidu, wanda yanayin wajen ya sanya ruwa ke taruwa a cikin masai ko shadda, wannan yana rushewa duk bayan watanni biyu.
A shekarar 2023, shirin samar da tsaftataccen ruwan sha ga yankunan karkara na WASH a jihar ta Jigawa ya samar da shadda ko masai ko salga a cikin gidaje 500 a yankin Karidu a karamar hukumar Guri, sai dai a wannan yanki da ke zama matattarar ruwa duk kokari na haka masai na nufin wani masan zai iya ruftawa, wasu mazaunan yankin sai suka rika samun babbar jarka suna binnewa a matsayin masai ko shadda sai dai suna saurin cika saboda rashin tsari na kwashewa. Wannan ya sanya al’umma suka koma yin bahaya a waje kasancewar masai kimanin 400 da aka haka sun rufta.
“Muna kira ga gwamnati ta kawo mana dauki ta hanyar gina masai na siminti wanda zai iya daukar lokaci mai tsawo.” A cewar Maimuna wata uwa mai ‘ya’ya guda hudu.
Maimuna Muhammed tana nuna yadda masai ko shadda ta rufta a farfajiyar gidansu. Wanda ya dauki hoto: Sunday Awosoro/DUBAWA
Wakili Kaigama, da ke zama mai gari a kauyen ya tabbatar da cewa al’umma da ke zaune a yankin sun fi kaunar amfani da bandakuna don bahaya a cikin sirri sai dai basa iya haka masai a gina da siminti saboda yanayi na matsin tattalin arziki, yayin da dama suke fafutuka ta samun bukatuwar yau da kullum, Duk da sanin kalubalen da ke tattare da samun bukatar tasu Malam Kaigama sai ya nemi da a sama masu jarkoki don binnesu a kasa su zama masai ko shadda.
Fadakar da jama’a ba tare da tilastawa ba
A lokacin da gwamnatin wannan jiha ta kaddamar da yaki da yin bahaya a bainar jama’a ta gabatar da wasu dokoki da suka mayar da aikata yin bahayar a bainar jama’a a matsayin babban laifi a kowace karamar hukuma.
Mazaunan yankin sun tabbatar da kamfen din da ma bayyana dokar, wasu ma sun tabbatar da samun wani tallafi, sai dai bayan kaddamarwa sai aka dena ganin jami’an gwamnati ko wani aiki. Babu wani mutum da aka taba kamawa ko aka yi masa horo saboda yana bahaya a waje, jami’an WASH ba su nuna wa mai dauko rahoton wannan doka ba da ake magana akai, koma ba a ganta ba.
A shekarar 2021 gwamnati ta gabatar da taron fadakarwa a kauyen Gabasmari wani kauyen Birniwa, inda a baya mazauna yankin suke ganin babu wani dalili na gina masai ko shadda, a lokacin ziyartar kauyen an fadakar da jama’a kan illar da ke tattare da yin bahaya a waje inda anan aka samar masu da butoci da sabulun wanki, wannan ya sanya mutane da dama suka rika gina masai sai dai anan ma kamar sauran sai suka rika ruftawa.
Usman Galadima, guda ne daga cikin masu fadakarwa a kauyen yace da fari mazauna kauyen sun rungumi dabi’ar yaki da yin bahayar a bainar jama’a sai kuma suka yi watsi da ita “saboda babu wani tallafi da suke samu daga bangaren gwamnati.”
Masai ko shadda gidan Malam Galadima a bayan bukkarsa kafin ta rufta. Wanda ya dauki hoto: Sunday Awosoro/DUBAWA.
Mataimakin dagacin kauyen Muhammad Abubakar, yace gwamnati ta fito da doka ta hana yin bahaya a waje ko bainar jama’a da fari, sai dai wannan yunkuri ya ci tura saboda rashin ci gaba da kokari, sai mutane suka koma ci gaba da yin bahayarsu a waje.
“Sun kawai fadakar da mu suka bamu butoci da sabulun wanki. Ina tabbatar maka da abin ya ci gaba mutane za su rungumi abin su kaucewa yin bahaya a bainar jama’a.”
