African LanguagesHausa

Yadda ake gane “labaran bogi” a manhajojin TikTok da Twitter

Da wasa-da wasa manhajojin TikTok da Twitter sun zama kafofi masu tasiri sosai kan jama’a a dandalolin sada zumunta na soshiyal mediya. Wadanda kuma suke yada labarai cikin hanzarin ta hanyoyin da ba’a ma taba tuanin zasu yiwu ba a baya.

Misali, manhaja kamar TikTok, wadda kamfanin ByteDance ya kirkiro a shekarar 2016, yanzu na da mutane sama da biliyan biyu da rabi wadanda ke amfani da shi.

Bisa bayyanan shafin samun shawarwari kan hanyoyin zuba jari na Investopedia, ana danganta shaharar da ya yi da irin abubuwan da ke taimakawa masu amfani da shafin su kirkiro bidiyoin cikin sauki da abubuwan inganta hotuna na musamman, sauti da wakoki. Da masu amfani da ita a kasashe fiye da 150, yadda TikTok ke kai ga jama’a na da ban mamaki.

A daya hannun kuma Twitter kamfanin soshiyal mediya ne wanda Jack Dorsey ya kirkiro a shekarar 2006; ba kamar TikTok ba, Twitter na da mahimmanci wajen yadda ake yadawa da tattauna mahimman kanun labarai dangane da batutuwa kamar zabe. Alal misali, kwanaki kadan kafin zabukan Amurka na 2019, dandalin ya yi hasashen yadda da na kama shi saboda bayanai marasa gaskiya dangane da siyasa. Wannan ne ma ya sa aka dakatar da tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump daga amfani da shafin.

Bugu da kari, ba kamar TikTok ba Twitter na bai wa jama’a damar tattaunawa. Rikicin #EndSARS na 2020 a Najeriya ya dauki hankali ne saboda yadda Twitter ke sada jama’a ba tare da wani bango ko iyaka ba. Sai dai kuma ya gaza daukar tsauraran matakai kan wadanda suke karya dokokin shi. Misali mai kyau shi ne sadda aka dakatar da shafin shugaba Muhammadu Buhari’s, , abun da ya kai ga hana amfani da dandalin baki daya  a Najeriya.

Sai dai duk da irin matakan da ya dauka dan gane sakonnin da ke sabawa dokokin shafin, kamar TikTok shi ma har yanzu yana fama da matsalar labaran bogi. Yayin da zabukan 2023 ke karatowa, samun kwarewa wajen gane bayanan da ba dai-dai ba ne na da mahimmancin gaske.

Gano bayanan bogi a TikTok

  • Yi la’akari da bayanin da ke tare da alamar # (wato hashtag) sa’anan ku bi bidiyoin

Alamar Hashtag (#) a TikiTok ne ke taimaka wa bidiyoyi su yadu a kan dandalin. Masu kirkiro bidiyoyi da sauransu na yawan amfani da su da zarar sun wallafa abu saboda ya kai ga jama’a da yawa musamman idan an danganta su da bididoyin da dama suka riga suka dauki hankali a shafin. A babban shafin TikTok a kan manhajar da ke bisa waya, akwai shafuka biyu: For you page (FYP) – shafin ku, da kuma Following – mai dauke da shafukan da ku ke bi.  A shafin FYP, akwai shafuka daban-daban wadanda kan bayyana bisa shawarwarin da suka samu daga tsarin dokoki da lissafin da aka sanya cikin manhajar, yayin da za’a iya ganin sauran bididyoyin a bangaren da ke dauke da wadanda mai shafin ke bi – wato shafin Follwoing. Masu kirkiro bayanai sukan yi amfani da alamar ta hashtag ne saboda wannan tsarin dokokin da lissafin da aka sanya cikin manhajar ya gano su.

Duk da cewa ta haka ne ake amfani da hashtags, wata sa’a sukan yi karin bayani dangane da bidiyo dan su yaudari jama’a ko kuma su dora sabon bidiyo a kan tsoho. Wannan ya kan faru idan akwai hashtags kamar #comedy – wato #barkwanci ko #prank – wato #ba’a a cikin gurbin da aka tanadar dan kwatancen bidiyon. Idan dai haka ne kada a dauke shi da gaskiya ko da ma batun ya yi kama da gaskiyar.

