|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: An yada wani labaria kafafen sada zumunta da ke cewa Majalisar Tarayya ta amince da ƙirƙiro sabbin jihohi 12.

Hukunci: Yaudara ce. Wannan labari ba gaskiya ba ne, majalisa na tattaunawa ne, amma ba a kammala kuma ba amince da sabbin jihohi ba.
Cikakken bayani
A ‘yan kwanakin nan, an sake yada labarin cewa majalisar tarayya ta amince da ƙara sabbin jihohi a Najeriya, kamar yadda aka yi ta rade-radin yi a can baya. Sai dai wannan karo labarin da ke yawo shine har majalisa ta amince da kirkiro jihohi 12.
Labarin na nuna cewa jihohi biyu ne za a kirkiro daga kowane yanki cikin yankuna 6 na Najeriya.
Wannan ya haifar da ce-ce-ku-ce da buƙatar neman bayani a tsakanin jama’a, musamman ma waɗanda ke fargabar cewa za a raba ƙasar.
Domin tabbatar da sahihancin labarin. DUBAWA ta yi bincike domin gano gaskiya..
Tantancewa
Wani rubutun bayani da DUBAWA ta wallafa a ranar 24 Fabrairu, 2025, an yi bayani kan yadda tsarin ƙirƙirar jihohi yake a Najeriya, inda aka jaddada cewa Majalisa ba za ta iya ƙirƙirar sabbin jihohi da kanta ba.
Menene Tsarin doka?
A ƙarƙashin Sashe na 8(1) na Kundin Mulkin 1999, don a ƙirƙiri jiha sabuwa, ana buƙatar:
A sami aƙalla rinjayen ƙuri’u biyu ta uku (2/3) daga dukan ‘yan majalisa a yankin da za a kafa jiha;
A gudanar da zaben jin ra’ayin jama’a (referendum) wanda dole ne sami rinjaye sosai;
Daga nan sai a mika sakamakon zuwa majalisun jihohin Najeriya duka su amince, sannan su kada kuri’a don amincewa da bukatar kirkirar jihohin.
Menene Majalisa ta yi a zahiri?
A halin yanzu, Majalisar Tarayya ba ta yanke hukunci kan ƙirƙirar jihohi ba.
Kwamitin Majalisar Dattawa mai nazari kan Kundin Tsarin Mulkin 1999, wanda aka kafa a ranar 14 ga Fabrairu, 2024, ya fara gudanar da zaman jin ra’ayin jama’a a shiyyoyi daban-daban na ƙasar.
A halin yanzu, kwamitin ya karbi buƙatu 32 daga sassa daban-daban na ƙasar nan da ke neman a ƙirƙiri sababbin jihohi, inda yankin Arewa maso Yamma ke da buƙatu 6, Arewa ta Tsakiya 8, Arewa maso Gabas 6, Kudu maso Gabas 5, Kudu maso Kudu 6, sai Kudu maso Yamma da ke da buƙatu 4.
Shugaban kwamitin, Sanata Michael Opeyemi Bamidele, ya jaddada kudurin Majalisar Dattawa na gudanar da wannan aikin cikin gaskiya da kuma bada dama ga kowa ya bayyana ra’ayinsa.
A karshe
Labari ba gaskiya ba ne, majalisa ba ta yanke hukunci kan ƙirƙirar sabbin jihohi ba har zuwa ƙarshen matakai da ake buƙata.




