PC: gateway-africa.com/
Zargi: Wani bidiyo wanda ake ta yadawa a soshiyal mediya a Najeriya, ya nuna wadansu maza da mata suna raira wakoki yayin da su ke rike da bindigogi. Taken bidiyon na kokarin bayyana cewa wasu matan Filani ne aka baiwa bindigogi domin su kai ma kablilar yarubawa farmaki a duk yankunan da su ke a Najeriya

Wannan labarin ba gaskiya ba ne. DUBAWA ta gano cewa a yankin Afar na kasar Habasha da ke yankin gabashin Afirka aka dauki hoton bidiyon, ba a Najeriya kamar yadda ake zargi ba
Cikakken labari
Ranar Lahadi 5 ga watab Yuni wadansu mahara su kai hari kan wadansu wadanda su ka je ibada a cocin katolikan st Francis da ke garin Owo a jihar Ondo. Yayin da โyan sanda ba su riga sun kai ga gano wadanda suka aikata wannan aikin ashar ba, gwamnatin tarayya ta dora alhakin harin a kan kungiyar ISWAP duk da cewa ba ta da wata kwakwarar shaida ko hujja.
Kwanaki biyar bayan harin wadansu rahotanni sun bulla a soshiyal mediya suna zargin an kama maharan. Sai dai kuma rundunar โyan sandan jihar Ondo ta karyata zargin cewa an kama wasu wadanda ake zargi da taโaddanci.
To amma bacin haka an cigaba da tabka mahawara a Najeriya dangane da wadanda ke da alhakin tabka wannan mugun abun, inda wadansu ke zargin Filani da aikatawa.
Bayan harin na Owo, wani shafin Facebook ya wallafa wani bidiyo mai tsawon dakiku 30 da taken da aka yi mi shi da harshen yarubanci wanda ke cewa an yi wa matan Filani dammara domin su kai hari kan Yarubawa.
Ga fassarar taken :ย
In kun yarda ku yi hattara, Filani sun fara yi wa matansu dammarar makamai dan su kashe yarubawa. Muna bukatar yin adduโa dan kada mu sake samun irin wadannan โyan siyasar da mu ke da su yanzu. Ya kamata mu fadawa โyan siyasa cewa ba zaโa yi zabe a kasar Yarubawa ba, tsare rayukanmu ya fi komai mahimmanci a wannan lokacin. #โYancin Walwala #Yorubanation
Da muka duba irin sharhin da aka yi a karkashin bidiyon mun lura cewa mutane da yawa sun yarda wai da gaske ne Filani na kokarin kai hari kan Yarubawa kamar yadda labarin ya fada. Wani mai tsokaci Oluwasegun Adegbule ya tambayi mahukuntan kasar dalillin da ya sa ake barin fararen hula da bindigogi.
โBindigodin wa ne ne? Na โyan sanda ne, ko sojoji ko jamiโan tsaro bayan shugaban kasar ya ce duk wanda aka kama da bindiga kirarย AK47 wanda bai kamata ya na dauke da shi ba, a cafke shi a kulle. Wannan bai dace ba tamkar harshen damo ake yi,โ a cewar mai amfani da shafin na Facebook.
Kashe-kashen da aka yi a Owo ya bar โyan Najeriya da dama a cikin wani yanayi na fargaba abun da kuma ya sanya yanzu sai a ga abu kadan ya yaudare jamaโa. Wannan bidiyon misali ne mai kyau dangane da wannan yanayin domin mutane da yawa da suka yi tsokaci dangane da batun sun nuna tsoro, fargaba da sauransu shi ya sa DUBAWA ke so ta fayyace gaskiya.
Tantancewa
DUBAWA ta fara da tantance hoton bidiyon a manhajar tantance hotuna ta InVId. A nan nazarinmu ya gano cewa bidiyon ya fara bayyana a soshiyal mediya ranar 12 ga watan Maris 2022 a wani labarin da aka wallafa a shafin Facebook wanda ya kwatanta abin da ake gani cikin bidiyon a matsayin โsamar da almajirai, horas da masu bishara a alโummomin gida da kuma gyara yara gajiyayyu.
A wannan lokacin taken da aka yi wa bidiyon ya yi Allah Wadai ne da bindigogin da matan cikin bidiyon ke rike da shi, yana kiran shi wawanci da kuma dabbanci. Kadan daga cikin taken ya ce:
โMe ya sa ba zaโa illimantar da matan nan domin su gina alโummarmu nan gaba ba!! Ya kamata a kame duk shugabannin wannan alโummar.โ
Da DUBAWA ta binciki bidiyon mai tsawon minti 3 da dakiku20 (3:20) raye-raye da wake-waken da ma rawar da su ke yi ba buki ne ko ma wata kabila daga Najeriya ba.
Sai dai mun gano cewa mutanen โyan kabilar Afar ne wadanda ake samu a kasashen Habasha, Eritrea da Djibouti.
Dama can mutanen kabilar Afar sun dade suna neman kasarsu na cin gashin kan su wadda su ke kira โAfarriaโ ko kuma โAfar Triangleโ a turance na tsawon shekaru fiye da 50 yanzu.
Wadannan mutanen da ke cikin bidiyon wadanda ke dauke da bindigogi dakarun jamaโar Afar din ne wadanda suke kan gaba a gwagwarmayar da su ke yi.
Matar da ke rike da lasupikar tana dauke da tutar da ke da alamun kasar ta Afarria manne a dankwalinta yayin da take waka tana rawa. Tutar Afar tana da launin ja da siraran layuka a kai masu launin ruwan bula/shudi, fari da kore.
Har wa yau a cikin bidiyon ana iya ganin โyan sandan yankin suna tsaye a cikin dandazon mutanen.
DUBAWA ta kuma gano cewa rundunar mayakan sa-kai na Afar (APF) tana da shafin Facebook kuma ita kanta ta raba bidiyoyin rundunar mayakan sa-kai suna rawa suna raye-raye. A daya daga cikin bidiyoyin da ta sanya a watan Maris 2021 akwai mayakan sa kan na Afar a ciki.
Duk da cewa DUBAWA ba ta iya gano ainihin inda aka samo sauran bidiyoyin, nazarin da aka yi kan bidiyon da ake yadawa a Najeriyar ya nunacewa an dauki hotunan ne a yankin Afar da ke kasar Habasha, ba Najeriya ba kamar yadda ake zargi.
A Karshe
Labarin da ke zargu wai matan Filani sun yi dammarar bindigogi domin su kai ma yarubawa hari a yankuna daban-daban na kasar ba gaskiya domin DUBAWA ta yi bincike taย gano cewa lamarin ya akfu ne a yankin Afar da ke kasar Habasha a yankin gabashin Afirka ba Najeriya kamar yadda ake zargi ba.