Kamar Gabasmari, mazauna Duleri da Taljare da Matamu da Aljari a karamar hukumar Birniwa da Garin-Ando a karamar hukumar Kiri-Kasama da Aji-Bukara da Karidu a karamar hukumar Guri suma sun bayyana cewa an kai masu irin wannan tallafi amma an sake komawa gidan jiya.
Mazaunin Karidu na taka inda aka yi masai . Wanda ya dauki hoto: Sunday Awosoro/DUBAWA
A kokari na kai tallafin an bukaci mazaunan Matamu su biya naira 700 don a gina masu masai na gargajiya a cewar mai garin Sani Magini babu mazaunin kauyen da zai iya biyan wannan kudi.
“ Zan iya ba da wurin da za a haka, amma idan aka ce sai an biya kudi to babu shakka ba zan iya biyan kudin ba, ko yanzu zan iya ba da wurin da za a gina idan akwai wadanda za su gina min.” A cewarsa
Makarantu ma ba a barsu ba
Jihar Jigawa karkashin shirin Asusun kula da kananan yara na UNICEF da ya duba batun tsafta da ruwa a Najeriya (SHAWN) ya samar da wurin dibar ruwa a makarantar firamaren Matamu sai dai wannan waje ya dena aiki, haka nan wani bangaren na bandakin maza da mata ya rufta, sai yara suka koma yin bahaya a wajen wankin hannayen bayan bandakuna da bayan ajin karatunsu, abin takaici DUBAWA ba ta samu damar tattaunawa ba da malaman makarantar kasancewar sun tashi daga makaranta.
Makarantar firmaren Taljari bandakin ya dena aiki. Wanda ya dauki hoto: Sunday Awosoro/DUBAWA.
Yanayin makarantar firamaren Taljari shima yayi kama da na firamaren Matamu. Umar Sule hedimasta ko shugaban makaranta na firamaren Taljari ya fada wa DUBAWA cewa dalibai na yin bayan gida a waje sai dai laifin na gwamnati ne saboda rashin ba da kulawar da ta dace.
“Dukkaninsu suna shiga daji ne tun da babu bandaki, gwamnati ta gina bandaki sai ta yi watsi da shi yanzu bandakin ya rufta saboda rashin kulawa, a cewarsa.
Yanayi shima a sakandaren Sabon-Gida babu dadi kasancewar dalibai na yin kashi ko bayan gida a azuzuwan karatu da ba a amfani da su kasancewar bandakuna basu da kyau.
A firamaren Matsaro da ke Hadejia karamar hukumar (Hadejia), malamai ne kawai ke da bandaki da ake amfani da su, yayin da aka bar dalibai na bahaya a bayan aji-aji.
A Madachi, duk da cewa bandakuna da aka gina da siminti na makarantar jeka ka dawo suna aiki amma na firamaren yankin sun rufta.
Dalibai na kashi a ciki da wajen ajujuwansu a sakandaren Sabon Gida da firamaren Madachi da firamaren Matsaro da ke Hadejia. Wanda ya dauki hoto: Sunday Awosoro/DUBAWA.
Shelkwatar karamar hukuma ta inganta
Manyan garuruwa a kananan hukumomi bakwai da aka ziyarta sun inganta a kawar da yin bahaya a bainar jama’a, da yawa gidaje na zamani ne sabanin gidajen laka a kauyika. Hakazalika da dama wadannan gidaje an gina su tare da bandakuna gidajen laka kadan kuma an gina masu masai ko shadda da siminti da kankare. Sai dai har yanzu mutane na bin gefen hanya suna bahaya ko a kangwaye da wuraren zubar da shara.
A garin Hadeja akwai mutane masu gidajen wanka idan za ka yi kashi 100 idan kuma fitsari ne naira 50, duk da haka ana samun masu yin bahayar a gefen hanya da cikin kasuwa, irin wannan kuma shi aka lura da shi a Malam Madori a karamar hukumar Malam Madori.
