Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Wata mai amfani da shafin Facebook Judith James tayi da’awa (claims) cewa Elon Musk na aikin samar da wani mutum-mutumi da zai taimaka wa mata wajen goyon ciki.
Hukunci: Karya ce! Bayani daga “We, Robots” da Tesla dama wasu kafofi a hukumance sun tabbatar da cewa babu wani aiki da ake yi mai kama da wannan, da aka bayyana ko ake tattaunawa akai, haka kuma dabarun aiki ma da ake amfani da su don gano asalin hoto sun tabbatar da cewa hoton da aka makala an samo shine ta hanyar amfani da kirkirarriyar basira ta AI.
Cikakken Sako
Elon Musk, fitaccen mai harkar masana’antu ne kuma dankasuwa ne mai hangen nesa shine mai kamfanoni na PayPal da SpaceX da Tesla da Neuralink da Boring Company. Mista Musk ya mayar da hankali kan makamashi da ake sabuntawa da bincike a samaniya da harkokin sufuri da kirkirarriyar basira. Daga cikin abubuwa da ya kawo sabbi sun hadar da samar da motoci da ke amfani da lantarki da batun aikin zuwa samaniya don bincike na masu zaman kansu da samar da roket da ake sabuntawa da fafutuka ta ganin duniya ta rungumi amfani da makamashi da ake sabuntawa.
A shafin Jimploded na Facebook an rubuta wrote cewa Mista Musk na kirkirar mutum-mutumi (robot) da aka tsara shi yadda zai taimaka wa mata wajen daukar ciki. A wallafar Mis James ta kara da cewa mutum-mutumin na bukatar kwan haihuwa daga mace da maniyi daga namiji.
“Kamar yadda na ambata a baya zan ci gaba da samun bayanai daga mawallafa da (ma martani) wadanda nake karantawa:
Elon Musk kawo yanzu yana aiki wajen samar da sabbin robot wadanda za su rika daukar goyon cikin yaranku tsawon watanni tara yayin da a gefe guda za ku tafi ayyukanku. A bin da kawai ake bukata shine ke da mijinki ku ba kwayoyin haihuwarku (maniyi da kwai) za su hade su dauki tsawon watanni tara a cikin na robot.
Ga wani martani game da labarin: “Wato kamar lokacin Annabi Nuhu kenan?” Wannan shine martani da aka rubuta.
Wannan wallafa ta yadu sosai a shafin na Facebook kamar yadda za a gani a wadannan wurare(here, here, here, here, here, here.) Wannan wallafa (post) ta samu wadanda suka nuna sha’awarsu 823 (likes) da masu sharhi 496 (comments) da masu sake yadawa 57 (shares) tun bayan da aka wallafa labarin a ranar 24 ga Oktoba,2024.
Duba da yadda wannan labari ya yadu da bukatar taka tsantsan a kansa dama shi mutumin da aka ambato ya sa DUBAWA shiga aikin bincike akai.
Tantancewa
Da aka fara bincike ta hanyar amfani da wasu muhimman kalmomi sai aka samu labarai mabanbanta kan abin da ya shafi Tesla (event) a ranar 11 ga watan Oktoba, 2024 Mista Musk ya gabatar da mota mai tsarin mutum-mutumi ko robot don jigila “cyber cab” a wannan taro da ya shafi sufuri.
A bidiyon mai tsawo awa guda sun yi dogon bayani kan motar mai tuka kanta da ayyukan da robot (Optimus robots) ke iya yi da iya mu’amalarsa ta yadda yake iya taimakawa a harkokin cikin gida. A cewar Musk Optimus zai iya yin abubuwa da dama a ciki da wajen gida yace robot din zaa iya samunsa a kan farashi Dalar Amurka $30,000. Duk da wadannan bayanai bai ce robot din zai iya taimaka wa mace wajen daukar ciki ba.
Kafar yada labarai ma ta Tech Explore News ta bayyana cewa Mista Musk na aiki kan mutum-mutumi da zai taimaka kan harkokin gida yau da kullum.
“Zai iya zama malamin makaranta ko mai raino ko dan rakiyar kare ko yanke ciyawa ko ya je ya yo cefane ko kawai ya zama aboki ko ya rika kawo abin sha” kamar yadda fejin ko shafin ya rubuta. Mun leka shafin Tesla page kuma bamu ga wata sanarwa ba wacce ta nuna mutum-mutumi mai daukar goyon ciki.
Bayan amfani da manhajar hivemoderation da aiornot, mun gano cewa hoton da aka wallafa a shafin na Facebook kirkira ce kawai kuma kaso 98% da 99% sun nunar da cewa anyi amfani da kirkirarriyar basira ne ta AI kuma hoton mutum-mutumin ko robot din bai kama da Optimus robot ba na bidiyon Tesla.
Karshe
Da’awar cewa Elon Musk na aikin kirkirar wani mutum-mutumi ko robot da zai iya goyon ciki karya ce tsantsa. Bayan duba ga “We, Robots” taron Tesla da bayanai daga jami’an kamfanin, babu inda aka yi maganar ko ma aka bayyana cewa akwai wannan maganar kuma ma su kansu hotunan da aka wallafa dabaru ne kawai wanda kuma ba su yi kama da robot ko mutum-mutumi na Optimus ba.