African LanguagesHausa

Da gaske ne, fiye da kashi 30 cikin 100 na mukaman gwamnatin Sanwo – Olu na hannun mata 

Zargi: Gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu, ya ce wai matan da ke aiki da shi sun fi kashi 30 cikin 100. Ya bayyana hakan da ya ke lissafa yawan alkawuran da gwamnatinsa ta cika lokacin da take neman mulkin jihar a 2019.

<strong>Da gaske ne, fiye da kashi 30 cikin 100 na mukaman gwamnatin Sanwo - Olu na hannun mata </strong>

Sakamakon Bincike: Gaskiya. Binciken mu ya nuna mana cewa wakilcin mata a majalisar ministocin jihar Legas ya wuce kashi 30 cikin 100.

Cikakken bayani

Gabannin zabukan gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi, ‘yan takara sun cigaba da daukar matakan da za su taimaka mu su wajen samun magoya baya.

Ranar Laraba 8 ga watan Maris 2023, gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu wanda ke neman yin tazarce a kujerar gwamnan jihar ya rubuta gajejjerun sakonni dama a shafin Twitter dan tunawa da Ranar Mata ta Duniya 

A cikin  jerin sakonnin na Twitter , ya ce gwamnatinsa ta cika alkawarinta na tabbatar da cewa mata sun wuce kashi  30 cikin 100 a mukaman gwamnati.

A cewar gwamnan, manufofin da ya sa da nufin kara yawan mata a manyan mukaman gwamnatin ne ya sa mata suka sami manyan mukamai a Legas.

Yayin da mutane da dama suka rika yabawa gwamnan, wani mai amfani da shafin Twitter Doctor Spec (@doctorspec_ds), ya ce bai yarda ba. A tsokacin da ya yi, Doctor Spec ya ce, “Ba wanda zai yarda da maganganun ka dan ka cika karya.” 

DUBAWA ta yanke shawarar gano gaskiyar batun da Mr Sanwo-Olu ya yi dan ta fayyace komai. 

Tantancewa

A shafin jihar Legas, majalisar zartarwar na da mambobi 42, a ciki har da gwamna da mataimakin sa. idan aka cire gwamna da mataimaki, akwai mutane 40, wadanda 12n su mata ne 28 kuma maza wanda ke zaman kashi 30 da kashi 70 cikin 100 bi da bi.

Haka nan kuma wani rahoton Premium Times ya nuna masu bayar da shawara na musaman guda bakwai wadanda gwamnan ya nada a  2022.  Ko da shi ke a wannan nade-naden maza sun fi yawa, inda mata biyu ne kawai suka kasance cikin su. 

Wadannan matan sun hada da Aderemi Adebowale, Mai bayar da shawara na musamman kan hulda da jama’a sai kuma Toke Benson-Awoyinka, Mai bayar da shawara na musamman kan samar da gidaje.

Cikakken jaddawalin sunayen kwamishanoni da masu bai wa gwamna shawara na musaman wadanda gwamnatoin jihar Legas ta nada daga 2019-2023 shi ma ya nuna wani abu makamanicin haka. 

Takwas daga cikin kwamishanoni 22 mata ne, yayin da sauran suka kasasnce maza. Wannan ya nuna cewa kusan kashi 36 cikin 100 mata ne a yayin da kashi 64 cikin 100 suka kasance maza.

Kwamishanonin mata guda takwas sun hada da: Folashade Adefisayo (ilimi), Cecilia Bolaji Dada (Harkokin mata da kawar talauci), Ajibola Ponnle (Manyan kamfanoni, horaswa da fanshow), Aramide Adeyoye (Ayyuka da Ababen More Rayuwa), Uzamat Akinbile-Yusuf (Harkokin cikin gida), Yetunde Arobieke (Harkokin kananan hukumomi da al’ummomi), Lola Akande (Ciniki da Masana’antu) and Olufunke Adebolu (Yawon Bude Ido, Fasahohin zane-zane da Al’adu). 

Daga cikin masu bayar da shawarwari kuma na musamman tara daga cikinsu ne maza a yayin da sauran hudun kuma suka kasance mata abun da ke zaman kashi 31 cikin 100.

Masu bayar da shawarar hudu sun hada da; Ruth Bisola Olusanya (Noma) Aderemi Adebowale (hulda da jama’a ‘yan jiha) Toke Benson-Awoyinka (Gidaje/ Gine-gine) Solape Hammond ( Burakan tabbatar da cigaba mai dorewa) 

A karshe

Bincikenmmu ya nuna mana cewa sama da kashi 30 cikin 100 na kwamishanonin jihar Legas mata ne. Dan haka zargin gwamnan gaskiya ne.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button