Kashin mutane da aka gani a babbar kasuwar Hadeja. Wanda yayi hoto: Sunday Awosoro/DUBAWA.
A garin Dutse, babban birnin jihar ta Jigawa DUBAWA ta ga wani yaro mai suna Mustapha Waje “a tashar motar da ta gudanar da aikin bincikenta “ yana kora kashi a cikin kwata ko magudanar ruwa da aka tsara ruwan wanka ya rika bi. Wannan magudanar ruwa ta koma wurin bahaya ganin yadda mutane ke kora kashinsu cikinta. Duk da cewa masu gudajen wanka da ake biyan kudi suna karbar naira 150, mutane sun gwammace su rika kashinsu a kwata ko magudanan ruwa.
.
Mustapha Waje, yana kora ruwa ya tura bahaya zuwa cikin magudanan ruwa a tashar mota da aka gudanar da bincike akanta a Dutse. Wanda ya dauki hoto: Sunday Awosoro/DUBAWA
A sabuwar tashar motar Malam Umar Maladi a Guri, direbobi sun lalata bandakuna ta yadda suka zama ba wanda ke son shiga bahaya, wannan ya sanya da dama suka koma yin bahaya a kewaye.
Halin da tashar motar Malam Umar Maladi ke ciki kenan a Guri. Wanda ya dauki hoto: Sunday Awosoro/DUBAWA.
Asibitoci suma na fuskantar wannan matsala
Ba duka yankunan al’umma da DUBAWA ta ziyarta ba ne suke da cibiyoyin kula da lafiya, a wasu yankunan al’umma kan yi tafiya ta kimanin awa guda kafin su isa wata cibiyar lafiya. Sai dai ga Sabon Gida da Matamu dukkaninsu suna da cibiyoyin kula da lafiya a matakin farko. Abin takaici kamar makarantu a wannan yanki bandakunansu basa aiki.
A Matamu cibiyar kula da lafiya a matakin farko duka bandakunan da ke cikin ginin da wadanda suke waje basa aiki, DUBAWA ta lura cewa wadannan kayayyaki basa samun kulawa kuma babu wanda zai yi bayani kan dalilin da jawo hakan.
Abdullahi Gamani, wanda shine jami’i da ke kula da cibiyar kula da lafiya a matakin farko ta Sabon Gida yace hanyar shigar ruwa zuwa bandakin ce ta samu matsala tun a watan Afrilu wannan ya sanya ta toshe.
‘‘Matsalar ta fara ne watanni uku da suka gabata lokacin da famfo ya fashe tsakanin bandakin da inda in an yi bahaya yake zuwa ya taru, mun yi kokari mu gyara abin ya ci tura don haka muka rufe bandakin. Bamu da bandaki amma muna da inda mutane ke zuwa su yi bayan gida da yin wanka inda aka haka rami. Muna bukatar gyara ne baki daya.”
A lokacin da ya fara aikin kula da asibitin Malam Gamani yayi kokari wajen hada kai da al’umma don gyara bandakin amma abin ya fi karfin aljihunsa.
The Halin da asibitin na Sabon-Gida da Matamu ke ciki kenan, wanda ya dauki hoto: Sunday Awosoro/DUBAWA.
Jawaban da jami’an gwamnati ke yi
A jihar Jigawa jami’ai na kokari na ci gaba da rike kambun jihar na zama wacce babu masu yin bahaya a bainar jama’a (ODF) a cikinta saboda kalubalen da suka dabaibaye nasarar. Abba Tahir shine jagoran shirin na WASH a Jigawa yace yayin da ake samun cigaba a wannan fafutuka samar da bandakuna na wucin gadi da suke lalacewa shi ya sa al’umma ke komawa gidan jiya.
“Abin da zan fadi nan shine, idan kana neman wuraren da mutane ke bahaya a waje a duk karamar hukumar da ka je, ka je can kauye za ka samu wasu na da dabi’ar yin bahaya a bainar jama’a.”
