African LanguagesHausa

Jami’ar Najeriya ba ta Hana Dalubanta Kiristoci gudanar da ayyukansu na ranar lahadi ba

Zargi: Wani mai amfani da shafin tiwita ya yi zargin cewa jami’ar tarayya na Dutsen-Ma a jihar Katsina ta hana dalubanta kiristoci gudanar da ayyukansu na ranar lahadi a cikin makarantar. 

Wani mai amfani da shafin tiwita da suna @FestusGreen ranar litini 7 ga watan Maris ya wallafa wani bayanin da ke zargin cewa makarantar ta hana kiristoci gudanar da shirye-shiryensu a cikin makaranta.

Mai zargin ya danganta bayanin shi da wata wasika wadda ya ke zargi mahukuntan jami’ar ne suka bayar. Sa’annan ya ce ranakun Talata da Laraba ne aka amince da su a matsayin ranakun ibada wa kiristoci amma banda lahadi.

Mutane same da 900 suka yada labarin abin da ya janyo martanoni daban-daban daga ‘yan Najeriya.

@UchennaObiora wani mai amfani da shafin tiwita ya ce abin da ya faru ke nan a jami’ar Umaru Musa ‘Yaradua amma ba wanda ya ce uffan.

Ita kuma @_sarah_Emmanuel ta musanta zargin inda ta ce “Ba ku karanta abu da kyau kafin ku wallafa. A ina ne aka rubuta wai an hana ayyukan addini ranar lahadi?”

Radio Biafra a shafin shi na facebook shi ma ya wallafa zargin inda mutane sama da 200 suka sake wallafawa.

Dan yawan mutanen da suka yi ma’amala da batun zargin ne DUBAWA ta kuduri aniyar gano gaskiyar batun. 

Tantancewa

DUBAWA ta gano cewa wasu marubutan blog su ma sun yi amfani da wannan zargin a shafukan su. Misali shafin Siggy da News Spot Nigeria duk sun wallafa batun. Sai dai jaridar The Punch, wadda ke cikin jaridu masu nagarta a Najeriya, ta ce mahukuntan jami’ar sun karyata zargin cewa sun takaita lokutan ibadan dalibai kiristocin. 

Da DUBAWA ta tuntubi darektan hulda da jama’a na jaridar The Punch, Habibu Matazu, ya tabbatar mana cewa rahoton da suka yi gaskiya be kuma takardar da aka yi zargi yana dauke da dokokin da suka takaita ayyukan dalubai kiristocin karya ne. 

Bayan nan ne jami’ar ta fitar da sanarwar manema labarai ta karyata labarin. 

Baya ga sanarwar manema labarai 

Baya ga sanarwar manema labarai DUBAWA ta tuntubi Stephen Shekari, shugaban Zumuntan Kungiyar Daliban Evangelika na Kasa. Shekari a hirar da muka yi da shi ta wayar tarho ya ce mana ba wai an hana dalubai kiristoci gudanar da ayyukan ibadansu a cikin makaranta baki daya ba ne, an dai rage ranakun da suke ibada ne daga uku zuwa biyu. 

“Da ma kwanaki uku ne a mako mu ke sujada sai aka rage zuwa kwanaki biyu.  Yawancin ayyukanmu ranar asabar mu ke yi, kuma sai aka cire asabar daga cikin ranakun abin da ya raunata mana hidimominmu sosai ke nan,” ya ce. 

Shugabn kungiyar ya ce ranar asabarin na da mahimmancin sosai domin ranar lahadi dalibai da mallamai duk suna amfani da cocin makarantar wajen yin sujada dan haka ba su da wurin ganawa. 

“Ayyukanmu na mako ne aka takaita. Ayyukan makon ne muke ta korafi a kai ba sujadar da aka yi ranar lahadi ba,” ya tabbatar mana. 

A Karshe

Zargin da ake yadawa karya ce kawai. Cocin jami’ar na cigaba da gudanar da sujadarta kowace lahadi. Yawan kwanakin da ‘yan kungiyar kiristocin ke gudanar da ayyuakna makonsu ne aka takaita. 

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Translate »