Zargi: Wani mai amfani da shafin Facebook na zargin wai gwamnatin kasar Ghana da gabatar da wasu sabbin rigunan makarantar da ya kamata malaman makaranta su rika sanyawa.

Wannan zargin ba gaskiya ba ne. Jami’ar hulda da jama’a ta ma’aikatar ilimin kasar da mai magana da yawun ma’aikatar duk sun fito sun karyata wannan zargin
Cikakken labari
Bisa dalilai na tabbatar da daidaito tsakanin yaran da suka fito gidajen da ke da galihu da na marasa galihu, da tabbatar da kariya da ma yin la’akari da cewa ba’a bar kowa a baya ba, ya sa aka fitar da tsarin rigar makaranta a tsakanin ‘yan makarantar firamare da sakandare a Afirka. Wadannan rigunan makaranta ne ake so duk dalibai su sanya a makaranta. Yawancin makarantu suna da salon dinki daban-daban kuma kowane da irin launin da ya ke zaba “domin banbanta tsakanin daliban makarantun da ake da su”
Ba kamar dalubai ba, malaman makaranta a Afirka ba su sanya wata riga ta musamman dan makarantan illa dai kawai su sanya rigunan da ya nuna cewa za su je wani aiki mai mahimmanci.
Shi ya sa ya kasance abin mamaki da wannan zargin ke cewa wai gwamnatin Ghana ta fitar da rigar makaranta wa malamai. Wani mai amfani da shafin Facebook ne ya wallafa wannan labarin. Mai shafin ya wallafa labarin ne tare da hoton wasu mata wadanda ke sanye da riga mai ruwan hoda tare da buje da wando mai ruwan kasa. Nan da nan hotunan suka fara yaduwa a shafukan soshiyal mediya musamman tiwita. A saman aljihun da ke kirjin rigar, an rubuta “Ghana Education Service” da turanci, wato Sashen Ilimin Ghana.
An yada labarin sosai kuma ya janyo cece-kuce da mahawarori inda wasu suka nuna bacin rai a kan cewa hakan bai dace ba a yayin da wasu kuma suka yi maraba da abin da su ka kira ci-gaba.
Da ta ke mayar da martaninta wata mai amfani da Facebook Alice Chobola ta yi Allah-wadai da matakin gwamnatin inda ta ce bai dace a ce malamai suna sanya rigar makaranta ba.
Ta rubuta: “Ba daidai ba ne abin da gwamnatin Ghana ta yi. Nas na sanya rigar zuwa aiki, amma marasa lafiya suna sanya na su dan haka dalubai su sa riga su ma malamai su sanya wanda su ka ga dama, Epela.”
Sai dai ba kamar Alice ba, Mavis Mulundano ta ce gabatar da rigunan makaranta ga malamai zai rage irin ayyukan da malaman kan yi cikin sirri lokacin sa ake makarantar.
Ta rubuta: Irin wannan matakin zai yi kyau a Zambia dan ya rage yawan malaman da ke zuwa shan giya a lokacin da ya kamata suna koyarwa a makaranta domin za su yi fargabar za’a kama su idan har aka gan su da rigar makarantar.”
Domin yawan yadda aka labarin ne ya sa DUBAWA ta dauki nauyin fayyace gaskiyar lamarin.
Tantancewa
DUBAWA ta fara da binciken mahimman kalmomi inda ta ga labarin a taskokin blog har guda uku, sai dai ko daya ba ta ga labarin a cikin kafofin yada labarai na gargajiya ba wadanda aka fi daukar labaran su da sahihanci.
Daga nan DUBAWA ta tuntubi Cassandra Twum, jami’ar hulda da jama’a na sashen ilimin Ghana wadda a nan take ta karyata zargin
“Oh ai wannan tsohon labari ne na karya! Ku yi watsi da shi. Ba gaskiya ba ne:”
Baya ga haka, DUBAWA ta tuntubi Kwasi Kwarteng, Mai magana da yawun ma’aikatar ilimin Ghana ta WhatsApp inda shi ma ya karyata labarin da cewa:
“Sashen kula da ilimi na Ghana bai gabatar da wata rigar makarantar malamai ba”
A Karshe
Jami’ar kula da hulda da jama’a da mai magana da yawun ma’aikatar ilimin Ghana duk sun karyata wannan labarin. Dan haka labarin cewa gwamnatin Ghana ta fitar da rigar makaranta wa malamanta karya ne.