“Matsalar ita ce ci gaba da dorewa, a lokacin da muka yi wannan aiki mutane na kiranmu suna godiya suna fada mana cewa dabi’ar mutane na sauyawa, kuma garuruwansu sun zama masu tsafta. Babu tsarin samar da bandaki da zai zama mai kwari da zai dauki lokaci mai tsawo. Masu gari da mabiyansu suke ba da hadin kai wajen gina masai ko shaddar da aka samar.” a cewarsa.
Da yake tabbatar da abin da DUBAWA ta gano shugaban shirin samar da ruwa mai tsafta WASH a karamar hukumar Birnewa ya bayyana cewa kokari na ci gaba da rike kambun zaman jihar a matsayin wacce aka dena yin bahaya a bainar jama’a yana tafe da babban kalubale kasancewar ana yin ruwan sama mai karfi wanda kanyi sanadi na ruftawar masai ko salga.
Ya bayyana cewa sashin na WASH a Birnewa na karbar naira 100,000 ne duk wata don aikin kula da motoci daga Janairu zuwa Agusta,2024 wanda aka tsara a rika amfani da su don ziyartar gani da ido kan halin da bandakunan suke ciki, sai dai a nasu bangaren mazauna yankin sun bayyana cewa tun bayan da aka zo a ka fadakar da su tun da fari basu sake ganin jami’ai ba daga WASH.
Malam Umar ya kara da cewa a wasu lokutan su kan dauki mutane a yankunan al’umma don su yi aikin fadakarwa a gare su suna ba su naira 1000 don tallafa wa ayyukansu na fadakarwa.
Sai dai kuma duk da cewa akwai doka kan masu yin ba hayar baa samun daukar hukunci kan mutanen ko gidajen da babu bandaki. Ya danganta hakan da matsi na tattalin arziki sannan za a iya samun turjiya daga mutanen da ke zaune a yankunan.
“Wannan lokaci ne da mutane babu abin da ya dame su illa abin da za su ci, ba lallai ma su saurara ba, sannan ba za a iya tursasa su ba. Wannan shine halin da muke ciki. Za a iya samun hargitsi idan aka nemi a tilasta masu,” a cewarsa.
Ado Isah jagoran shirin WASH a kaframar hukumar Kafin Hausa shima nasa labarin haka yake, yace wadanda basa bin umarnin ba a hukunta su sai dai a karfafa masu gwiwa su rungumi dabi’ar amfani da bandaki. Yace ana samun yawaitar masu bahaya a bainar jama’a a wuraren da ke kusa da kogi ko koramu da yankunan da ke fama da ambaliyar ruwa.
Sabanin Birniwa, yace su basa samun kudaden naira 100,000 don gyara motoci sama da shekaru biyu da rabi, wannan ke zama cikas ga kokarin zagayawa don ganin halin da al’umma ke ciki game da amfani da bandakuna.
“ Ba zai yiwu ba a hukunta mutane, muna dai basu shawara su samu shadda ko salga ko masai a yankunansu, wasu lokutan ambaliyar ruwa na tashin al’umma, don haka suna hijira daga wani waje zuwa wani, Ba za su iya gina masai na dindin ba, wasu wuraren mutane na ci gaba da amfani da bandakuna don yin bahaya sai dai wurare da suke fama da ambaliyar ruwa, suna kokari su gyara bandakunansu daga masai na gargajiya na laka zuwa na siminti da kankare.”
Kokari da DUBAWA ta yi na tuntubar mai rikon kujerar shugabancin hukumar da ke samar da ruwan sha a yankunan karkara (RUWASA), a Jigawa yaci tura kasancewar duk kiran da aka yi masa yaki dauka sannan sakonnin da aka tura masa bai amsa ba.
