Zargi: Wani mai amfani da shafin Facebook na zargin wai ma’abota wasar kwallon kafar da su ka je Katar dan kallon gasar cin kofin duniyar na shigar da giya ta haramtacciyar hanya inda su ke boye giyar Heineken a karkashin takardar lemun Pepsi
Labarin wai an yi kokarin shigar da giya zuwa Katar ne ba gaskiya ba ne. Ainihin labarin ya faru ne a Saudiyya shekaru bakwan da suka wuce sadda aka kama wani na kokarin shiga Saudiyya da giyar da aka sakaya a sunan Pepsi
Cikakken bayani
Giya dai ya dade yana kasancewa daya daga cikin abubuwan da ma’abotan kwallon kafa ke zuwa da shi kallon wasa dan ya kan kara wa wasannin armashi. Sai dai wasannin na Katar 2022 ba irin wadanda aka yi a baya ba ne. Wannan ne karon farko da wasar ke zuwa yankin Gabas Ta Tsakiya, kuma wannan ne karon farko da kasar da ke karbar bakunta wasannin ta ke shan kaye a wasarta ta farko.
Wuni biyu kafin a kaddamar da wasannin na bana mahukunta suka sanar wa ma’abotan cewa za’a haramta shan giya a duk filayen wasannin kasar guda takwas (8), sabanin alkawarin da su ka yi a baya.
Bayan wannan sanarwar, wasu hotunan giyar da ake kira Heineken suka bulla an sakaya su da takardun lemun Pepsi. Hotunan suna ta yawo a kafofin soshiyal mediya har ma wadansu kafofin yada labarai sun wallafa. Labarin da ya bi hotunan na kokarin cewa bacin haramta shan giyar da Katar ta yi, wadansu ma’abota wasannin sun yi dabara suna shigar da ita ta haramtacciyar hanya.
Wani mai suna Nnamdi Abana wanda ya kwatanta kansa a matsayin masanin kimiyar siyasa wanda ya kammala karauta a jami’ar Nnamdi Azikwe da ke Awka, jihar Anambran Najeriya ya wallafa hoton a shafin shi na Facebook ya na cewa ai ma’abotan wasan za su sake samun wata hanyar shigar da giyar tunda an gano wannan.
“To me su ka yi? Sun yi kokari sun yaudari tsarin ta hanyar sakaya gwangwanayen giyar da takardun lemun pepsi. Yanzu da aka kama su, mai yiwuwa za su sake neman wata hanyar,” ya bayyana.
Igetalk wata taskar blog inda ake wallafa labarai masu sosa rai sun yi labarin suna kokarin cewa masu yawon bude ido na iya shigar da gwangwaneyan da aka sakaya cikin filayen wasannin ba tare da an gane ba.
“… masu yawon bude idon da ke ziyara suna iya shigar da giyar da aka sakaya cikin filayen wasannin a Katar…”
“Suna kuma iya saida su a filayen wasannin ko da shi ke suna iya amfani da wata hanya ta sirri wajen yin haka. Yi tunanin wani wanda bai ji bai gani ba ya je sayen abin da ya ke tunani lemun kwalba ne irin su coke, sai dai daga ya kai baki sai ya gane cewa Heineken ne,” ya ce.
Ubuntu Jacob Navro, wani mai amfani da shafin Facebook ya ma bayar da ainihin yawan gwangwanayen giyar da ma’abota kwallon kafar su ka shigar zuwa Katar; a wata sanarwar da ya wallafa a shafinsa Jacob ya ce gwangwanaye fiye da dubu 800 ne aka kama.
“Yau da safe, jami’an kwastama a Katar sun kama gwangwanayen giya dubu 800 wadanda aka yi amfani da takardun pepsi aka rufe suna da tambari giyar dan kada a gane. Wane ne ba ya son jin dadi, wannan Heineken din na Katar ya wuce na Navrongo,” ya rubuta.
Gasar cin kofin kwallon kafa na duniyar ta shiga makonta na farko, bacin shan suka da yawan jayayyar da ya biyon samun damar karbar bakuncin gasar da Katar ta yi. Yayin da ma’abota gasar ke kokarin jin dadin wasannin, wajibi ne a tantance duk zarge-zargen da ke bullowa dan kada su yi tasiri a gasar.
Tantancewa
DUBAWA ta fara da gudanar da binciken kwa-kwaf kan hoton dan tantance ko hoton na gaskiya ne ko na bogi ne wanda wani ya zauna ya kaga. Sakamakon da aka samu daga Forensically, wata manhajar da ke tantance ko hoto na gaskiya ne ko kuma na bogi ne ya nuna cewa hoton na gaskiya ne kuma ba’a taba shi ba.
Bayan haka, DUBAWA ta yi amfani da google dan gano ainihin inda hoton ya fito. Sakamakon ya nuna cewa hoton gwangwanayen giyar Hineken da aka rufe da takardar Pepsi ya fara yawo a duniyar gizo tun shekarar 2015.
A shekarar 2015 jaridar The Telegraph ta wallafa wani labari mai taken:
“‘Yan Sumoga sun yi yunkurin shiga Saudiyya da gwangwaneyen giya 48,000 wadanda aka sakaya da takardar lemun kwalba na Pepsi.”
Labarin ne kuma aka sake wallafawa a jaridar Morocco World News, shi ma da taken
“Saudiyya ta cafke gwangwanayen giya 48,000 wadanda aka sakaya su da takardun lemun Pepsi”
Duka labaran biyu sun yi amfani da hoton da ake kokarin dangantawa da Katar.
Gaskiyar Labarin
A shekarar 2015 ‘yan sandan Saudiyya suka cafke giyar da aka yi kokarin wucewa da shi a matsayin lemun pepsi. Lamarin ya afku ne a Al Batha, iyakar da ke tsakanin Saidiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa inda jami’ai suka tsare wata mota tana dauke da haramtattun kayan, kamar da yadda kafofin yada labarai da dama a Saudiyya suka bayyana.
“Dan sumogan ya yi kokarin shigar da kayayyakin ta yin amfani da kyakyawar dabara, bayan da ya sanya takardun Pepsi ya lullube alamar giyar da ke kan ainihin gwagwanin, sai dai dabarar ba ta yiwu ba domin jami’an Saudiyya sun dago kuma sun hana shi cimma burin shi.” Wani bangare na labarin ya bayyana.
Tambadin da ke kan rigar jami’in da ake gani a cikin hoton tambarin ‘yan sandan Saudiyya ne ba Katar ba.
Bugu da kari babu wani labari makamancin wannan a kafofin yada labaran Katar tun da dai idan da ya faru, labari ne da ya kamata a ce majiyoyin cikin gida sun kawo. Abun ya faru ne shekaru bakwan da su ka gabata a Sadiyya, ba kwanan nan a Katar ba kamar yadda ake zargi.
A Karshe
Labarin wai an yi kokarin shigar da giya zuwa Katar ne ba gaskiya ba ne. Ainihin labarin ya faru ne a Saudiyya shekaru bakwan da suka wuce sadda aka kama wani na kokarin shiga Saudiyya da giyar da aka sakaya a sunan Pepsi.