Zargi: Wani mai amfani da shafin Facebook ya yi zarge-zarge da damda dangane da yadda kodar dan adam ke aiki da ma irin cututtukar da kan kam ta.
Uku daga cikin zarge-zargen ne gaskiya a yayin da a sauran biyun ana bukatar karin hujjoji kafin a tabbatar da sahihancinsu
Cikakken bayani
Bisa bayanan Gidauniyar Koda ta Kasa, kashi 10 cikin 100 na al’ummar duniya na fama da cutar koda (CKD) kuma miliyoyin jama’a kan rasa rayukansu kowace shekara saboda ba su da halin samun magungunan da su ka dace.
Kasidar PubMed ta ce bincike da dama wadanda aka yi a Najeriya na nuna cewa cutar na afkuwa a Najeriya da kimanin kashi 1.6 zuwa 12.4 cikin 100.
A ‘yan makonnin da su ka gabata, jaridar Tribune ta rawaito cewa babban darektan kamfanin Rencare African Limited,Mr ZahiEl-Khatib, kimanin mutane 20,000 ne ke kamuwa da cututtukan koda wadanda ba su jin magani kowace shekara.
Ranar dayaga wtan Afrilu 2022 wani sanannen dan wasa a Najeriya wanda aka fi sanin shi da sunan da ya ke amfani da shi wajen wasannin kwaikwayo da barkwancin da ya ke yi a fina-finan yarbawa, Dejo Tunfulu ya rasu a dalilin cutar kodar kamar yadda jaridar Punch ta bayyana.
Cutar koda ta dade tana kasasncewa sanadiyyar hallakar mutane da dama a kasashen da suka cigaba da ma wadanda ke tasowa dan haka ne ake cigaba da tattauna abubuwan da suka shafi kariya daga kamuwa da cutar da irin abubuwan da ke janyo ta.
Dan haka wani mai amfani da shafin Facebook Aramide Olayemi Olaleye wanda ke da shafi na musamman kankiwon lafiya maisuna Aramide Health Tips ya wallafa wadansu bayanai dangane da abubuwan da ke janyo cutar koda yana gargadin cewa lallai a kiyayi yin wadannan abubuwan
Tun bayan da wallafa wannan gargadi ko shawarwari kan abubuwan da ya kamata a guji yi dan kaucewa daga kamuwa da cutar koda mutane fiye da 200 suka nuna alamar amincewarsu, an kuma sake rabawa sau 100 a yayin da aka sami sharhi wajen 50, duk a lokacin da aka yi wannan labarin watakila yanzu wannan adadin ya fi haka.
Yawanci wadanda su ka yi tsokacin sun mika godiyar su ne ga wadadanda su ka kirkiro shafin domin mahummancin da batun ya ke da shi. Patience Ugwuegede daya daga cikin masu sharhin cewa ta yi “batu mai kara sani da illimantarwa.” Nagode shi kuma Ayan Abel Abiona addu’a ya yi yana cewa “Abu mai matukar illimantarwa. Allay ya albarkace ku.”
Yawan mutanen da suka yi ma’amala da wannan labarin na nufin cewa yawancinsu za su yi amfani da abin da aka fada ba tare da duba sahihancin labarin ba. Shi ya sa mu ke so mu tantance gaskiyar.
Tantancewa
Zarge-zarge biyar ne kuma mun dauki kowanne mun duba
Zargi na daya: Bai kamata a rike fitsari har na wani tsawon lokaci ba tare da an je an yi ba
Wannan gaskiya ne
A wani labari da muka karanta mai taken “Rike Fitsari: Akwai hatsari? Shafin Healthline wanda ke labarai masu sahihanci dangane da abin da ya sahfi lafiyar mutun ya ce wata sa’a (Ba’a cika gani ba) fitsarin na iya komawa cikin kodar mutun ta yadda zai iya haddasa cuta ko kuma ya yi wa kodar lahani.
Jaridar Medical News Today ita kuma cewa ta yi, rike fitsari na iya sa kwayoyin cuta su habaka, wannan zai iya janyo cuta a hanyar fitsarin abin da ake kira UTI a turance.
Dangane da hadarin da ke tattare da rashin zuwa yin fitsarin a kan lokaci, Dr Babaniji Omosule kwararre ne a kan koda a makarantar kodar da ake kira Worcestershire Royal Hospital wanda ya bayar da sahawarar cewa lallai ya kamata a yi fitsari a duk sadda aka ji yi domin kaucewa kamuwa da cuta.
“Yana da kyau a duk sadda aka ji yin fitsari a je a yi domin rashin yi na iya kara hadarin kamuwa da cuta, domin rashin yin fitsarin na iya hana fitsarin fita yadda ake so ko kuma toshe magudadar fitsarin a wani abin da ake kira stasis da turanci. Idan hakan ya faru yana iya janyo cututtuka.”
