African LanguagesHausa

Dukan yara:  Illar rashin aiwatar da dokar kare hakkin yara ta Najeriya

Getting your Trinity Audio player ready...

Gabatarwa

Dokar kare hakkin yara ta 2003 ita ce dokar da ta tabbatar da ‘yancin kowane yaro a Najeriya. Dokar dai tana da sassa 278 kuma ta kunshi batutuwa da dama da suka hada da ‘yancin samar da ayyukan kiwon lafiya, haramta auren yara da kuma rawar da gwamnatocin jihohi ke takawa wajen kare hakkokin da aka gindaya a cikin dokar.

Dokar ta ayyana cewa, yaro shi ne mutumin da bai kai shekaru 18 da haihuwa  a duniya ba.

A cewar hukumar kare hakkin dan adam ta Najeriya, ya zuwa yanzu jihohi 24 cikin 36 na Najeriya sun amince da dokar a matsayin doka a cikin jihohohin, sai dai akwai jihohi goma sha biyu 12 da har yanzu ba su amince da sanya dokar a cikin dokokinsu ba.

Yadda ake ci gaba da take hakkin yara

Duk da dokokin da suka kare hakkokin kananan yara a Najeriya, har yanzu ana ci gaba da samun cin zarafin yaran ta hanyar fyade, safarar su da tilasta musu aikin karfi har ma da dukan su.

A ‘yan kwanakin nan wani bidiyo ya karade shafukan sada zumunta dake nuna yadda wasu mata da miji ke dukan wasu yara yan mata biyu; Hajara Goni mai shekaru 13 da Hauwa Goni, ‘yar kimanin shekaru 11, saboda sun ciro mangoro a cikin gidansu.

Wannan bidiyon dai ya janyo mahawarori da dama ya kuma tunzura mutane da dama inda har wasu lauyoyi suka rubuta wa hukumomin tsaro korafi akan su dauki mataki kan wannan cin zarafin da aka yi wa yaran.

Rundunar ‘yan sandan jihar Borno ta dauki mataki bayan an kai yarinyar asibiti domin duba raunin da ta ji tare da kama ma’auratan da suka ci zarafin yarinyar da ma yada bidiyon da suka dauka a shafukan sada zumunta.

Me dokar kare hakkin yara ta ce?

Jihar Borno da jihohi 23 na Najeriya suka sanya hannu kan wannan dokar ta kare hakkin yara, tare da amincewa da ita.

Binciken Dubawa ya gano cewar sashi na 11 na dokar kare hakkin yara ta 2003, ya ce kowane yaro yana da hakkin a mutunta shi, kuma ta bayyana cewa babu wani yaro da za a yi w rauni a jiki, ko a tunanin, ko cin zarafi, ko yin biris da shi, ko musgunawa, da ta hada da lalata da su. 

Haka ma sashi na 221 na dokar ya jaddada cewa babu wani yaro da za a yi masa hukunci ta hanyar bugun jiki ko dauri gidan yari.

Wannan yana nuna cewa duk wani nau’i na azabtarwa ga jiki ko duka da zai iya haifar da rauni ko cutar da yaro, tamkar take hakkin yaro ne a karkashin wannan dokar.

Abin da kwararru suka ce

Dubawa ta tuntubi wani lauya a jihar Bauchi, Muhammad Bashir Abdullahi ya ce rashin aiwatar da dokokin da aka kafa na kawo cikas ga kare hakkin yara a Najeriya musamman yadda ake cin zarafin su, “dokar kare haƙƙin yara ta fada a fili cewa duk wani nau’in cin zarafi, ciki har da duka, haramun ne.” 

Ya kara da cewa idan kotu ta tabbatar da laifin da ake zargin wadannan ma’aurata na dukan yaran, za a iya yanke musu hukuncin zaman gidan kaso ko kuma tara ko duka biyun.

“Yana da matukar mahimmanci a tuna cewa aiwatar da dokar kare hakkin yara ya bambanta daga jiha zuwa jiha, don haka ya kamata a duba dokokin jihar Borno ta musamman” inji Bashir.

Sai dai Sidi Bello, lauya a jihar Sokoto, ya shaida wa Dubawa cewa dokar ba ta tanadi hukuncin ga wanda ya taka hakkin yara ba, ta yi bayani ne kawai akan hakkokin yara da ya kamata iyaye da malamai, da ‘yan uwa da kuma sauran al’umma ya kamata su kiyaye.

Sidi Bello ya kara da cewa za a iya gurfanar da wadannan ma’auratan a kan haddasa rauni ga yaran kuma idan kotu ta same su da laifi za ta yanke musu hukuncin da ya dace.

“Ita matar za a gurfanar da ita akan hada baki da taimakawa, yayin da shi kuma mijin za a iya gurfanar da shi akan laifin haddasa rauni” Sidi Bello ya ce ya danganta da raunin da yaran suka ji.

Dukanin Lauyoyin Sidi Bello da Muhammad Bashar sun shaida wa Dubawa cewa, akwai bukatar jihohin da ba su amince da dokar ba su yi hakan cikin gaggawa, haka kuma “su tabbatar da cewa hukumomin tsaro da na shari’a suna aiwatar da dokar kare haƙƙin yara yadda ya kamata.”

Hakama sun ba da shawarar a wayar da kan al’umma akan wannan doka domin sai mutane sun san da ita ne za a samu nasara wajen hana cin zarafin yara a Najeriya.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button
Translate »