African LanguagesHausa

Haramcin tafiya da jakakuna samfurin Ghana-must-go, daga kamfanin jirgin Ethiopian Airline ne ba FAAN ba

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: FAAN ta haramta amfani da jakankunan Ghana-must-go.

Haramcin tafiya da jakakuna samfurin Ghana-must-go, daga kamfanin jirgin Ethiopian Airline ne ba FAAN ba

Sakamakon bincike: YAUDARA CE. Hukumar FAAN ta nisanta kanta da wannan labari inda ta ce ba ita ta haramta ba face kamfanin jiragen Ethiopian Airlines. 

Cikakken sakon

A ranar Juma’a daya ga watan Disamba, 2023 an baza labarin cewa Hukumar da ke lura da tashoshin jiragen sama a Najeriya  (FAAN) ta haramta amfani da jakankunan nan masu kama da buhu samfurin (Ghana-must-go bags,) labarin da aka wallafa a kafofin yada labaran  Arise News, Leadership, Daily Post Nigeria, the Guardian Nigeria, baya ga sauran kafofi.

Wadannan kafafan yada labarai sun alakanta asalin labarin nasu daga wata takardar sanarwa mai taken “Re: Prohibition of Usage Of Ghana Must Go” ma’ana sake hana amfani da jakankunan na Ghana Must Go. Sanarwar da manajan Airport ya rattabawa hannu.

DUBAWA ya shiga bincike kan wannan labari don kaucewa haifar da rudani.

Tantancewa

Mun gudanar da cikakken bincike ta hanyar (Google Search) ta hanayr amfani da wasu muhimaman kalmomi da dabarun bincike kana muka ziyarci shafin (FAAN’s website) don neman rahoton amma bamu samu komai ba da ke kama da wannan labari. A wannan labarin aka makala wannan sanarwa daga kamfanin na Ethiopian Airlines.

Daga nan mun ziyarci shafin X na FAAN (@FAAN_Official) inda muka ci karo da wani sako da ke nesanta hukumar da labarin inda ta yi bayani (clarifying)  cewa haramcin ya fito ne daga kamfanin jiragen saman na Ethiopian Airlines. 

Haramcin tafiya da jakakuna samfurin Ghana-must-go, daga kamfanin jirgin Ethiopian Airline ne ba FAAN ba

Domin gano asalin inda sanarwar ta fito mun ziyarci shafin intanet na kamfanin jirgin da shafinsa na X (@flyethopian), amma bamu ga sanarwar ba. Sannan muka ci gaba da bincike ta hanyar amfani da dabarun gano asalin hoto na kofin hoton sanarwar da FAAN  ta yi, amma wannan ma sai ya kaimu ga wasu bayanan da ba su da alaka da abin da muke nema.

Da muka sake yin wani binciken ta hanyar amfani da wasu muhimman kalmomin kan haramcin da kamfanin na  Ethiopian Airlines yayi, mun ga yadda wasu kafafan yada labaran kamar Punch Newspaper da The Cable, suka yi labarin inda suka ce sun samo shi daga kamfanin Ethiopian Airlines a Najeriya.

Rahotannin guda biyu duk sun nunar da cewa an samu haramcin a takardar da ke dauke da sa hannun Henok Gizachew, manaja na filin tashi da saukar jiragen saman. Rahoton ya nunar da cewa an tura wasikar ne ga manajan yanki na FAAN. Muma mun karbi kofi na wasikar da aka rubuta ranar 24 ga watan Nuwamba, 2023 wacce aka tura wa hukumar ta FAAN wacce ta ba da tabbacin asalin inda gidajen jaridun na Punch da Cable  suka samo labarinsu. 

“Da Allah a kiyaye cewa daga ranar 26 ga watan Nuwamba, 2023 an haramta tafiye-tafiye da jakankuna samfurin Ghana Must Go a jiragenmu.” Wani bangare kenan na abin da wasikar ta kunsa. Mun kuma lura cewa jaridun Leadership da Daily Post, wadanda suka ce FAAN ce ta haramta sun sake rubuta labarin daga baya inda suka ce kamfanin jiragen na Ethiopian Airlines ne yayi haramcin. Watakila bayan da suka ga sanarwar FAAN da ta nesanta kanta da daukar matakin.

Kammalawa

Labarin rahoton da ke cewa  FAAN ta haramta tafiye-tafiye da jakankuna samfurin Ghana-must-go bags yaudare ne/ba daidai bane. FAAN ta nesanta kanta da wannan labari, inda ta bayyana cewa kamfanin jiragen sama na Ethiopian Airlines ne ya fitar da haramcin.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button
Translate »