Image source: BBC
|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Za ka sha mamaki yadda a wani kauye a arewacin Najeriya za ka ga labarai na yaduwa cikin hanzari ta hanyar shafukan WhatsApp da tarukan al’umma. Wata rana an yada irin wannan wallafa wacce aka jirkita inda ake da’awar cewa wani dan siyasa shugaban al’umma na shirin yaudararsu. Duk da cewa wannan wallafa karya ce an yada ta sau daruruwa abin da ya jawo sanya tsoro da bacin rai dama tayar da hankali. Wani shafin da ba a sani ba shi yada labarin don kawai a haifar da fargaba a tsakanin al’umma don cimma manufar wata kasar waje wacce zaa ga tasirinta a yada labaran da aka jirkita su da yin kutse (Foreign Information Manipulation and Interference (FIMI).
FIMI na nufin abubuwa da dama ga jama’a, ya danganta da matakin iliminsu ko bayanan da suka hadu da su. Sai dai abu guda da ya bayyana shine ya zama hanya ko makamin yada labaran karya da gangan, musamman a yankunan da samun bayanai ingantattu suke da iyaka. Mutane da ke a can kasa suna da iyaka wajen samun bayanai, suna kuma dogara ne da jin labarai daga wane zuwa wane, su aka fi yaudara da irin wadannan dabaru.
Isar da sakonnin na ketare da ke zama FIMI na amfani da raunin mutane ta hanyar tsara labaran karya da aka tsara su don wasu al’umma masu wata al’ada da siyasa da wasu bayanai da suka shafi zamantakewa.
Ta yaya ake Cutar da Al’umma
1. Mayar da kafafan sadarwar zamani da manhajojin isar da sakonni kayan fada
Al’umma tun daga tushe suna dogara da kafofi kamar Facebook da WhatsApp da wasu manhajoji da aka tanada a cikin al’umma don samun bayanai ko labarai. Wadanna ke jagorantar yada irin wadannan labarai na FIMI na amfani da wadannan kafafe wajen yada labaran cikin hanzari a lokuta da dama ana amincewa da su ba tare da bincike ba, ga misali a lokacin gangamin yaki da tsadar rayuwa a 2024 #EndBadGovernance a arewacin Naeriya masu zanga-zangar sun rika daga tutar kasar Rasha don nuna siyasar wani yanki, wato nuna yadda Rasha ke da ta cewa a siyasar wasu kasashe kamar Nijar, kafafan sadarwar zamani Social media sun taka muhimmiyar rawa anan wajen yada labarin da ke zama na karya don nuna irin tasirin Rasha a harkokin cikin gidan wata kasa. Wannan ya nunar da yadda Masu yada Labaran Tasirin Kasashen Waje FIMI suke yaudarar mutane tun daga tushe ta yadda suke kambama sakonnin siyasa ta hanyar isar da sakonni da za a iya gani da ido ko da kuwa wadannan sakonni ba su ne manufofin kasashen na ketare ba.
2. Amfani da yare da abin da al’umma suka fi fahimta
Masu yada Labaran Tasirin Kasashen Waje FIMI sau tari suna amfani da yarukan al’umma su isar da sakonni na karya da gangan ta yadda za a gansu kamar na gaske da za a iya dogara su.Ga misali labarin karya da aka rubuta a harshen al’umma kan wasu tsare-tsaren gwamnati kan yadda za a dora wa manoma haraji mutane za su dauka nasu ne kuma abin da za su yarda da shi musamman idan aka yada shi ta hanyar wasu mutanensu a yaransu.
3. Amfani da masu fada aji da wakilai
Wasu mutane da al’umma ta yarda da su kamar malamai da shugabannin addini da wasu ‘yanwasan kwaikwayo masu fada aji, masu yada labaran karyar na tasirin kasashen waje (FIMI) na amfani da su don isar da sakonninsu na karya.Duk sa’ilin da mutanen da ake mutuntawa suka yada labaran da ke zama na karya. Labaran kan samu kima su kuma yadu sosai ga misali idan akwai wani malami ko shugaban addini da ake mutuntawa cikin rashin sani ya yada wani labari da aka wallafa wanda ke zama na karya da aka yi kan batun lafiya, al’umma da dama za su dauki labarin da gaske, saboda ikonsu a cikin al’umma, mutane za su amince tare da tallafawa wajen sake yada labarin ba tare da yin wata tambaya ba a kansa.
4. Amfani da rashin ilimin mutane
Wasu mutanen da ke a can kasa basu da ilimi ko iliminsu na boko ya takaita ko kuma suna da rauni wajen samun sakonni na gaskiya, masu yada labaran karyar na tasirin kasashen waje (FIMI) na amfani da rashin ilimin mutane ta yadda za su yada labaran da za su zama kamar daga hukumomi suke amma babu shakka na karya ne. Ga misali akwai masu yada labarai cewa magungunan gargajiya sun fi tasiri a wajen maganin cutar cizon sauro ko maleriya.
