Kusan kowa na farin cikin zagayowar ranar da aka haifi shi/ta. Yawanci su kan karrama wannan rana da bai wa wanda ke bukin kara yawan shekarun kyaututtuka.
Kwanan nan DUBAWA ta lura da wani sabon salon da ake amfani da shi wajen aikar da sakonnin taya murnar ranar haihuwar inda wasu ke tambayar lambobin wayar madanda ke bukin zagayowar ranar haihuwar ta su a sunan wai za su tura musu wata kyauta. Ko kyautar katin waya ce ko ta data wa’allahu alam, sai dai wannan zai ja hankalin mutun musamman idan sakon ya fito daga abokanai ne.
“Shigo ba zurfin” da ake yi da zagayowar ranar haihuwar masu amfani da Facebook
Lokacin da ranar haihuwata ta zagayo a bara wato 2021, na sami sakonnin taya murna da yawa wadanda ke tambaya ta in tura lambar waya domin samun wata kyauta.
Ban dauki sakonnin da mahimmanci ba dan haka ban tanka su, sai dai da sami sakonni makamantansu a bana, sai ya daukar mun hankali na fara tunanin abin da ake nufi da hakan
“Happy Birthday. Ina mi ki fatan tsawon rai da rayuwa mai inganci. Turo mun lambar wayarki. Ina da kyautar da zan ba ki,” daya daga cikin sakonnin ya bayyana.
Wani shafin wanda ba ya cikin jerin sunayen abokanai na a shafin amma kuma ya taba tura mun sako dangane da wata dama ta zuba jari a watan Yunin 2021, shi ma ya tura mun irin sakon taya murnar.
Yayin da kamanceceniyar da ke tsakanin sakonnin ya sanya ni tunanin da walakin goro a miya, samun wata wasika daga wadda mu ke zuwa makaranta tare, wadda ke da lambar wayata wadda kuma mun ma yi hira da ita kwanaki kadan kafin zagayowar ranar haihuwar ta wa ya tabbatar mun cewa akwai wani abin da bai kamata ba da ke faruwa.
Dan me wanda na san yana da lambar wayata zai sake tambayata lambar waya? Wannan ne ya sa na tuntuntubi wannan abokin wanda ya tabbatar mun cewa masu yaudara sun shiga shafinsa tun watan Maris 2022, watanni biyu kafin watan da aka haife ni.
Yadda masu yaudarar ke aiki
Kamar ni, akwai ‘yan Najeriya da dama da suka shiga hannun ire-iren wadannan mazambatar. Offorka Jerry wani kwararre a fannin Bayanai, Sadarwa da Fasaha (ICT) kuma kwararre kan lafiyar kwakwalwa ya bayyana irin abin da ya fuskanta
Mr Offorka ya ce ya sami sako makamancin wannan daga daya daga cikin abokan shi wanda ya suka jima ba su ga juna ba.
Wannan abokin ya taya shi murnar zagayowar ranar hauhuwarsa ya kuma ce mi shi mataimakin shi zai tuntube shi nan ba da dadewa ba. Jim kadan bayan hakan, wani wadanda ake kayautata zaton mataimakin ne sai ya bugo masa waya ya tambaye lambar Asusun Bankin sa wanda ya tura masa ba tare da bata lokaci ba.
Bayan haka dai PAn ya sake kira ya ce ya tura masa lambobin sirri ko kuma pin din da aka turo masa, nana da nan Mr Offorka ya dago cewa akwai matsala domin irin lambobin sau daya ake bayarwa dan haka sai bai bayar ba.
“A matsayi na wanda ke aiki a fanin bayanai da fasaha na san abin da lamber OTP ke nufi, ke nan sun yi kokarin shiga asusun banki na ta barauniyar hanya amma sun gaza, saboda haka da na aika musu lambar OTPn da sun yi amfani da shi sun kwashe duk wata ajiyar da na ke da ita a banki
Ba kamar ni da Mr Offorka ba, wasu da yawa ba su yi sa’a ba domin sun rasa shafukansu na Facebook bayan da suka ba da lambobinsu da sauran bayanan da aka bukata.
“Haka nem ya faru da yaya na. Yanzu ba shi da shafi a Facebook,” a cewar Merit wata wadda abin ya dame ta sosai.
