African LanguagesHausa

Karya ne! INEC ba ta kara wa’adin rajistar zabe a intanet ba

Zargi: Wani mai amfani da WhatsApp na zargin wai INEC ta ce ta kara wa’adin yin rajistar zabe a yanar gizo zuwa 30 ga watan Yuni

Karya ne! INEC ba ta kara wa’adin rajistar zabe a intanet ba

INEC ta kammala rajistar wadanda su ka cancanci jefa kuri’a a shafinta na yanar gizo tun a ranar 30 ga watan Mayu. Kuma ba ta kara wa’adin yin rajistar ba, sai dai yanzu duk mai son yi, dole sai ya je ofisoshin da su ke yi kafin nan da 30 ga watan Yuni

Cikakken labari

Bayan da aka kara wa’adin zabukan fid da gwani na jam’iyyu, kungiyar SERAP wato shirin tabbarar da gaskiya wajen kare hakkokin tattalin arziki da zamantakewar al’umma, ta bukaci INEC da ta daga wa’adin yin rajistar zabe.

SERAP, wadda ta yi barazanar kai hukumar kolin zaben kotu idan har ba ta yi haka ba, ta ce zai baiwa ‘yan Najeriya karin lokacin da suke bukata domin su cika hakkokinsu.

Ana cikin haka, wani mai amfani da WhatsApp ranar 2 ga watan Yunin 2022 ya raba wani hoton da ke bayanin cewa an daga wa’adin yin rajistar zabe a yanar gizo wanda ba sai ka je an gan ka ido da ido ba.

Mutumin ya raba wannan hoton yayin da yake kira ga al’umma da su je su karbi katin zaben su ne.

Ga dai yadda ya bayyana batun: “Yin rajistar PVC: INEC ta daga wa’adin yin rajista zuwa 30 ga watan Yuni! Yanzu baku da wan abun cewa, ga adireshin zuwa shafin yin rajistan zaben (CVR Portal)

Ganin cewa al’umma tana bukatar bayanan gaskiya dangane da yin rajistar zaben, DUBAWA ta ga cewa yana da mahimmanci a yi wannan binciken.

Tantancewa

Da muka kai ziyara zuwa shafin na INEC da adireshin da marubucin WhatsApp ya bayar mun ga cewa an rubuta wata sanarwa mai mahimmancin da ke cewa an kammala rajista ta yanar gizo tun ranar 30 ga watan Mayu yayin da ake cigaba da na CVR har zuwa karshen Yuni.

To rajistar da ake yi a yanar gizo-gizon ta bambamta ne da CVR? A’a babu banbanci. Tsarin na CVR ya hada da (na farko yin rajista na matakin farko da kuma daukar hoton yatsotsi) daukar sunayen wadanda suka yi rajista amma kuma su ke neman sauyi ko na wurin zabe ko kuma wadansu bayanan su da kuma cire wadansu bayanan da ba’a bukata.

DUBAWA ta tuntubi kwamishanan INEC na kula da yada labarai da wayar da kan masu zabe, Mr, Festus Okoye wanda ya ce mana an daina yin rajista a yanar gizon, wadanda ke da gyare-gyaren da su ke so su yi suna iya yi amma duk rajista sai dai a je a yi ido da ido.

Babban sakataren yada da labaran shugaaban na INEC Rotimi Oyekanmi ya bamu tabbacin cewa an kammala yin rajistar a yanar gizo.

A Karshe

Zargin wai ana cigaba da yin rajistar masu zabe a yanar gizo-gizo ba gaskiya ba ne an riga an kammala shi tun ranar 30 ga watan Mayun 2022. Yanzu sai rajista na ido da ido ake ye wanda za’a cigaba har zuwa 30 ga watan Yuni. Dan haka wadanda ba su riga sun sanya bayanansu da hotunan yatsunsu ba, yanzu ba za su iya yi ba domin lokaci ya kure mu su.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button
Translate »