Zargi: Wani mai amfani da shafin Tiwita ya yi zargin wai Farfesa Babagana Zulum, gwamnan jihar Borno na sayen katunan zabe ko kuma PVCn wadanda suka rasa matsugunnensu gabanin zabukan 2023

Wannan zargin ba gaskiya ba ne kuma abin da aka gani kudi da abinci da sauran kayayyakin more rayuwa ne kawai ake rabawa yayin da gwamnan Bornon ke ziyara a karamar hukumar Damboa.
Cikakken bayani
Borno, daya daga cikin jihohin da ke yankin arewa maso gabashin Najeriya ya yi rauni sosai daga rikicin ‘yan ta’adda da dakarun gwamnati wanda aka yi ta tabkawa tun daga 2009. Sakamakon haka milliyoyin mutane sun rasa matsugunensu dan dole sun je suna samun mafaka a sansanonin wadanda suka rasa mastugunensu a wurare daban-daban a cikin jihar.
A shekarar 2019, Farfesa Babagana Zulum ya zama gwamnan jihar a karkashin inuwar jam’iyyar APC, jam’iyyar da ta karbi iko a shekarar 2015 da alkawarin cewa za ta maido zaman lafiya da daidaito a duk yankunan Najeriya. Wanda a halin yanzu kuma ya ke neman yin tazarce a zaben shekarar ta 2023.
Kwanan nan wani bidiyo ya bulla a shafin tiwita yana zargin gwamnan da zuwa sansanonin wadanda su ka rasa matsugunnensu ya na sayen katunan zabensu. Bidiyon ya gwado hoton wani mai sanye da riga kaftan da hulan da ke dauke da rubutun ZULUM 2023 tare da wani mai sanye da kayan jami’an tsaro. Mutanen biyu suna raba wadansu abin da ke kama da takardun nairori ga wadansu mutanen da su ke zaune.
Wani mai amfani da shafin da sunar Evars Hair (@EOguguah) ne ya wallafa bidiyon da zargin cewa an baiwa jama’an da ke cikin bidiyon kudi ne dan su bayar da katunan zabensu gabanin zabukan na 2023.
“Domin dukkansu masu magudi ne!!! Zulum (gwamnan jihar Borno) a sansanin wadanda su ka rasa matsugunnensu dan anshe mu su katin zabe,” ya rubuta.
Dr Ope Banwo, sanannen dan wasa a Najeriya wanda aka fi sani da Ali Baba ya nuna amincewarsa da zargin inda shi ma ya sake wallafa labarin yana bayyana takaicinsa da kuma kira ga shugaba Muhammadu Buhari da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta INEC da su dauki matakan da su ka dace su shawo kan wannan lamarin. Wannan labarin da ya wallaga ya janyo martani daga mutane fiye da 300,000 yayin da alkaluma su ka nuna cewa mutane fiye da 60,000 sun kalli bidiyon dun kuma yi tsokaci a kai.
“Da gaske? Wani ya fada mun cewa ba katin zabe ne ake saidawa Nera 500 ba a yankin arewa haka. Da gadara? A bainar jama’a? Ina Buhari? Ali Baba ya rubuta a kusa da bidiyon bayan ya wallafa.
To sai dai ba wannan ne karon farko da bidiyon ke daukar hankali haka ba. Daga farkon watan Disembar 2022 an wallafa bidiyon a shafin Nairaland, wani dandalin musayar bayanan da ke da mutane fiye da milliyan hudu wadanda ke amfani da shafin kowace rana.
A watan Yulin 2022 ma an wallafa shi a shafin tiwita, inda a nan ma ya sami martanoni iri-iri daga masu amfani da shafukan sada zumuntar.
Sayen katin zabe na daya daga cikin matsalolin da ke kalubalantar zabe a Najeriya. A zabukan da suka wice, an yi zarge-zargen cewa jam’iyyu da dama sun sayi katunan zabe. Dan haka, ana iya cewa zage-zarge irin wannan na yawan bulla kuma ma suna tasiri ne domin al’ummar Najeriya ba ta yarda datsarin gudanar da zabe a kasar ba, kuma idan har ba a shawo kan matsalar ba za ta durkusar da ingancin da ake sa ran gani a zaben 2023.
Tantancewa
Domin tantance gaskiyar wannan zargi, DUBAWA ta fara da gano sadda bidiyon ya fara bulla a duniyar gizo. Ta yin amfani da manhajar InVid mai tantance sahihanci bidiyo ta gano cewa bidiyon ya fara bulla ne a manhajar TikTok a shafin da ke amfani da sunar @honhabu. An wallafa bidiyon a watan Yulin 2022 ba tare da wani tsokaci ko take ba.
