Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Wani mai amfani da shafin X yayi da’awa (claimed) cewa sanata a Najeriya yana daukar naira miliyan 2.48 a duk wata a matsayin gundarin albashinsa (salarinsa) baya ga wasu abubuwan.
Hukunci: Akwai kanshin gaskiya a labarin!Shugaban majalisar dattawa a Najeriya na karbar salari miliyan 2.48 duk wata, sai dai sauran sanatoci na karbar naira miliyan 2.26 duk wata.
Cikakken Sakon
Yayin da ‘yan Najeriya ke fama da matsalar tsadar rayuwa (costs of living) a bangare guda kuma ana ci gaba da kiraye-kiraye na a kara mafi karancin albashi (minimum wage) sai batun abin da ake biyan sanatoci ya zama babban labarin muhawara a kasar.
Majalisar dattawan Najeriya (Senate) ita ce mafi girma wajen fitar da doka a kasar, Ita aka dorawa alhaki na yin dokoki (laws) da yi wa wasu kwaskwarima su kuma ke amincewa da ba da mukamai na gwamnati da bangaren shari’a . Tana dai shan suka kan kudaden da ake kashe mata
Yayin da ake samun rahotanni cewa sanatoci na karbar makudan kudade a duk wata idan aka kwatanta (compared) da takwarorinsu a fadin duniya, akwai dai bayanai mabanbanta.
Ana tsaka da wannan muhawara ce a ranar 3 ga tawan Yuni 2024 wani mai amfani da shafin X sai ya fitar da wata wallafa (tweeted ) cewa Sanatoci a Najeriya suna karbar albashi N2.48m duk wata gundarin albashi baya ga wasu kudaden.
Ga dai abin da ya rubuta,
“Abin da kowane sanata a Najeriya ke samu gundarin albashi- N2.48m, Alawus na wasu ayyuka masu wahala– N1.24m da Alawus na yankunan da suka fito– N4.97m, kudin alawus na kujeru – N7.45m, da kudin jarida….…amma mu abin da za a biya mu N150,000-N200,000 ya gagara duk da hauhawar farashin kayan abinci ga cire tallafin manfetir.!”
Ya zuwa ranar 6 ga watan Yuni wannan wallafa (post) an kalla (views) sama da sau 260,000 an samu wadanda suka nuna sha’awarsu (likes) 3,700 da wadanda suka sake wallafawa (retweet) 2,800 da masu tsokaci 228 ( comments ) a shafin X.
Akwai dai tsokaci da dama na masu amfani da shafin da ya nunar da rashin yarda a dangane da da’awar.
Wani mai amfani da shafin na X @theglobalfeed_, ya rubuta: “wannan abin ban mamaki ne karara” wato ya nuna cewa abin da sanata ke samu a duk wata ya fi karfin abin da mutum guda zai bukata, adadin kudin fa shine yana samun miliyan N23.4 kimann Dalar Amurka ($57,000 USD).” ”
Shima @olorunwadayo ya rubuta cewa “Duk wadannan kudade da suke samu ba za ka ji tashin farashin kayayyaki ba, amma da zarar an ce ma’aikaci zai dauki 400k ko sama da haka za ka ji hauhawar farashi ta fara.”
Wannan kuwa mai suna @DiceOfTruth, nuna rashin yarda yayi inda yace tayaya haka zai zama gaskiya “ how???”
Ganin yadda wannan wallafa ta samu jan hankali da martani a tsakanin masu amfani users, da shafin na Twitter, DUBAWA ya ga dacewar gudanar da bincike kan batun.
Tantancewa
A cewar hukumar da ke kula da rarraba haraji da kudaden shigar gwamnati Revenue Mobilisation Allocation and Fiscal Commission (RMAFC), wacce ke fitar da salari da kudadaen alawus-alawus na sanatoci, a jadawalin kudaden da ake ba wa jami’an kamar yadda aka sabunta a 2007, wannan hukuma ta bayyana abin da sanatoci ke samu. Yayin da shugaban sanatocin ko shugaban majalisar dattawa ke samun miliyan N2.48 sauran sanatocin na samun miliyan N2,26.
Ga jadawalin kudaden albashi da hukuma ke ba wa shugaban majalisar dattawan a harshen Turanci.
Image Source: rmafc.gov.ng
Ga kuma abin da suma sanatocin ke samu:
Image Source: rmafc.gov.ng
Fayyacewa kan abin da ke shigar wa sanatocin abu ne muhimmi, a jimlace abin da ke shigarwa sanatocin ya kunshi bangarori biyu, albashinsu da “kudaden gudanarwa” inda anan ne ake muhawarar.
Wasu rahotanni sun nunar (quoted) da cewa ana biyansu miliyan N13.5 a duk wata, amma a shekarar 2021 lokacin shugaban majalisar dattawan shine Ahmed Lawan yayi karin haske clarified inda yace a kowane watanni hudu ake biyansu inda kudin kan kama miliyan N52 a duk shekara.
Sai dai kuma akwai wani abu muhimmi da ake ta muhawara a kansa wato fadin gaskiya kan hakikanin alawus-alawus da ake ba su. Tana iya yiwuwa a samu banbanci tsakanin abin da hukumar da ke rarraba harajin (RMAFC) ke tsarawa a biya da kuma hakikanin abin da ke zuwa ajihunsu.
Kudaden da ake warewa don hada-hadar yau da kullum anan ne ba a cika tsayawa kan wani adadi ba, don haka nan ne ake zargin za a iya kara adadin alawus din. A kwai kuma wasu bayanan da ke nuna cewa sanatocin na karbar karin kudade fiye da abin da RMAFC ke bayyanawa recommendation karkashin kudaden hada-hadar yau da kullum
Hukumar ta RMAFC ta yi da’awar cewa tana da iyaka kan batun kudaden na hada-hadar yau da kullum sannan kudaden salari da ke zuwa ga ‘yanmajalisa abune da ya kamata al’ummar Najeriya su sani ko suna da bayanai. Ace hakikani ga abin da ake ba su compensation na iya zama ba abu da za a fahimta kai tsaye ba, sannan suna banbanta ya danganta da alawus-alawus da ma abin da za a amfana benefits
Karshe
Binciken da muka gudanar ya nunar da cewa da’awar da ake cewa shugaban majalisar dattawa a Najeriya na karbar miliyan N2.48 a matsayin abin da ke zama salarinsa, za a iya cewa akwai kanshin gaskiya a ciki, sannan sauran sanatocin na karbar miliyan N2.26 a duk wata.
Wannan rahoto an fitar da shi ne karkashin shirin gano gaskiya na DUBAWA 2024 karkashin shirin kwararrun masu gano gaskiya labari na Kwame Karikari da hadin giwa da Diamond 88.5 FM Nigeria a kokarin da ake yi na mutunta fadin gaskiya a aikin jarida da inganta ilimin aikin jarida a Najeriya.