Zargi: Wani mai amfani da shafin Facebook ya ce Mike Tyson ya mutu

Sakamakon Bincike: KARYA! An gyara hoton da aka yi amfani da shi ne ba hoton gaskiya ba ne, kuma Mr Tyson ya yi bayani a kan shafin shi ba da dadewan nan ba.
Cikakken bayani
Michael Tyson, wanda aka haifa ranar 30 ga watan Yunin 1966, dan asalin Amurka ne kuma tsohon dan wasan dambe ko kuma boxing, sana’ar da ya yi daga shekarar 1985 zuwa 2005. Sadda ya fara wasan damben an rika mi shi lakabi da sunayen da suka hada da “Iron Mike” da “Kid Dynamite” kafin daga baya aka fara kiransa “The Baddest Man on the Planet,” wato mutumin da ya fi mugunta a duniya. Ana wa Tyson kallon daya daga cikin shahararrun wasan damben boxing. Bayan da ya yi nasara, babu wanda ya iya kalubalantar sa daga 1987 zuwa 1990.
Da ya fara barin filin wasan na boxing, Mike Tyson ya kuma sake samun wasu karin nasarori a fannoni daban-daban. Misali yana da wani shirin podcast mai suna “Hotboxin w/Mike Tyson,” kuma ya shiga fagen fina-fiani da kasuwanci. Duk da cewa a shekarar 2005 ya yi ritaya daga wasan damben boxing a hukumace, Tyson ya shiga an dama da shi a wani wasan nishadin da aka yi a shekarar 2020
Sai dai, Honduras Radio, wani shafi a Facebook ya wallafa labarin cewa Tyson ya mutu. Masu izinin rubutu a shafin sun ce sun sami tabbacin cewa tsohon dan wasan damben boxing din ya cika ne ranar 14 ga watan Agustan 2023.
A shafin tsokaci, mutane da yawa sun bayyana shakkunsu dangane da sahihancin batun. Vixie Yawii ta rubuta, “Shin wannan gaskiya ce kuwa? Ba na tsammani.” Wani kuma mai suna Yolany Parenteau shi kuma shawara ya bayar ya ce ya kamata a rika tantance gaskiyar bayani kafin a wallafa.
Tuni da labarin ya fara daukar hankali sosai bayan da aka wallafa ranar 14 ga watan Agustan 2023.
Sarkakiyar da wannan batun ke da shi da mutanen da labarin ya shafa ne ya sa DUBAWA gudanar da binciken gano gaskiya.
Tantacewa
Mun fara lura cewa labarin na dauke da adireshi, dan haka sai muka latsa adireshin mu ga inda zai kai mu. Wannan sai ya kai mu wani shafin da ya wallafa dogon tarihin tsohon dan wasan damben boxing din, nasarorinsa da wuaren da ya gaza ba tare da wallafa abun da ya yi sanadin mutuwar da ake zargi ya yi ba. Daga nan ne muka yi tunanin cewa wannan labarin bogi ne.
Mun gudanar da bincke kan hoton da aka yi amfani da shi a shafin, daga nan ne muka gano na ainihin a shafin jaridar The Onion, wata kafar yada labaran Amirka.
Daga nan ne muka je shafinsa na Instagram @miketyson inda muka ga cewa ya wallafa bayani dangane da sabon shirin da ya yi a podcast din shi na 29 ga watan Agustan 2023. Kuma daga bidiyon Tyson na cikin koshin lafiya.
Daga karshe, idan har mutum kamar Tyson wanda ke idon jama’a kusan ko da yaushe ya mutu, babu shakka labarin zai dauki hankali sosai kuma za’a ji labarin a kafofin yada labarai, sai dai babu karar da ta yi wannan labarin.
A Karshe
Tyson bai mutu ba. Hoton da aka yi amfani da shi a bayyana mutuwarsa ma an gyara ne ba na ainihin ba ne. Karin binciken da muka yi ya nuna cewa ya wallafa abubuwa a shafukansa na soshiyal mediya ko bayan da aka yi zargin ya mutun.