African LanguagesHausa

Karya ce!Gwamnatin Tarayya ba ta amince da N155,000 a matsayin mafi karancin albashi ba a Najeriya

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Gwamnatin Najeriya ta amince za ta biya  N155,000 a matsayin mafi karancin albashi a Najeriya.

<strong>Karya ce!Gwamnatin Tarayya ba ta amince da N155,000 a matsayin mafi karancin albashi ba a Najeriya</strong>

Hukunci: Karya ce: Bincike da shirin binciken gaskiya na DUBAWA ya gudanar ya tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayyar Najeriya ba ta amince da N155,000 a matasin mafi karancin albashi ba a duk zaman da ta yi da kungiyoyin kwadago ko kuma wata kungiya.

Cikakken  sakon

Tsadar kayan masarufi a Najeriya ta sanya kungiyoyin kwadago kiraye-kirayen neman kara mafi karancin albashi ta yadda ma’aikata za su samu sauki daga radadin farashin ababen masarufi a kasar.

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya kafa kwamiti mai bangarori uku bisa jagorancin mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima a ranar 30 ga watan Janairu, 2024, cikin hakkin da aka rataya wa kwamitin ya hadar da ji daga al’umma daga bangarori shida na kasar inda za a ji ta bakin ma’aikata da kungiyoyi masu zaman kansu da fannoni da ba na gwamnati ba da jami’an gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki inda za a tattauna kan batun na mafi karancin albashi.Ya zuwa yanzu mafi karancin albashi shine 30,000 da aka amince da shi (approved) bayan tattaunawa mai tsawo daga bangaren gwamnati da bangaren na ‘yankwadago.

Kwamitin an dora masa wannan aiki da ake sa rai ya mika wa gwamnatin tarayya zuwa karshen watan Maris, daga bisani a turawa majalisa don ta amince da shi.

Ana tsakan da wannan ne sai ga wani mai amfani da shafin X A.Ayofe a ranar 26 ga watan Maris,2024 yayi da’awar cewa gwamnatin tarayya ta amince da biyan N155,000 a matsayin mafi karancin albashi ( the new national minimum wage) a Najeriya. Ya kara da cewa an cimma wannan matsaya ce bayan tattaunawa.

A yadda ya wallafa labarin yace “Gwamnatin Tarayya ta amince da biyan 155k a matsayin mafi karancin albashi, shugabannin NLC da TUC sun godewa duk mambobi da suka shiga wannan tattaunawa kamar yadda suka bayyana a taron manema labarai sannan sun bukaci gwamnatoci a matakin tarauyya da jihohi su aiwatar da abin da aka amince akansa tun da fari, akwai wasu karain bayanan da ke tafe ba da dadewa ba.”

Wannan wallafa (post) da aka ganta sama da sau  210,000 ya zuwa ranar 28 ga watan Maris 2024 ta samu wadanda suka nuna sha’awa (likes) sama da 1,300 da wadanda suka sake yadawa (retweets) 220 sannan an samu masu tokaci kusan 350 a shafin sada zumuntar na X.

Wannan wallafa dai ta samu mabanbantan martani daga masu amfani da shafin wasu na nuna farinciki yayin da wasu ke taka tsantsan da wannan ci gaba.

Wani mai amfani da shafin na X Gerat Bourdillion ya rubuta cewa “Fake News” wato labarin karyayayin da wani kuma mai suna Obina Aguerie yab rubuta cewa “Abin mamaki hakan abune mai yiwuwa kuwa? Yayin da wasu jihohi ke fafutuka su ma biya dubu 30 a matsayin mafi karancin albashin.”

Shi kuwa wani mai amfani da shafin Micheal Agwogie nuna shakku yayi game da inda labarin ya fito inda ya rubuta: Ina tushen labarin yake?”

Ganin yadda ake ci gaba da mayar da martani daban-daban kan wannan wallafa ga kuma irin adadi mabanbanta (contrasting figures ) na bukatu da ‘yankwadagon Trade Union Congress (TUC) da Nigeria Labour Congress (NLC)  suka gabatar kamar yadda rahotanni suka gabata dama sakamakon da ake tsammani daga kwamitin da aka ba wa alhakin wannan aiki da ake tsammani daga  Afrilu 2024, shirin gano gaskiya na DUBAWA ya tsara gudanar da bincike don ganin hakikanin gaskiya kan wannan labari.

Tantancewa 

Da aka fara bincike da Google ta hanyar amfani da wasu muhimman kalmomi babu wata kafar yada labarai sahihiya a Najeriya da ta ba da wannan rahoto, haka nan da aka duba shafin kungiyar ta kwadago (NLC’s social media platforms) da ma shafin fadar gwamnati ( State House) babu wani labari da aka yi da ya shafin wannan batu. 

Da muka tuntubi Abimbola Fasasi, shugaban TUC a jihar Osun yayi watsi da wannan labari da ya ce na bogi ne , yace babu wata matsaya da aka cimma daga dukkanin bangarorin kan kudi N155,000 ya zuwa ranar 28 ga watan Maris, 2024.

Yayin da ake ci gaba da rade-radi (speculations) cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu na iya bayyana mafi karamncin albashi a ranar daya ga watan Mayu a ranar  kwadago ta duniya, babu wata kafa mai karfi da ta tabbatar da haka ko dai daga bangaren tarayyar kjo daga bangaren na ‘yankwadago kan wannan batu.

Kammalawa

A karshe bincikenmu ya ya tabbatar da cewa babu gaskoiya kan wannan da’awa cewa gwamnatin tarayya ta amince za ta biya N155,000 a matsayin mafi karancin albashi a Najeriya, don haka da’awar karya ce.

 Mai binciken yayi wannan aiki ne karkashin shirin gano gaskiya na DUBAWA 2024, karkashin shirin samun kwarrewa na Kwame KariKari da hadin gwiwar gidan rediyon Diamond 88.5 FM Nigeria, a kokari na fito da “gaskiya” a aikin jarida da inganta ilimin aikin jarida a fadin kasar.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button