Zargi: wani labarin da ake zargi BBC ce ta wallafa a shafin Facebook, na neman tallafin kudi wa wani Joshua Tosin Ajayi wanda ya yi rauni sosai sakamakon wani hatsarin da ya yi a wata mahakar ma’adinai.
Sakamakon Bincike: Babu ciakken gaskiya. Bincikenmu ya nuna cewa wannan labarin karya ne kawai kuma an yi shi ne da niyyar yaudaran ‘yan Najeriya ta yin amfani da wani mutumin da suke zargi ya yi rauni a kafa da kashin baya, alhali kuma babu wani mutumi haka
Cikakken bayani
Shafin samun taimakon kudi na GoFundMe da wadansu shafukan soshiyal mediya na daga cikin wadansu hanyoyin da ake amfani da su wajen samun tallafin kudi dan taimakawa marasa lafiya wadanda ba su da halin biyan kudin asibiti da na magunguna kuma an san ‘yan Najeriya da kyauta wadansu lokutan musamman idan abun da ya faru na da sosa rai.
Kwanan nan wani labarin da aka wallafa a Facebook daga wani shafin da ke kiran kan sa BBC News Nigeria ya ja hankalin DUBAWA saboda yadda ya ce yana neman tallafi wa wani mutumi mara lafiya.
Wannan labarin ya bulla ranar 4 ga watan Fabrairun 2023, da hotuna uku na wani mai suna Joshua Tosin Ajayi wanda ake zargi ya samu rauni a kashin baya da kafa bayan da ya fadi cikin wata mahakar ma’adinai yaain da yake aiki a shekarar 2021.
Yadda aka tsara labarin ya shiryu sosai kuma zai iya jan ra’ayin mutane su ba da ko da nawa ake nema.
Shafin da ake zargi na BBC ne a yanzu haka na da mabiya 73, yayin da labarin kuma ya sami tsokace-tsokace fiye da 5,000 mutane sama da 9,200 sun yi ma’amala da labarin kuma an raba shi har sau 480 a shafin na Facebook.
A baya, mutane sun yi amfani da irin wadannan labaran sun yaudari jama’an da ba su ji ba su gani ba, dan haka ne DUBAWa ta kuduri aniyar tantance gaskiyar batun dan ta wayar da kan al’umma.
Tattancewa
Mun kula cewa shafin ba’a tantance shi da alamar da ke tabbatar da halaccin shafi ba, sa’anan yawan wadanda ke bin shafin ya dauki hankalinmu saboda yawan idan aka kwatanta da kimar da BBC ke da shi.
Dan haka DUBAWA ta duba shafukan da BBC ke amfani da su a hukumance a Facebook inda ta gano cewa shafin BBC na tashoshin Afirka na da suna BBC News Africa ba BBC News Nigeria ba. Shafin na BBC News Africa kuma na da mabiya fiye da miliyan biyar sa’annan yana dauke da alamar tantancewa na kamfanin Meta.
DUBAWA ta tura da sako kai tsaye zuwa ga shafin BBC News Africa dan tantance gaskiyar shafin da ke bayanin neman tallafin kudi, sai dai ba mu sami amsa kai tsaye ba.
Daga nan sai muka yi bincike muka yi amfani da manhajar da ke gane mafarin hotuna a google wato google reverse image search dan bin diddigin hotunan mutumin amma kuma bamu sami komai dangane da hotunan ba. Da muka sake yin wani binciken a manhajar TinEye ita ma na hotunan, ba mu ga komai ba.
Sai dai da muka yi amfani da manhajar Veracity, ya nuna mana cewa akwai wadansu wuraren da aka gyara hoton da photoshop, wuraren wuya da fuska amma sai an kalla da kyau za’a gane.
Da muka cigaba da bincike sai ya kai mu shafin jaridar Daily News a Facebook wanda aka kirkiro ranar 8 ga watan Fabrairun 2023. Ba wanda ke bin shafin kuma babu wani abu illa wannan labarin wanda babu wanda ma ya yi ma’amala da shi. Shafin yana dauke da wani adireshi kamar haka: Progresstmt5@gmail.com.
Haka nan kuma da muka duba google dan gano shafin Daily News Nigeria sai muka ga cewa babu wani shafi da wannan sunan kuma ba shi da ma wani labari a shafin kafin wannan batun na neman tallafi.
Zamba daya, labarai daban-daban
Ganin yadda masu zamban suka dage suna so su yaudari wadanda ba su hi ba su gani ba, sun sake wallafa wani labarin wanda aka sa a wani shafin bogi mai suna NTA News Nigeria wanda shi kuma aka kirkiro 12 ga watan Fabrairun 2023, amma wannan karon sun sanya bidiyon wata mata ce mai suna Madam Comfort wadda ake zargin ta haifi tagwaye kuma tana neman N750,000 dan a sallame ta daga asibiti. Abun mamaki sai muka ga cewa labarin na dauke da lambar asusun bankin Joshua Tosin Ajayi 0728203559, GT Bank.
Mutane sun kalli bidiyon sau 25,000 a Facebook, an raba labarin sau dubu 80 kuma masu amfani da Facebook 109,000 suka yi ma’amala da labarin.
Da muka sa hotunan a google ba mu sami wani bayani mai gamsarwa dangane da bidiyon ba. Sai DUBAWA ta yi binciken da mahimman kalmomi a Google Pinpoint da YouTube, nan ma ba mu sami wani bayanin kirki ba.
Binciken mahimman kalmomi a shafukan soshiyal mediya ya nuna mana wani bidiyo na wata mai suna Comfort Apeh wanda aka rika yadawa amma a wannan karin ba’a fayyace mai shafin ba kuma yana da mabiya 23 ne kacal.
Binciken DUBAWA ya sake kai mu wani shafin mau suna TVC News Nigerian, wanda ke da mabiya 153, suma sun sanya wannan labarin suna neman tallafi. Shafin TVC na ainihi a Facebook shi ne @tvcnewsng wanda kamfanin meta ya tantance kuma yana da mabiya 300,000.
Nazarin da muka yi kan wadannan labaran ya nuna mana cewa da walikin goro a miya a kowanne daga cikinsu. Na farko dai duka shafukan ba su da nagartattun adiresoshi da lambobin waya. Haka nan kuma babu bayani dangane da masu shafon a wurin da aka yi tanadin bayyanawa wato a shafin “About”
Duka shafukan na dauke da adiresoshi daban da sunaye daban-daban idan aka kwatanta su. Bisa tanadin manufofin kamfanin Meta, tilas ne shafi ya sami suna a cikin adireshin yadda za’a iya kwafa, amma lamarin ba haka ba ne a wadannan shafukan.
Bacin hakan an yi amfani da irin adiresoshin da ba za’a iya tantancewa ba ne wajen kirkiro shafukan wadanda kuma aka kirkiro su kusan lokaci guda da labari daya kadai a shafukan.
A Karshe
Binciken DUBAWA ya nuna cewa labarin da ya dauki hankali a Facebook wanda ke nuna wani mai suna Joshua Tosin Ajayi da zargin cewa ya yi rauni a kashin baya da kafa ba gaskiya ba ne. Labarin tare da wani bidiyo mai tsawon dakiku 30 na wata ita kuma mai suna madam Comfort tana neman tallafi shi ma karya ne kuma bincikenmu ya nuna mana cewa duka labaran karya ne kuma an yi su ne da nufin yaudaran mutanen da ba su ji ba su gani ba.