African LanguagesHausa

Labarin da ke bayanin cewa gwamnan Imo ya ce gwamnatinsa za ta dauki nauyin aure tsakannin wasu kabilun jihar yaudara ce.

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Wani mai amfani da shafin Facebook na da’awar cewa gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, ya sanar cewa za’a gudanar da bukuwan aure kyauta tsakanin ‘yan asalin jiharsa da Filanin da ke zama a jihar.

Labarin da ke bayanin cewa gwamnan Imo ya ce gwamnatinsa za ta dauki nauyin aure tsakannin wasu kabilun jihar yaudara ce.

Hukunci: Yaudara! Binciken DUBAWA ya nuna cewa hoton ma da aka hada labarin an gyara shi, ta yadda zai zo daidai da yaudarar da ake so a yi wa jama’a kuma a yanzu haka batun ya shiga ko’ina.

Cikakken bayani

A ‘yan kwanakin nan, an yi ta samun rigingimun da ke da nasaba da kabilanci tsakanin manyan kabilu ukun da ke Najeriya a kafofin sada zumunta daban-daban.

Ana cikin haka ne wani mai amfani da shafin Facebook, Ferdinand Azi, ranar 30 ga wata Satumba, ya yi ikirarin cewa gwamnan jihar Imo, gwamna Hope Uzodinma, ya amince da gudanar da aurarraki kyauta tsakanin ‘yan asalin jihar da Filani mazauna jihar.

Hade da wannan bayanin akwai hoton jaridar This Day da ke bayanin cewa duk wani mazaunin jihar da ya ki mutunta wannan dokar zai gamu da tarar Nera miliyan daya.

Sadda  DUBAWA ta ga wannan labarin, ya na da tsokaci 14 da alamar like 5 sa’annan an sake raba shi sau daya.

Bacin haka DUBAWA ta kuma lura cewa wasu masu amfani da shafukan X da Facebook Su ma sun sake raba labarin. Kamar yadda muka gani a  nan, nan, nan, nan, da nan.

Yayin da wasu suka amince da labarin, wasu sun bayyana shakkun su dangane da sahihancin kasancewar irin wannan manufar.

Wani mai amfani da shafin na Facebook Bright Chinedu, tambaya ya yi: “Me ya sa ba zai fara da aurar da ‘yarsa ba?”

Yayin da shi kuma Chukwuma Ndukwe ya rubuta: “rikicin 419 na mutumiun nan ba zai taba karewa ba. Me ya sa bai fara da ‘yarsa ba?”

Shi ma wani mai amfani da shafin Ifeanyi Okoh cewa ya yi: “Sam ban yarda da wannan labarin ba. Ina sane da cewa Uzodinma karen farauta ne dama amma har ya kai wannan matakin kai na ba ya dauka.”

“Ya kama mu ji daga wurin mutanen jihar Imon su ma! A cewar John Kalu.

Bukatar kawar da duk wani rashin fahimta game da batu irin wannan mai sarkakiya ne ya DUBAWA daukar nauyin tantance wannan labarin. 

Tantancewa

DUBAWA ta yi amfani da manhajar binciken hotuna na Google Reverse Image Search, Wanda ya kai mu ga wani rahoto a jaridar  This Day wanda aka wallafa a watan Agustan 2021, inda kafofin yada labarai suka karyata wannan da’awar.

Rahoton ya nuna cewa an sauya babban shafin jaridar daga taken da ke kai dama wanda ke cewa “Buhari na matukar farin ciki bayan da NNPC ta sami akasi a karon farko ta bayyana cewa ta sami ribar N287bn a karon farko cikin sekaru 44,” zuwa  “Abin mamaki: Uzodinma ya ayyana aure kyauta tsakanin Filani da ‘yan matan jihar Imo.”

Bugu da kari, mu duba duka kafafen yada labaran da muka san suna da sahihanci dan ganin ko suma sun dauki labarin, a nan ma ba mu ga komai illa rahotannin da muka gani a TheCable da Kamfanin dillancin labaran Faranca Agence France-Presse (AFP) wadanda su ma suka karyata labarin da ya bayyana a jaridar This Day cikin shekarar 2021. 

A karshe

Binciken DUBAWA ya tabbatar mana cewa wannan da’awar ba ta da tushe yaudara ce kawai. Haka nan kuma binciken ya nuna cewa an gyara hoton da aka yi amfani da shi ne dan a yaudari jama’a.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Translate »