African LanguagesHausa

Abinda Muka Gano Kan Da’awar Shigar Da Dabbobi A Saudiyya Lokacin Aikin Hajji, Da Kuma Yawan Mahajjata na Shekara ta 2024

Getting your Trinity Audio player ready...

Cikakken Bayani 

Wani labari da aka rika yadawa a kafafen sada zumunta musamman shafin Facebook na cewa “Hukumomi a Saudiyya sun tabbatar kimanin raguna miliyan 1 da dubu 700 sun isa birnin Jiddah, adadin yawan Alhazan da ke aikin Hajjin bana domin yin Hadaya.”

Labarin wanda aka wallafa a shafukan yada labarai na Hausa daban-daban kamar su Hausa Daily Times, News24 Hausa da kuma Fikrah TV, ya fara bayyana ne a ranar Lahadi 9 ga watan Yuni 2024.

Abinda Muka Gano Kan Da’awar Shigar Da Dabbobi A Saudiyya Lokacin Aikin Hajji, Da Kuma Yawan Mahajjata na Shekara ta 2024
  • Hoton da aka zakulo a shafin Facebook

Wannan dai na zuwa ne yayinda maniyyata aikin hajji daga kowane fanni na duniya ke tururuwa zuwa kasar Saudiyya domin gudanar da aikin hajji, a matsayinsa na daya daga cikin shika-shikan musulunci.

Yanka dabbobi ko kuma Hadaya a ranar sallah wata muhimmiyar ibada ce wajiba da mahajjata ke yi a ranar sallah babba a matsayin cikamakon aikin hajjin su.

Ganin yadda labarin ya soma jan hankali, Dubawa ta yi bincike akan da’awar da aka wallafa a shafukan sada zumunta.

Da’awa 1: Adadin Raguna miliyan daya da dubu dari bakwai hukumomin Saudiya suka shigar a kasar domin yin Hadaya.

Abinda Muka Gano Kan Da’awar Shigar Da Dabbobi A Saudiyya Lokacin Aikin Hajji, Da Kuma Yawan Mahajjata na Shekara ta 2024

Hukunci: Yaudara ce! Bincike ya nuna cewa Saudiyya tana shigar da dabbobi domin yin hadaya amma labarin da ake yadawa a yanzu tsoho ne, tun a watan azumi ne Saudiyya ta sanar da shigowar dabbobi miliyan 1.7.

Tantancewa

A yayin bincike mun gano cewa kasar Saudiya na shigar da dabbobi kasar kowace shekara domin samar da isassun dabbobin da mahajjata zasu yanka domin yin ibadar Hadaya.

Mujallar NatureMedicine ta wallafa wani bincike a ranar 3 ga watan Yunin 2024, wanda ta bayyana cewa a can baya, maniyyata ko dai su yanka dabbobin ne da kan su a wajen aikin Hajji ko kuma su kula da yadda ake yankani.

A shekara ta 1983, Gwamnatin Saudiyya ta kirkiro da shirin kula da yadda ake yankan dabbobi wanda bankin ci gaban Musulunci ke kula da shi, tayi hakan ne domin baiwa alhazai damar biyan kudin yankan dabbobi ta hanyar yanar gizo, tare da kare su daga cudanya da dabbobi kai tsaye ko ziyartar inda ake yankan dabbobin.

Sai dai labarin da ake yawo da shi cewa “kimanin raguna miliyan 1 da dubu 700 sun isa birnin Jiddah, domin yin Hadaya” ba sabo bane domin ba wata kafar yada labarai da ta wallafa shi kuma ta bayar da madogarar labarin ta, har da shafin Life In Saudi Arabia dake dandalin X. 

Haka kuma wani shafin StartupPakistan sun wallafa irin wannan labarin a shekarar da ta gabata ba tare da bayyana madogarar su ba.

Amma a binciken da muka yi mun gano cewa wannan labarin ya bayyana ne tun a watan maris, yayin da aka samu karin bukatar nama a lokacin azumin watan Ramadan.

Kamar yadda jaridar GulfNews ta ruwaito, ma’aikatar noma Saudiyya ta bayyana cewa kasar ta shigo da shanu miliyan 1.7 cikin watanni biyu da suka gabata sakamakon karuwar bukatar naman da ake samu a watan Ramadan da kuma kusantowar lokacin aikin Hajji.

Da’awa 2: Mutane miliyan daya da dubu dari bakwai ke gudanar da aikin hajji bana.

Abinda Muka Gano Kan Da’awar Shigar Da Dabbobi A Saudiyya Lokacin Aikin Hajji, Da Kuma Yawan Mahajjata na Shekara ta 2024

Hukunci: Karya ce! Hasashen da aka yi mahajjatan zasu haura adadin mutane miliyan daya da dubu dari takwas da suka yi aikin hajji a shekarar da ta gabata. 

Tantancewa

A binciken da muka yi bamu samu wani labari daga hukumomin Saudiyya dake ayyana cewa mutane miliyan daya da dari bakwai ne zasu yi aikin hajji, tun farko dai hasashen cewa mahajjatan zasu kai miliyan biyu. A shekarar da ta gabata mutane miliyan daya da dubu dari takwas ne suka gudanar da ibadar a fadin duniya. 

Bayanin da suka fitar dangane da wannan batun, hukumomin kasar Saudiyya sun ce suna hasashen mahajjatan daga cikin gida da kasashen waje zasu haura adadin mahajjatan shekarar da ta gaba, domin a ranar Talata 11 ga watan Yunin 2024 maniyata miliyan daya da dubu dari biyar sun riga sun isa kasar Saudiyya kuma ana dakon isowar wasu, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AP ya ruwaito

Adadin mahajjata na ci gaba da karuwa tun bayan farfadowa daga sauyin da annobar korona ta kawo na takaita yawan mahajjata dake zuwa daga kasashen duniya, a shekara ta 2019 kafin annobar an samu mahajjata miliyan biyu da dubu dari biyar

A ranar Jumu’a 14 ga watan Yuni 2024 ake sa ran soma gudanar da aikin hajji a hukumance, yayin da za a yi sallah a ranar Lahadi 16 ga wata. 

A karshe

Da’awar cewa an shiga da Raguna miliyan daya da dubu dari bakwai a Saudiyya domin yin Hadaya Yaudara Ce! Bincike ya nuna cewa tsohon labari ne. Hakama Hasashe ya nuna mahajjatan wannan shekarar zasu kai kusan miliyan biyu sabanin da’awar da aka yada cewa miliyan daya da dubu dari bakwai ne.

An yi wannan binciken ne karkashin shirin Binciken Gaskiya na DUBAWA wato Indigenous Language Fact-Checking 2024, tare da hadin gwiwar Vision 92.5FM, Sokoto, domin dabbaka labarun “gaskiya” a cikin aikin jarida da karfafa ilimin yada labarai.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button
Translate »