Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Wani shafin yada labarai a Facebook ya wallafa labarin cewa hukumar EFCC ta bada belin Rabi’u Musa Kwankwaso.
Hukunci: Yaudara ce! Domin babu tabbacin EFCC ta kama Kwankwaso bare ta bada shi beli, sai dai akwai majiyoyi da suka ce ta gayyace shi a ofishin ta.
Cikakken Bayani
A wani bayani da shafin yada labarai a Facebook mai suna Alfijir Hausa ya wallafa a ranar Laraba 5 ga watan Yunin 2024, ya ce “hukumar EFCC ta bada belin tsohon gwamnar Kano Rabi’u Musa Kwankwaso bisa wasu Sharuɗɗa” bayan da ta kama shi da zargin badaƙalar naira biliyan biyu da rabi.
Labarin ya janyo muhawara sosai a kan shafin inda a cikin sa’o’i takwas kawai aka yi sharhi (comments) har sau dari da uku yayinda aka yada labarin sau hamsin a cikin rana daya kawai.
- Hoton da aka zakulu a Facebook
Wannan na zuwa ne bayan da kungiyoyi masu zaman kansu, har da Northern Arewa Network ke ci gaba da yin kira ga hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta binciki tsohon gwamnan akan badaƙalar kudade a lokacin gwamnatin sa da kuma zargin karkatar da kudaden kamfe na jam’iyyar NNPP.
La’akari da yadda labarin ya ja hankalin mutane Dubawa ta yi bincike don gano gaskiya.
Tantancewa
A baya-bayan nan cece-kuce akan zargin aikata ba daidai ba da kudaden kamfe na jam’iyyar NNPP ya janyo maganganu da dama tare da kiraye kirayen kama tsohon gwamnan jihar Kano kuma dan takarar shugaban kasa a zaben shekara ta 2024 Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.
Hakama akwai tsohon binciken da hukumar ke yi masa a kan badaƙalar kudaden fansho na ma’aikatan jihar Kano da suka kai Naira biliyan 10.
A binciken da muka yi mun gano wani labari da jaridar Punch ta wallafa, dake nuna cewa hukumar EFCC ta gayyaci Kwankwaso ofishin ta domin yayi bayani akan binciken da take ci gaba da yi inda ake zargin zambar kudaden fansho biliyan 2.5.
Haka ma mun ga labarin a jaridar Vanguard inda ita kuma ke cewa EFCC ta gayyace shi ne kan zargin karkatar da kudaden yakin neman zaben jam’iyyar NNPP.
Wasu jaridu da dama na Najeriya sun ruwaito labarin cewa EFCC ta gayyaci Kwankwaso domin ya amsa tambayoyin ta.
Shin EFCC ta gayyaci Kwankwaso?
Duk jaridun da suka ruwaito wannan labarin basu ambato hukumar EFCC na tabbatar da gayyatar Kwankwaso domin amsa tambayoyi ba akan wannan bincike ba, domin kuwa jami’in hulda da jama’a na hukumar Dele Oyewale, ya ki cewa uffan akan wannan batu.
Ana haka ne kuwa sai shugaban jam’iyyar NNPP a jihar Kano Hashimu Dungurawa ya karyata zargin bincike akan Sanata Kwankwaso, inda yace yan adawa ne ke yada wannan jita-jita domin shafawa jagoran su kashin kaji.
Sai dai a shekara ta 2021, Dr Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi bayanin cewa yaje ofishin na EFCC inda ya gabatar da bahasi akan korafin da aka gabatar a kan sa tun a shekara ta 2015 kan zargin karkatar da kudaden yan fansho a jihar Kano.
A Karshe
Yaudara ce! Bincike ya nuna cewa EFCC bata tabbatar da cewa ta kama Kwankwaso bare ta bada shi beli, sai dai akwai rahotanni daga kafafen yada labarai na Najeriya sun ce ta gayyace shi a ofishin ta tare da yi masa tambayoyi.
An yi wannan binciken ne karkashin shirin Binciken Gaskiya na DUBAWA wato Indigenous Language Fact-Checking 2024, tare da hadin gwiwar Vision 92.5FM, Sokoto, domin dabbaka labarun “gaskiya” a cikin aikin jarida da karfafa ilimin yada labarai.