Shafin na TikTok yana da dauke da hotuna da bidiyoyin wannan mutumin wanda aka gani yana raba kudi. Daga nan ne DUBAWA ta gano cewa sunan mutumin Habu Daja wanda dan majalisa ne a Majalisar dokokin jihar Borno wanda ke wakiltar mazabar Damboa.
Da DUBAWA ta tuntubi Habu Daja ta wayar tarho dangane da bidiyon, mataimakin shi Mohammed Baba ya bayyana mana cewa an dauki bidiyon ne lokacin wata ziyara da gwamnan ya kai a daya daga cikin sansanonin wadanda suka rasa matsugunnen na su da ke Damboa, inda ya raba kudi da sauran kayayyakin da ke da mahimmanci ga mazauna wurin da ma wadanda ambaliya ta yi barna,
“Wannan ba kwanan nan ya faru ba, an dauki bidiyon nan lokacin ziyarar da gwamna ya kai Damboa ranar 25 ga watan Yulin 2022. Mai girm Hon. (DAJA) ya rabawa mazauna sansanin kudi da wadansu abubuwan da su ke bukata.”
Dangane da maganar da aka yi kan katin zabe, Mr Baba ya ce wadannan takardun da ke hannunsu da ake zargi katunan zabe ne baucas (voucher) ne aka ba su dan su sami sauki wajen rabon abubuwan da ak ba su
“Ba katunan zabe ba ne. Baucas ne na musamman da ake baiwa masu zama a sansanonin domin kada a rika ba mutun daya sau biyu wanda a baya aka rika fama da shi kafin aka kaddamar da tsarin amfani da da takardun baucas din,” ya ce.
Zulum ya kai ziyara Damboa ranar 25 ga watan Yulin 2022?
A shafin Gwamnan Jihar Borno na Facebook, an wallafa wata sanarwar manema labarai ranar 25 ga watan Yulin 2022 da cikakken bayani dangane da ziyarar da gwamnan ya kai karamar hukumar Damboa dan ganawa da mazauna IDP camps da wadanda ambaliya ta yi wa ta’adi.
Rahoton mai taken: Zulum a Damboa, ya raba Nera miliyan 172, da abinci ga mazauna 30,436 …. Ya kwatanta yadda gwamnan da tawagarsa suka raba kudade da kayayyakin more rayuwa ga mazauna Damboa kamar dai yadda Baba ya bayyana.
Hotunan da aka sanya tare da rahoton na Facebook sun zo daidai da wadanda ke cikin bidiyon. Wani mutumin da ke tsaye a bayan gwamnan a daya daga cikin hotunan da aka wallafa tare da sanarwar manema labaran da aka sanya a shafin ya kasance a cikin bidiyon.
DUBAWA ta sake gano wani bidiyon a Facebook dangane da ziyarar ta Zulum a Damboa. Shi ma wannan bidiyon ya nuno mutumin nan mai sanye kaftan yana raba kudi. Sa’annan a wani bidiyon kuma an ga wata mata tana rike da kudi da bauca.
Job Kaltho wani jami’in agaji da ke aiki da Mery Corps ya ce katunan bauca din suna dauke da wadansu alamu na musamman dan tsaro wadanda mazauna sansanonin wadanda suka canci samun kudi da kayan abinci ne kadai suka sani domin hana wadanda za su zo su karbi abin da ba na su ba ta barauniyar hanya.
Mr Kaltho ya ce: “An kaddamar da amfani da katunan ne shekaru ukun da suka gabata domin tantance wadanda sukan saci jiki su zo su karbi abincin da ba nasu ba su hana wadanda ke bukata samu.
“Dan haka katunan hanya ce ta hana barayi samun abinci da kuma hana wadanda su kan karba sau biyu su je su saida a waje a yayin da wasu ‘yan uwansu a wurin ba su samu ba.”
Ya yi dariya da ake cewa an yi zargin katunan baucas din katunan zabe ne inda ya ce yawancin masu aikin agaji a Borno na sane da batun katin. “Wannan katin ya kawo sauki wajen raba abinci da ma sauran abubuwa ga mutane masu yawan gaske,” ya bayyana.
A daya daga cikin hotunan da aka sanya tare da sanarwar manema labaran na shafi facebook, an nuno mata da yawa suna rike da katin a hannunsu.
Bugu da kari, kafofin yada labarai da dama kuma masu nagarta sun dauki labarin, kafar TVC misali ta yi labarin ziyarar ta Zulum a Damboa ranar 25 ga watan Yulin kuma ta yi amfani da hotunan da aka wallafa a shafin gwamnan.
A karshe
Babu rahoto ko kuma ma kafar yada labaran da ta yi labari dangane da abin da ake zargi ya faru a cikin bidiyon. Wannan zargin ba gaskiya ba ne kuma abin da aka gani kudi da abinci da sauran kayayyakin more rayuwa ne kawai ake rabawa yayin da gwamnan Bornon ke ziyara a karamar hukumar Damboa.