Dan haka bincikenmu ya nuna mana cewa zuwa yin fitsari a kan kari na kare mutun daga kamuwa da cuta. Yin fitsari na kare afkuwar abin da ake kira stasis wanda zai iya kai ga cutar koda. Dan haka wannan zarhing gaskiya ne.
Zargi na biyu : Cin gishiri da yawa na iya janyo cutar koda
Wannan gaskiya ne
Wata kungiya mai suna Action on Salt, mai binciken yadda gishiri ke tasiri kan kiwon lafiya wadda ke da mazauninta a jami’ar Queen Mary da ke Landan tare da tallafin wadansu kwararru a fanin kimiya guda 24 sun yi bayani kan dangantakar da ke tsakanin cin gishiri da koda.
A cewar wannan kungiyar, cin gishiri da yawa yana kara yawan sinadarin protein a ikin fitsari, wanda babban hadari ne ga koda. A yanzu haka akwai hujjojin da ke nuna cewa cin gishiri da yawa na iya ta’azzara cutar koda a jikin wadanda su ke da shi.
A wani labarin da jaridar Economic Times ta rubuta, Dokta Kamlesh Parikh ya yi kira ga jama’a da su kula da yawan gishirin da su ke ci.
Ya ce: “Ire-iren abincin da ke da gishiri sosai sukan sauya daidaiton sinadarin da ake kira sodium (sinadarin ne ke kula da aikin da jijiyoyi ke yi, da motsin tsoka a jiki, da kuma tabbatar da cewa jiki ya sami yawan ruwan da ya ke bukata tare da sauran sinadaran da jiki ke amfani da shi ba tare da wani ya gota wani ba) a jiki. Dan haka idan gishirin da mutun ya ci ya kara yawan sinadarin sodium a jiki zai sauya daidaiton da aka riga aka samu za’a sami matsala, domin kodar za ta fara rike ruwa. Wannan ruwan zai takurawa kodar ta yadda za ta iya daina aiki.”
A waje guda kuma, Dr Omosule ya ce da ma can cin gishiri da yawa na da lahani kuma zai iya kasancewa hadari ga koda.
Ya kuma ce cin gishiri da yawa na iya haifar da cutar hawan jini wanda shi kan shi zai iya haddasawa ko kuma ta’azzara cutar koda domin hawan jini ne kan gaba wajen haddasa cutar koda
Bisa bayanan Gidauniyar Koda ta Kasa, wadda ke mayar da hankali kan yaki da cutar, ta ce cutar suga da ta hawan jini na biyu daga cikin manyan abubuwan da ke janyo cutar koda.
Shafin WebMd shi ma ya ce cututtukan suga da na hawan jini ne mahimman cututtukan da ke janyo cutar koda.
Dan haka bincikenmu ya nuna cewa cin gishiri da yawa na da lahani ga jikin dan adam. Cin gishiri da yawa na janyo hawan jini wanda ke daya daga cikin mahimman cututtukan da ke haddasa cutar koda
Zargi na uku: Cin Jan Nama da Yawa na Janyo Cutar Koda
Wannan gaskiya ne
Gidauniyar Cutar Koda ta Kasa ta ce sinadarin protein din da ake samu daga naman dabbobi na dauke da wadansu nau’o’in da za su iya yin lahani ga koda daya a cikinsu shi ne acid wanda tamkar guba ce.
Duk da cewa yawancin gabobin jikin dan adam na bukatar sinadarin protein domin bunkasa, sabunta kansu da ma gyara wuraren da suka sami lahani, wajibi ne a hada naman da ‘ya’yan itace da kayan lambu domin su daidaita abincin.
Haka nan kuma shafin Medicinenet a rahoton wani binciken da ya yi a kasar Singapore ya ce cin jan nama da yawa na iya kai ga cutar koda. A cewar rahoton, cin jan nama musamman namar alade na janyo cutar koda. Mun kuma sake gani wani rahoton da ya yi wannan bayanin a shafin WebMD.
Shafin Piedmont, shi ma ya goyin bayan hakan inda ya ce jan nama, da madara da dai sauran kayan da ake samu daga dabbobi na yin lahani mai muni a kan koda saboda su na mata wuyar sarrfawa.
A waje guda kuma Dr Omosule ya ce ba lallai ne cin jan nama da yawa ya janyo cutar koda ba amma kuma zai iya janyo cutar zuciya saboda yana iya kara yawan wani sinadarin da ake kira Cholesterol (wanda ake samu a jinin mutun wanda kuma ke taimakawa wajane ingantawa da kuma gina kwayoyin halitta amma kuma idan ya yi yawa a jiki yana iya kawo tangarda) idan ya yi yawa yana iya kaiwa ga ciwon zuciya
Likitan ya kuma kara da cewa yawancin masu cutar koda su na da cutar zuciya
Bincikenmu ya nuna mana cewa cin nama da yawa na iya janyo cutar koda dan haka wannan zargin gaskiya ne.
