Getting your Trinity Audio player ready...
|
Cikakken bayani
Tun asaki da ma Turawa aro kalmomi suke yi daga wasu harsuna. Dan haka ganin kalmomin Faransanci ko Girkanci ana amfani da shi a harshen turanci tare da ma’anan kusan iri daya ko ma daban baki daya ba wani abin mamaki ba ne.
Kamus na turanci wato The Oxford English Dictionary (OED) kundi ne da ke adana labaran asalin kamomi da yadda suke bunkasa da habbaka. Idan har ana son kalma ta shiga cikin kamus din ko kuma OED, dole a fara da sa shi cikin kalmomin da ake sanyawa ido. Wanna jaddawalin na dauke da kalaman da aka samo daga sassa daban-daban wadanda kuma a kan tara a tantance baki daya.
Bayan da aka bi wadannan hanyoyin ne Oxford English Dictionary kwanan nan suka gabatar da kalmomin Najeriya 20 a bayan da suka sabunta Kamus din a watan Disemban 2024. Wadannan kalmomi ne wadanda da ma aka saba amfani da su wajen zantawa a Najeriya.
Kafin wannan karon, da ma can an taba sa kalmomin Najeriya cikin Kamus din a sabuntawar da suka yi cikin watan Janairun 2020
A wani bangare na shirin DUBAWA na fadakar da jama’a, wannan rahoton na bayyana kalmomin da aka kara:
Sabbin kalmomin da aka kara sun hada da:
- Agbero: Wani wanda ke karbar kudi wurin mutane da yin tasiri kan jama’a ta yin amfani da karfi da miyagun ayyuka. Kalam ce kuma wadda ake amfani da shi wajen kwatanta zauna gari banza wadanda ke zawan zama a tashar mota.
- Area boy: Wato yaro ko magidancin da ke ansar kudi da karfi da yaji wajen mutane. Area boy yawanci suna da hanni a miyagun ayyuka irinsu sata, sha ko sayar da kwayoyi da sauran abubuwan da suka karya doka.
- Cross-carpeting: wannan kuma na nufin sauyin shekar da ‘yan siyasa kan yi daga jam’iyyarsu su koma wata wadda suka ga cewa za ta fi taimaka mu su wajen cimma burakansu, musamman samun nasara a zabe.
- Kanuri: Kanuri na nufin mamba na wani rukunin wata al’ummar ‘yan Afirka wadanda yawanci suke rayuwa a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya amma kuma a kan sami wasu ‘yan kalilan a yankunan kasashe makotan Najeriyar wadanda suka hada da Niger, Chad, Kamaru da Sudan.
- Cross-carpet: Wannan na nufin sauya jam’iyya.
- Kobo: Tsohon kudin Najeriya ne. A shekarar 1973 aka fara amfani da shi sai dai yanzu ya bata saboda ba shi da wata daraja a kasuwannin Najeriya.
- Jand: Wannan na nufin komawa wata kasa da zama. Wato komawa kasar waje da zama musamman dan karatu ko samun aikin yi ko kuma dai wata dama wadda za ta inganta rayuwar mai tafiyar.
- Janded: Wannan na iya nufin inda wani/wata ta koma a kasar waje; ya na kuma iya nufin halayyar wani ko wata.
- Naija: wato lakabi ko kuma yadda ake kwatanta Najeriya.
- Abi: kalma ce ta Yarubawa wadda ake amfani da shi wajen tambayar da akan yi idan ana neman tabbacin wani batu.
- Japa: Kalmar da ‘yan Najeriya ke amfani da ita wajen kwatanta yadda ake barin kasar zuwa kasashen da ke da karfin tattalin arziki da nufin samun ingantaciyar rayuwa.
- Suya: Wato tsire dai ke nan, kuma wannan kalma ce da Hausawa ke amfani da ita wajen kiran nama gasashiya wadda ake yankawa a tsira, sa’annan a gasa a bakin wuta kafin a ci.
- Eba: An fi saninta da taiba a Hausa kuma garin rogo ne ake dafawa a ci da miya.
- Edo: Edo sunar wata jiha ne a yankin Kudu maso Kudancin Najeriya.
- Gele: Sunan da ake kiran irin manyan dankwalayen da ake daurawa wajen buki, wadanda yawancin a kan yi su da tufafi iri-iri kamar su Aso-oke, Adire, Damask, Sego, da sauransu. An fi samun shi a matan yankin Yammacin Afirka a kasashe irin su Najeriya, Benin, da Togo.
- Yahoo: Wannan na nufin zambar da ake yi ta yanar gizo na tambayar kudi daga wadanda ba su ji ba su gani ba dan wasu kayayyaki ko aikin da ba za’a taba yi musu ba.
- Yahoo boy: Mutunn, musamman namiji, wanda ke zamba cikin aminci ko kuma aikata yahoo din a yanar gizo-gizo.
- Yarn dust: wato maganar banza.
- 419: Wannan na nufin abin da ‘yan Najeriya ke kira yaudara a yanar gizo, musamman wadanda sukan tambayi kudi kai tsaye. Lambobi ne da ke zaman wata alamar gane zambar da ake yi na kudi inda wasu sukan bukaci makudan kudi daga wajen mutanen da ba su taba gani ba da nufin cutar su.
- Adire: Adire yadi ne irin wanda yawanci matan Yarubawa ke rinawa.