Asusun UNICEF yayi tsokaci
Chiranjeevi Tiwari, jami’in UNICEF mai kula da shirin samar da tsaftataccen ruwan sha na WASH, ya bayyana yanayin na jihar Jigawa da matsayin zamiya, inda al’umma da fari suka cika kai’idoji na yin ban kwana da yin kashi a bainar jama’a ODF sai daga bisani suka yi baya saboda wasu dalilai da suka hadar da yawaitar al’umma da yin hijira da rushewar masai ko shadda ko salga da aka rika samu. Yayi alkawarin tattaunawa da ofishin UNICEF da ke Kano. Ya kara da cewa UNICEF na tallafa wa gwamnatoci ne ba daidaikun iyalai ba.
Mista Tiwari ya kara da cewa abubuwan da ke gaban UNICEF bai tsaya a Jigawa kadai ba tun da aka bayyana ta a matsayin wacce ba a samun yin bahaya a bainar jama’a. Yace alhaki ne da ya rataya a wuyan gwamnatin jiha da ta kananan hukumomi su jajirce wajen ci gaba da rike kambun jihar a nasarar da ta samu a baya.
“A wasu lokutan idan kudaden tallafi suka kare kamar a Jigawa ba lallai ne mu samu wani gagarumin aiki a jihar ba, wannan shine kalubalen da muka fuskanta, kasancewar kudaden da muke da su suna da iyaka. Mun mayar da hankali kan wasu yankunan da ake da kalubalen aikin, idan aka kammala aiki gwamnati ita ke da hakki na ci gaba da tabbatar da ganin cewa aikin ya dore, su tabbatar da ganin aikin bai samu tawaya ba, bai kuma rushe ba.” A cewarsa.
‘Shedar zama jiha da ba a bahaya a bainar jama’a ta (ODF certificate) za a iya janyewa- Ma’aikatar albarkatun ruwa ta kasa
A tattaunawar da DUBAWA ta yi da Okpara Chisoma, jagora mai kula da yaki da bahaya a bainar jama’a a ma’aikatar albarkatun ruwa da tsaftar muhalli ta kasa ta bayyana rashin jin dadi kan halin da aka samu kai a jihar Jigawa na koma baya kan batun na nasarar da tayi a baya a yaki da yin bahaya a waje, inda take cewa:
“Abin takaici ne ganin irin tarin ayyuka da aka yi na kokarin fadakar da al’umma da sauran abubuwa sai bayan an bayyana jihar da a zama wacce ba a yin bahaya a bainar jama’a sai muke jin wadannan labarai.”
Misis Chisoma ta tabbatar da cewa ana ci gaba da tattaunawa kan yadda aikin zai dore, sai ta bayyana bukatar da ke akwai na ci gaba da bibiya da shigar da al’umma inda ta bayyana bukatar daukar alhaki daga bangaren gwamnatin jiha da ta kananan hukumomi da masu rike da mukaman gargajiya da bangarori masu zaman kansu da kafafan yada labarai.
“Har ila yau muna bukatar a ci gaba da dabbakawa, hanyar kuma da ta rage shine ci gaba da bibiya kafa da kafa daga bangaren gwamnatoci a matakin kananan hukumomi da jiha da masallatai da majami’u a tabbatar da ganin abin na ci gaba da dorewa, alhaki ne da ya rataya a wuyansu su tabbatar da dorewar nasarorin da aka cimma a cewarta.
Da aka tambaye ta wane mataki suke dauka idan aka samu fadowa ko zamiya daga wata nasara da aka cimma, Misis Chisoma ta bayyana cewa gamayyar yaki da rashin tsafta ta kasa NTGS tana da ka’idoji na “tantancewa ta kasa da ba da sheda” wannan ya hadar da ba da maki daga lokaci zuwa lokaci a yankunan da aka bayyana da zama wadanda ba a yin bahaya a cikinsu. Ta bayyana cewa za a iya janye shedar da aka basu muddin suka gaza ci gaba da rike kambunsu na al’umma su ci gaba da gujewa yin ba haya a waje.
DUBAWA ta kuma tuntubi Adeyemi Ajose, jami’i da ke jagorantar hadakar tabbatar da tsfatar ta kasa NTGS. yaki amincewa a tattauna da shi ya ce duk wata bukata a gabatar da ita ta hanyar tuntubar ma’aikatar albarkatun ruwa.