Zargi na hudu: Shan kofi da yawa na janyo cutar koda
Wannan na bukatar karin hujjoji
Kungiyar Fresnius Kidney Care wadda ke taimaka wa wadanda ke fama da cutar koda ta ce Kofi ba zai iya wani lahani a kodar dan adam ba idan har kadan kadai ake sha. Shafin ya bayyana cewa Kofi na iya kara hawan jini, da yawan jinin da ke yawo a jiki ko kuma ma ya kuntatawa koda, sa’annan kuma ana yawan danganta samun duwatsu cikin koda da shan kofin.
Kamar yadda jaridar Independent ta rawaito akwai wadansu kwayoyin jini da ake dangantawa da shan kofi wadanda masu bincike a makarantar kiwon lafiya ta John Hopkins Bloomberg su ke zargi cewa wadannan kwayoyin na iya hadasa cutar koda a jikin dan adam
A cewar Gidauniyar Koda ta Kasa, bincike ya nuna cewa shan kofunan kofi 3 zuwa 4 a rana na iya kara hadarin kamuwa da cutar kodar ko kuma ma ya rage kargin aikin kodar. Dan haka yana da kyau a rage yawan kofin da ake sha.
Binciken da Cibiyar Lafiya ta Kasa ta gudanar ya nuna cewa lemun kwalba na janyo cutar suga, hawan jini, da kidney stones wadanda dukansu kan kai ga cutar koda.
Dr Omosule ya ce a iya sanin sa, babu wata hujjar da ta nuna dangantaka a tsakanin shan kofi da cutar koda. “Akwai bincike da dama da suka yarda da hakan akwai kuma wadanda suka karyata.” ya ce
Binciken da aka yi kan kofi da lemun kwalba duk sun nuna cewa akwai hadarin samun cutar koda idan aka rika shan su fiye da kima amma kuma babu wata hujja taka-mai-mai da nuna alakar da ke tsakanin su da cutar kodar.
Zargi na biyar: Rashin shan ruwa na iya janyo cutar koda
Wannan na bukatar karin hujjoji
Gidauniyar Koda ta Kasa ta ce rashin ruwa a jiki na iya janyo lahani a koda, dan haka ake bayar da shawarar cewa a rika shan ruwa sosai musamman a lokutan da ake aiki ko motsa jiki a yanayi mai zafi. A cewar gidauniyar akwai binciken da suka nuna cewa rashin ruwa ko da ba a kai – a kai ba ne yana iya lalata koda baki daya.
Norman Urology, kungiyar likitocin da suka kware wajen duba cututtukan da suka shafi mafitsara sun amince da bayanain gidauniyar Kodar ta Kasa. A cewar Norman Urology rashin ruwa a jiki na iya kashe kodar ko kuma ya hana ta aiki yadda ya kamata wanda zai iya kai ga mutuwar kodar baki daya.
Kidney Research UK, masu bincike kan Koda sun ce shan ruwa sosai a rana yana da mahimmanci sosai ga lafiyar koda. Kungiyar ta ce shan ruwa da yawa na iya rage hadarin kamuwa da cutar koda domin ruwan zai taya kodar wajen cire dukkan abubuwan da ba ta bukata musamman irin su gishiri da urea.
Shafin Mayo Clinic shi ma ya bayyana cewa rashin ruwa a jiki na iya janyo matsaloli masu hadarin gaske wadanda su ka shafi mafitsara da kodar. Kungiyar ta yi bayanin cewa idan har aka cigaba da samun lokutan da jiki ya kan rasa ruwan da ya ke bukata zai iya kai wa ga cututtukan mafitsara, duwatsu a cikin koda da ma mutuwar kodar baki daya.
A cewar kwararru kan kodar, rashin shan ruwa yadda ya kamata na iya tasiri a kan kodar. “Rashin shan ruwa na tasiri sosai a kan koda shi ya sa mu kan shawarci mutane su rika shan ruwa sosai.
A hirar da muka yi da wani kwararre kan kodar da ma binciken da muka yi a shafukan kwararru sun nuna mana cewa rashin ruwa a jiki ko kuma dehydration kamar yadda ake kiran shi da turanci ya kunshi rashin shan ruwa zuwa matsayin da jikin dan adam ke bukata, kuma hakan na da jadari dan yana iya janyo matsaloli a mafitsara da ita kodar kanta.
A Karshe
Bincikenmu ya nuna mana cewa uku daga cikin zarge-zargen ne gaskiya, sauran biyun babu cikakken bayani ko hujjar da zai tabbatar da sahihancinsu.