Dalilin da ya sa lambar waya ke da mahimmanci
Kwararru a faninin fasahohin bayanai sun bayyana dalilin da ya sa mayaudaran ke bukatar lmabar waya da yadda su ke amfani da shi.
Ore Afolayam wani dan kasuwar fasahohi ya ce mayaudara suna da kwarewa sosai wajen shawo kan wadanda ba su ji ba su gani ba su bayar da bayanansu na sirri.
Da lambar wayar mutun, ya ce suna iya samun duk wani bayani dangane da shafin Facebook din ka wanda za su iya amfani da shi su shiga shafin ba tare da izini ba.
“Illimin zamantakewarsu na da kyau sosai. Wanda ya saba irin wannan yaudarar zai bukaci lambar waya domin zai iya ba shi alamun da za su nuna mi shi bayanan da mutun ya yi amfani da shi wajen yin rajista a shafin, daga nan kuma idan su ka cigaba da tattaunawa za su gano dabarar da za su iya amfani da shi wajen gano kwanan watan haihuwa.
“Dukkanmu mun san yadda mutane da yawa ke amfani da kwanan watan da aka haife su a matsayin kalmar sirrin shiga shafukansu,” ya bayyana
Ana kuma iya amfani da wannan wajen shiga asusun banki. Mr Afolayan ya yi ja hankali game da rashin ingancin manufofin tantancen kwastamomin a bangaren kamfanonin fasaha wanda ake kira Know Your Customer Policies (KYC) a turance, domin a cewarsa hakan ne ya sa masu yaudara ke iya bude shafukan jama’a tare da lambar waya kadai.
KYC kuduri ne da ya tilastawa bankuna da sauran cibiyoyin kudi sanin kwastamominsu ciki da waje (Wato cikakken bayani kan masu amfani da kamfanoninsu)
Da zarar mayaudaran suka bude shafinku ba tare da izini ba a kan tura mu ku abin da ake kira OTP kai tsaye, shi ya sa idan mutun bai sani ba sai su ce ya turo mu su sakon da ya samu a wayar tasa.
“Domin mutane da yawa ba su gama fahimtar soshiyal mediya ba, sai su bude asusun bankin da ba su ma san suna da shi ba,” ya ce.
Wannan ne abin da Nana Abu ta fuskanta, wadda ta sami kanta a tsaka mai wuya bayan da wani kamfanin bayar da bashi ya ce ta karbi bashi wajensu ba ta biya ba.
Ba da saninta ba, kamfanin bashin ya raba wannan labarin da duk wadanda ke da lambobi a wayarta da wannan zargin. Mutane da dama, har da abokai da wadanda ke aiki tare da ita suka sami wannan sakon abin da ya tayar ma ta da hankali matuka.
Daga baya sai da ta fayyace cewa mayaudara ne suka shiga shafinta kuma tana kokarin shawo kan lamarin.
Mr Offorka, kwarre kan fasahohin komfuta da yanar gizo-gizo amfani da bayanan mutane wajen sace kudadinsu abu mai sauki ne ga mayaudara sai dai ba sosai ne su ke iya boye na su bayanan ba. Shi ya sa su kan bukaci lambar waya dan mutun dan su yi kokarin batar da siffar ta yadda ba za a iya gano su ba.
“A matsayi na na wanda ya kware a IT na san yaudarar jama’a ba shi da wahala, kuma ana iya sace kudin mutun a banki cikin sauki, sai dai ba kowa ne zai iya yin hakan cikin sirri ba tare da an gano ko shi wane ne ba. Dan haka shi ya sa wata sa’a su kan yi kokarin yin amfani da lambar wayoyin ku dan a ga kamar ku ne ke.”
Ya kuma yi bayani kan yayin da ake yi na shiga shafukan soshiyal mediyar mutane.
“Idan sabon shafi ne ya tura maka sako za ka yi tunanin da walakin goro a miya, idan kuwa shafi ne da ka sani ko daya ba za ka yi tunanin akwai makirci a ciki ba.”
Yayin da mayaudara su ke cigaba da sauyawa suna sajewa da zamani, yana da mahimmanci a rika kulawa