African LanguagesHausa

Labarin kama fasto yana safarar makamai ga yan ta’adda a Jos, tsohon labari ne

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Wani mai amfani da Facebook ya yi ikirarin cewa an kama malamin coci da makamai zai kai wa ’yan ta’adda a Jihar Plateau.

Labarin kama fasto yana safarar makamai ga yan ta’adda a Jos, tsohon labari ne

Hukunci: Yaudara ce. Ba sabon labari ne ba; tsohon hoto ne tun daga 3 ga Fabrairu, 2025 aka sake yadawa a matsayin sabon lamari.

Cikakken Bayani

A daidai lokacin da ake fama da tashin hankali, hare-hare da matsalolin tsaro musamman a yankunan Arewa da tsakiyar Najeriya, shafukan sada zumunta suna kara cika da labaran da ake yadawa ba tare da tantancewa ba. 

A kwanan nan wani mai amfani da Facebook ya wallafa wani hoto tare da sako mai taken:

“Yanzu yanzu an kama Malamin Coci da makamai zai kaiwa ’yan ta’adda a Jihar Plateau.”

Wannan ya ja hankali sosai, inda sama da mutane 4,400 suna dangwala yatsa ga hoton yayin da aka yada shi sau 349, kamar yadda muka zakulo a ranar Jumma’a, 21 ga Nuwamba, 2025. 

Sakamakon yadda sakon ya yadu, mutane da dama sun gaskata cewa sabon kame ne da aka yi kwanan nan a Plateau.

Akill Abdallah Abubakar ya yi martani cewa “Kiristoci fa su ne matsalar Najeriya”

Sai dai Nkeki J Ndirmbitah tambaya ya yi cewa, waye faston, a wace coci?

Ganin yadda wannan labari ke iya tayar da hargitsi, DUBAWA ta yi bincike don gano gaskiyar lamarin.

Tantancewa

DUBAWA ta fara da tantance fuskar jami’in ’yan sanda da ke cikin hoton aka yada. 

Mun gano cewa jami’in da ke hira da wanda ake zargi shi ne CP Muyiwa Adejobi, wanda tsohon mai magana da yawun rundunar ’yan sanda a lokacin da lamarin ya faru. 

Amma a yanzu ba shi ne kan mukamin ba; an maye gurbinsa da CSP Benjamin Hundeyin, wanda ke rike da wannan matsayi a halin yanzu.

Saboda haka ne, DUBAWA ta tuntuɓi CSP Hundeyin domin samun karin bayani.

Ya tabbatar da cewa lamarin ya faru ne tun 3 ga Fabrairu, 2025, kuma ya tura mana bidiyon yadda aka gabatar da wanda ake zargin.

A bidiyon, an ga malamin coci yana bayanin cewa makamin da aka same shi da shi wai domin kare kansa ne. Sai dai jami’in ’yan sanda ya bayyana masa cewa mallakar irin wadannan makamai haramun ne, kuma babu wata hujjar da za ta amince da mallakar su domin kare kai.

DUBAWA ta sake duba rahotannin kafofin watsa labarai, inda muka ga rahoton kafar News Central wanda ita ma ya ruwaito wannan kamen na gungun masu safarar miyagun makamai ga yan ta’adda a jihar Plateau a watan Fabrairu na 2025, ba a cikin watan Nuwamba na 2025 ba. 

Dukkan bayanan sun yi dai-dai da bidiyon da jami’in hulda da jama’a na yan sanda Benjamin Hundeyin ya samar.

Sai dai a wani labarin mai kama da wannan, hukumar tsaron farin kaya DSS ta ce ta kama wani mai safarara makamai a Plateau, mai suna Musa Abubakar, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

A Karshe

Binciken DUBAWA ya tabbatar cewa ba sabon labari ne ba, tsohon lamari ne aka sake yadawa.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button
Translate »