  • Tantance shafin

Bayanin da akan bayar a shafin da ke karin bayani a kan wanda ya mallaki shafin da ke wallafa bidiyon, kyakyawar hanya ce ta tantance sahihancin bidiyon da aka wallafa. Ka da ku kula da yawan mutanen da suka kalli bidiyon. Watakila ma ya riga ya yaudari wasu ko. 

  • Nemi bayanin da ke kwatancen sautin

Yawancin bidiyoin da ke kan TikTok sukan yi amfani da sautin da kowa ya riga ya sani ne. Wato wasu bude baki kawai suke yi yayin da ainihin sautin da suke kwafa ya ke bugawa a bayan fage. Ya kan kasance tamkar gaskiya idan aka yi da kyau. Hanyar da ta fi kyau wajen tantance wannan shi ne idan aka suba wajen da aka tanadar dan rubuta wanda ya kirkiro sautin da ake amfani da shi. Idan har akwai wannan kwatancen, da zarar aka latsa zai kai mutun zuwa ga sautin na ainihi da ma duk sauran bidiyoin da suka 

Gano labaran bogi a shafin Twitter

  • Amfani da shafin bincike – wato search

Shafin binciken Twitter na da taimako sosai, tamkar wani dan karamin shafin google ne. Za ku yi mamaki idan kuka ga irin bayanan da za’a iya samu daga shafin binciken twitter idan har kuka yi amfani da irin kalmomin da suka dace. Idan har kuka ga sako a twitter dole ku tantance. Kuna iya hin hakan ta hanyar kwafan wasu daga cikin mahimman kalmomin da ke kunshe a sakon ku sanya su a cikin shafin binciken na search. Idan mutane na magana a kai, za’a sani. Haka nan kuma, zai fayyace duk abin da ake so a sani dangane da labarin, wato idan gaskiya ce ko kuma dai abun da ba wanda ya sani ne. 

  • Kwatanta shi da abun da ke shafukan sada zumunta ko na labarai

Wata sa’a ana bukatar a duba abun da ke wasu shafukan domin samun karin bayani. Idan ku ga hoto tare da wani labari, kuna iya sanya hoton cikin manhajar binciken hotuna na google ku gani idan akwai wani labarin na daban ko kuma dai wasu hotunan masu kama da wannan. Kuna kuma iya duba shafin Facebook ku gani ko akwai hotunan da ke tashe wadanda su ma suke bayani dangane da batun da kuke kokarin tantance gaskiyarsa. Kyakyawar misali ita ce sadda wani ya wallafa labari dangane da wani batun da ya yi zargin bankin Zenith ya fada, to amma da aka duba ainihin abun da bankin ya bayyana a shafin Facebook sai aka ga ba daidai ba ne. 

  • Duba kwanan wata da lokacin da aka sanya labarin

Lura da kwanan wata da lokaci na iya taimakawa wajen tantance gaskiyar batu idan har mutun na binciken wani zargi. Kwanan wata da lokaci na iya nuna gibi ko rashin daidaito a labarin musamman idan abu ne wanda ke da nasaba da lokaci. Wannanyana da kyau idan kamar an dauki hoton wani bayani ne aka yi amfani da shi. Daga nan mutun zai gane ko zargin ya bulla tun kafin ainihin abun da ya faru ne ko kuma da dadewa da 

A Karshe

Iya gano labaran bogi cikin sauki a shafukan guda biyu na da mahimmanci. Wannan zai taimaka wajen kare yaudarar mutanen da ba su ji ba su gani ba daga shiga duhu saboda bayanan da ba dai-dai ba. Yayin da Najeriya ke fama da matsalolin da ka iya jefa ta cikin wani yanayi na rashin daidaito wanda kuma zai iya babban lahani ga dimokiradiyyar kasar da ta riga ta raunata, tantance labaran da ba gaskiya ba na iya taimakawa.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button