5. Amfani da jin tsoro da rashin tabbas
Masu yada labaran karyar na tasirin kasashen waje (FIMI) sau tari suna ribatar tsoro da rashin tabbas na al’umma da ke a can kasa, suna yada jita-jita a kan tashin hankali da barkewar annoba da wasu abubuwan da ke haifar da fargaba a tsakanin al’umma. Ga misali masu yada labaran karyar na tasirin kasashen waje (FIMI) na iya fitar da wani labari cewa wata kabila da ke fada da makotanta na shirin kai farmaki a wani kauye don su sanya tsoro da rudani ko ma su iya haifar da tashin hankali a kokari na mayar da martani ga labarin karyar da aka tsara.
6. Dasa labarin karya ta hanyar kafafan yada labarai na cikin gida
Kananan kafafan yada labarai na cikin gida wadanda ba lallai suna da hanyar samun bayanai daga masu aikin gano gaskiyar labari ba, suna daga cikin wadanda masu yada labaran karyar na tasirin kasashen waje (FIMI) ke son su kama. Wadannan kafafe na iyawa cikin rashin sani su wallafa ko su yada labarin da ke zama na karya ne da aka yi don yaudara, wanda zai iya isa ga tarin al’umma. Wani gidan rediyo na iya yada labarin karya cewa wani kayan tallafi na gwamnati an karkatar da su zuwa kasar waje , abin da zai kawo rashin yarda a tsakanin al’umma wadanda suka dogara da wannan tallafi don ci gaba da rayuwa.
Me yasa Labaran karyar na tasirin kasashen waje (FIMI) ke Tashe
Karancin Ilimin kafafan sadarwar zamani: Da dama al’umma a wadannan yankuna basu da sanin dabaru na iya gano hakikanin abubuwan da ake sanyawa a intanet ko su san yadda za su tantace su, wannan ya sanya cikin sauki masu yada irin wadannan labarai na tasirin kasashen ketare ke wasa da hankulan mutanen a yankunan.
Amincewa da kalaman baka: Cikin wasu al’umma da suka yarda da juna wannan ya kan sa mutane basa ba da wata kulawa da ta dace ga bayanan da suke zuwa masu, wannan aminta na sawa ko da labaran karya aka ba su sai su amince ba tare da sun bincika ba.
Rashin wadatattun masu aikin gano gaskiyar labari: Wadannan al’umma akan barsu su zama cikin sauki wajan wasa da hankulansu ganin masu aikin gano gaskiyar bayanai basu da yawa, ko su dogara da wasu hanyoyi nasu na binciko gaskiyar bayanai.
Ta yaya za a kalubalanci yada labaran da ke da tasirin kasashen na ketare FIMI
1. Samar da horo na ilimin yada labarai (MIL)
Ilimantar da al’umma kan yadda za su iya gano labaran karya shine babban jigo a yaki da FIMI. Karamin horo na iya sanyawa mutane su fahimci bukatar gano asalin labari da gano dabarun yaudara da amincewa da wasu kafofi da ke zama abin dogaro. Shirye-shirye da DUBAWA ke yi a Najeriya na taimakon al’umma su samu ilimin irin wadannan dabaru da fahimtar wane irin labari ne za su amince da shi.
2. Hadakar gano gaskiyar labarai a cikin al’umma
Kungiyoyi da ke gano gaskiyar labarai a cikin al’umma da aka aminta da mambobinsu za su iya bayyana labaran da ke zama na karya ta hanyar yada labaran da ke zama na gaskiya, aikinsu na iya tasiri ya taimaka wa al’umma su zama suna da sani.
3. Kambama muryoyi da aka yarda da su
Ta hanyar mutunta wasu fitattu a cikin al’umma kamar shugabanni na addini ko masu fada aji zai taimaka wajen yada labarai na gaskiya, idan irin wadannan mutane suka yi bayani a harshen da al’umma suke fahimta sakonninsu za su iya fatattakar bayanan da ba na gaskiya ba. Taruwa da ake a masallatai da majami’u wurare ne da zaa iya amfani da su.
4. Tallafar ayyukan jarida daga tushe
Tallafa wa ‘yanjarida daga tushe ta hanyar basu horo da abubuwan da suke bukata wannan zai taimaka masu su rika ba da rahoto na gaskiyar labari da gano labaran karya. Idan akwai ‘yanjarida daga tushe da suka samu horo wannan zai taimaka masu ta yadda za a samu bayanai ingantattu ko labarai sahihai duk da cewa basu da isassun kayan aiki.
Karshe
Idan ana so a dakile bazuwar yada labaran karya na tasirin kasashen ketare FIMI, shi ya kamata a fara bawa kulawa saboda tasirinsu na shafar al’umma a kananan yankunansu ta hanyar ribatar amincewarsu da sauyin da ake samu a al’adarsu, da takaice su da samun bayanai sahihai.
Don kawo karshen wannan sai an ilimantar da al’umma da ilimin dabarun aikin jarida a dukkanin matakai a tallafa wa ayyukan gano gaskiyar labarai da daga martabar muryoyin mutane da al’umma ta aminta da su.
