African LanguagesHausa

Karya! Messi bai ziyarci Davido a Najeriya lokacin bukin kirisimeti ba 

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Lokacin Kirisimeti, shahararren dan kwallon kafar Argentina Lionel Messi ya ziyarci  mawakin Najeriya David Adeleke wanda aka fi sani da Davido.

<strong>Karya! Messi bai ziyarci Davido a Najeriya lokacin bukin kirisimeti ba </strong>

Sakamakon bincike: Karya. Hoton, wanda aka yi amfani da shi a shafin Davido na X an gyara ne. Mawakin bai wallafa wannan labarin ba, kuma Messi bai kai ziyara Najeriya ba.

Cikakken labari

Stan culture is a primary characteristic of the showbiz industry and celebrity life in general. 

Al’adar Stan ko kuma Stan Culture kamar yadda aka fi sani a turance, al’ada ce da ake yawan samu a masana’antar fina-finai da rayuwar taurarin fina-finan baki daya. Lokaci zuwa lokaci, ma’abotan wani tauraro kan fitar da labarai (wata sa’a na karya) masu kayatarwa dan kara mi shi farin jini ko kuma dai tozarta wadanda suke wa kallon makiyarsa.

Ba abun mamaki ba ne a ga ma’abotan taurarin fina-finai suna takaddama ko kuma cacar-baki tsakaninsu a yanar gizo-gizo, inda kowane bangare zai rika neman kare nasa tauraron da kuma kwatanta ire-iren dalilan da ya sa suke ganin na su ya fi kowanne.

Wata kalma ko kuma inkiyar da ake amfani da ita sosai yanzu ita ce GOAT mai nufin greatest of all times a turance ko kuma gwani/gwanar da ba wanda ya taba komawa a fagen da ya/ta shahara. Ana yawan samun irin wadannan mahawarorin a fannoni daban-daban kama daga wakoki har zuwa kwallon kafa.

Lionel Messi, shahararren dan kwallon kafa da Davido sunaye ne da ke yawan bulla a wadannan mahawarorin. Duka biyun suna da ma’abota a kasashen duniya da dama.

Davido mawaki ne da ke da lambobin yabo da mabiya da dama wadanda suka kai miliyan 30 ( kuma ana yawan kiransu the 30 million Gang). Dan Najeriyar ya yi suna sosai, kuma a duk sadda ake mahawara dangane da waka akan hada shi da sauran manyana mawakan Najeriyar irin su Burna Boy da Wizkid.

A daya hannun kuma Messi, ya dauki kyautar Ballon d’Or sau takwas kuma da lambar yabon wanda ya fi zura kwallaye a Turai sau shida. Da shi da Christiano Ronaldo, dan asalin Portugal sun dade suna wannan hamayyar inda ma’abotansu ke mahawara kan wanda ya fi wani a tsakaninsu.

Kwannan nan wani mai amfani da soshiyal mediya ya wallafa wani hoton da ake zargi wai daga shafin Davido aka samu. Hoton na zargin cewa mawakin ne ke sanarwar cewa ya tarbi Messi, wanda ya kai masa ziyara na bukin kirisimeti.

Da muka kalli hoton da kyau, DUBAWA ta lura da cewa labarin da ake da’awar an samu a shafin Davido na dauke da kwanan watan 1 ga watan Janairun 2024. Ya ce, “@leomessi ya zo Najeriya ya yi kirisimeti … GOAT ya sa san GOAT! Ya ci teba har ya gaji.”

Hotunana da ke cikin labarin sun nuna Davido tsaye tare da Messi kusa da wani jirgin sama a wani wuri na daban. Ana iya ganin hoton cikin shafin facebook a  nan.

Tantancewa

Saboda irin kimar da mutanen biyu ke da shi a idon Jama’a, DUBAWA ta ga cewa ya kamata a tantance wannan batun.

Da farko dai mun lura cewa ba’a saita hotunan da kyau ba. Sun yi kama da irin hotunan da aka gyara domin tamkar taurarin biyu na yawo ne a cikin hoton.

Binciken da muka yi da manhajar binciken hotuna na Google Reverse Image Search ya nuna mana cewa hoton da ke hannun dama, an dauko shi ne daga shafin Instagram na Davido wanda ya wallafa a watan Satumban 2023 sadda ya ce bukin lambobin yabo, na bidiyoyin wakokin da aka yi Manchester a Burtaniya.  he made in Sept. 2023 during his visit to the Video Music Awards in Manchester. 

Bisa dukkan alamu kuma an dora hoton Messi ne a kai. Bacin haka, hoton da ke hannun hagu, da farko Messi ne kadai a ciki kuma an dauka ne sadda ya kai ziyara shirin Dubai EXPO wanda aka yi 2020. An wallafa ne a shafin Dolce and Gabana wanda aka tantance a  X, cikin watan Disemban 2021. 

DUBAWA ta kuma ziyarci shafin Davido a X dan tantance sahihancin wannan batun da mai amfani da shafin Facebook ya wallafa. Sai dai mun lura cewa labarin da mawakin ya wallafa ranar 1 ga watan Janairun 2024 bai yi wannan bayanin ba, illa dai kawai ya mika godiyarsa ga ma’abota da masu bin sa saboda goyon bayan da suka nuna mi shi a shekarar 2023.

A labarin na ainihi, ya ma yi kira da a cigaba da mara masa baya a cikin 2024. Labarin ya kunshi wasu daga cikin hotunansa sadda ya ke wasa a lokuta daban-daban cikin shekarar 2023.

Har ila yau sauran abubuwan da ya wallafa ma ba su yi bayani dangane da ziyarar shahararren dan kwallon kafar zuwa Najeriya ba.

Shi kan sa labarin wanda aka sa a Facebook ya yi kama da irin wanda aka kirkiro da sabbin manhojijin da ake iya kirkiro bayanan bogi da su irinsu Photoshop da TweetGen.

Tweetgen manhaja ce da ke wallafa bayanan bogi a shafin X. Ya na da suakin amfani kuma ana iya sa shi cikin kowani irin launi na shafin twitter. Masu amfani da shi na iya gyara shi duk yadda su ke so. Za su iya sa kwanan wata, lokaci, adadin mutanen da suka yi ma’amala da shafin, suka sa alamar Like, da wadanda suka sake yada labarin da sunan bogi – na wanda ke amfani da shafin da dai sauransu.

An ma sake inganta manhajar da duk sabbin kare-karen da aka yi a shafin twitter, hatta alamar nan wadda ke nuna sahihancin shafi.

DUBAWA ta kuma lura cewa harrufan “shubbyedits,” da aka gani a shafin na nuna cewa editing aka yi.

A Karshe

Labarin da ake zargin wai ya fito daga Davido inda ya ke sanar da ziyarar da Messi ya kai masa a Najeriya ba gaskiya ba ne. Messi bai je Najeriya lokacin kirisimeti ba kamar yadda marubucin ke zargi.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button