African LanguagesHausa

Idan har ta aka zabe ta gwamna, Aisha Binani ba za ta kasance macen farko a mukamin ba domin an taba gwamna mace

Zargi: Bashir Ahmad, mataimakin shugaba Muhammadu Buhari na musamman kan kafofin sadarwa na zamani  na zargin wai sanata Aisha Binani za ta kasance macen farko a mukamin gwamna a Najeriya idan har ta yi nasara a zaben gwamna a jihar Adamawa.

Idan har ta aka zabe ta gwamna, Aisha Binani ba za ta kasance macen farko a mukamin ba domin an taba gwamna mace

Ms Virginia Etiaba ce macen da ta fara kasancewa gwamna a Najeriya a jihar Anambra lokacin da kotu ta tsige Peter Obi daga mukamin gwamna na tsawon watanni uku a shekarar 2006. Tun da ita ce mataimakiyar gwamna, ta rike mukamin na wannan lokacin kafin dawowar Obi.

Cikakken bayani

Yayin da ‘yan Najeriya ke shirin zaben shugaban kasar da za’a yi a wata mai zuwa, mutanen jihar Adamawa ma na shirin tinkarar zaben gwamna a jihar.

Daya daga cikin ‘yan takaran da ke kan gaba ita ce Aisha Binanin wadda ta ajiye mukaminta na jagorar yakin neman zaben jam’iyyar APC a jihar a ‘yan watannin da suka gabata.

Kwanan nan mataimakin shugaban kasa na musamman kan kafofin sadarwa na zamani Bashir Ahmad (@BashirAhmaad) ya rubuta a shafinsa na tiwita cewa idan har Binani ta yi nasara a zaben gwamnan da za’a yi a jihar Adamawa za ta kasance macen farko a wannan mukamin a duk fadin Najeriya.

Da ya ke tsokaci dangane da batun Chima Obi (@Chimadodo) ya yabawa APC da suka gabatar da ‘yar takara mace. “Ina yabawa APC da su ka tsayar da ‘yar takara mace a karon farko a tarihinsu, ina son haka. Amma dai ba za ta yi nasara ba.”

Joseph (@Sabjin_bran) kuwa, ya kalubalanci zargin ya ce “Obi ya gabatar da wata a baya -Dame Virgy Etiaba Nuwamba 2006. Daina wannan batun gwamna mace na farko a Najeriya.

Ganin yadda wadannan martanoni da ke karo da juna ne ya sa DUBAWA ta ce za ta tantance gaskiyar wannan labari.

Tantancewa

DUBAWA ta fara da bincika google dan ganin ko akwai wani rahoto da ya yi bayani kan haka. Daga nan ne mu ka ga wani rahoton da gidan rediyon Voice of Najeriya ya wallafa inda gwamnan jihar Anambra na yanzu, Farfesa Charles Soludo ke taya Ms Virginia Etiaba murnar cika shekaru 80 da haihuwa.

“Gwamna Soludo na taya gwamna mace na farko murnar cika shekaru 80 da haihuwa,” a cewar taken.

Haka nan kuma a 2019, Shugaba Muhammadu Buhari shi ma ya taya Etiaba murnar cika shekaru 77 da haihuwa, inda shugaban ya kwatanta ta a matsayin “mai koyarwa ta gari wadda ta sauya tarihin Najeriya bayan da ta kasance mace ta farko a mukamin gwamna a Najeriyaa tsakanin watan Nuwamban 2006 zuwa Fabrairun 2007.”

A shekarar 2006, Sahara Reporters ta rawaito cewa an tsige gwamnan jihar Anambra na wancan lokacin wato Peter Obi bayan da aka same shi da wasu laifufuka.

Lokacin da aka tsige shi, mataimakiyarsa Ms Virginia Etiaba ta kasance mace na farko a mukamin gwamna a Najeriya. Jaridun Mail da Guardian sun rawaito cewa babban alkalin jihar ya rantsar da ita a mukamin duk da cewa ta ki karba tana jaddada alkawarin amincinta ga Peter Obi.

Bayan watanni uku, aka maido Peter Obi a matsayinsa na gwamnan hihar Anambra kamar yadda kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayyana. Dawowansa ya mayar da Etaiba ga mukaminta na mataimakiya bayan da ta sahfe watanni uku a mukamin gwamnan.

A Karshe 

Sakamakon tsige Peter Obi da aka yi a matsayin gwamnan jihar Anambra, mataimakiyarsa ta kasance macen farko wadda ta taba kasancewa a mukamin gwamna a Najeriya. Duk da cewa ba a zabe ta kai tsaye wajen jefa kuri’a ba, ta kasance gwamna a Anambra lokacin da aka tsige wanda aka zaba, dan haka wannan zargin ba gaskiya ba ne.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button