African LanguagesFeaturedHausa

Muhimmancin Dutsen Dala a tarihin birnin Kano

Getting your Trinity Audio player ready...

“HANGEN DALA BA SHIGA BIRNI BA”: Wannan wani karin magana ne da ke zama sananne idan ana maganar birnin Kano. Ko a wasu lokutan ana wa jihar ta Kano wacce ke a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya kirari da “Kano mai Dala da Goron Dutse” wadanda ke zama sanannu duwatsu a tsakiyar birnin na Kano, kasancewar dukkaninsu suna cikin badala ko ganuwa da ta zagaye birnin na Kano. A shekaru can baya kasancewar babu gine-gine kafin mutum ya isa birnin na Kano, yana iya hangen dutsen na Dala wanda kuma tafiya ce jajawur kafin kaiwa gareshi. Binciken kwararru ya gano cewa sama da shekaru 1000 al’umma sun rayu a kan dutsen na Dala Makera masu aikin kere-kere da karafa.

Jihar Kano dai na da fadin kasa murabba’in kilomita 21,000 ta yi iyaka da Jigawa daga yankin arewaci da gabashinta, haka kuma ta yi iyaka da jihar Kaduna daga Yamma da Kudu maso Yamma daga can kuma Kudu maso Gabashi ta yi iyaka da jihar Bauchi.

Dutsen Dala tsauni ne mai tsayi da ya kai mita 534 wato kafa 1,753, akwai matakala 101 daga kasa da ake takawa zuwa saman wannan dutsen da ke da muhimmin tarihi, kuma wannan matakala daga baya aka gina ta, kuma dutse ne da ke zama ginshiki a tarihin al’adun al’ummar Kano da ke magana da harshen Hausa  me kuma yawan jama’a da suka haure miliyan 16 a arewacin na Najeriya, harshen kuma da ake samun masu jin Hausa ko magana da shi a sassa daban-daban na duniya.

Harshen Hausa harshe ne fitacce da ake amfani da shi wajen yada bayanai ko labarai a kafafan yada labarai kamar na Burtaniya (BBC) da Jamus-Deutshe Welle (DW) da Radio France (RFI) da gidan rediyon kasar Sin (CRI) da sauransu.

  

Muhimmancin Dutsen Dala a tarihin birnin Kano

Malam Idris Dala daga hagu yana bayani ga wani bako daga kasar Tanzaniya a gefen dutsen Dala: Hoto: DUBAWA- Yusuf Nayaya 

Masana tarihi dai na bayyana cewa tarihin Kano ba zai cika ba, ba tare da bayyana dutsen Dala ba, wanda asalin al’ummar cikin birnin na Kano a nan ne suka fara zama kafin daga bisani suka fantsama zuwa wasu sassa. A cewar masana tarihi irin su Muhammad Idris Dala da ke zaune a unguwar ta Dala  “Ai asalin Kano daga nan ta fara, wanda al’ummar Maguzawa ke zaune a saman Dutsen suna harkokinsu da Ibadarsu ta tsafe-tsafe, suna da wata Aljana da suke bautawa ana kiranta da suna Tsumburbura, akwai kuma hadiminta Barbushe, shi ke zuwa ya karbo sako daga wannan Aljana sai ya zo ya gaya wa mutanen, abin da take bukata ko wata dabba da take so a yanka sai a yanka mata, su kuma suna ganin biyan bukatarsu ” a cewar Idris Dala

Dutsen Dala wuri ne da al’umma suka zauna sama da shekaru 1,000 kamar yadda aka ga shedun kwararrun masana na cewa al’umma sun zauna a wannan yankin tun a karni na 10.

A karni na 14 dutsen na Dala ya zama muhimmin wuri a daular Hausawa wanda ke daya cikin masu karfin iko a yankin Afurka ta Yamma a wancan lokaci. 

Muhimmancin Dutsen Dala a tarihin birnin Kano

 Wani yanki na birnin Kano daga saman dutsen Dala: Hoto: Yusuf Nayaya DUBAWA 2025

Muhimmancin wuraren da ake gani daga saman dutsen Dala

Daga saman na Dutsen Dala mutum zai iya kallon birnin Kano ta fuskoki da dama, gabas da yamma, kudu da arewa ga misali akasarin unguwanni da ke birnin na Kano, da wasu fitattun wurare kamar babban masallacin Juma’a na birnin Kano da gidan Sarkin Kano da gidan Isyaku Rabiu da filin tashi da saukar jiragen sama na Malam Aminu Kano da unguwar Dala da Kofar Mazugal da kasuwar Kofar Ruwa da Gwammaja, karin wasu muhimman wuraren kuma sun hadar da Kasuwar Kurmi: A farkon karni na 19 cikin masu leken asiri da Burtaniya ta aiko Kano sun hadar da Hugh Clapperton da Henry Barth, wadannan Turawa sun ziyarci birane da dama masu sahara da masu yabanyar bishiyu a kasashen Afurka kuma kowannensu ya ba da bayani kan yadda ya kalli wadannan kasashe ga abin da Hugh Clapperton ke cewa bayan ziyartar Kano:

“The great emporium of kingdom of Hausa” Babbar Daular kasuwancin kasar Hausa”. Hakanan ya kara da cewa:  “Well supplied with every necessary luxury in request among people…there is no market in Africa so well regulated.”Kasuwa da aka tanadar mata duk abubuwan da mutum ke bukata, babu kasuwa kamar ta da tsari a Afurka.

Wannan kasuwa dai mai tarihi an kafa ta tun a karni na 15, ta kasance babbar kasuwa da ke samun baki na zuwa cin kasuwa daga sassa daban-daban na Afurka ta Yamma. Kasuwar ta kasance ta daban tsakanin takwarorinta a Kano, kasancewar ta taba fannoni da dama na rayuwa, a wannan kasuwa ne za ka samu kayan da aka hada da fata mafi kyau kamar takalmi da jaka da tabarmar fata da sauran kayan ado na fata da sauransu. Yanayin kasuwanci a kasuwar kuma tsakanin mai siya da mai siyarwa ne, kuma kaya na da sauki. Wadanda ke zama baki daga wasu kasashen duniya kamar Burtaniya da Jamus da Masar da sauransu su kan nemi mai fassara wanda ke masu jagoranci ko tafinta idan sun je wannan kasuwa don siyan kayayyaki a lokacin ziyara zuwa Kano.

Muhimmancin Dutsen Dala a tarihin birnin Kano

Wani yanki na kasuwar Kurmi  Hoto: Yusuf Nayaya

Wannan kasuwa ta kuma kasance babbar cibiya da ke hada mutane daga wadannan kasashe inda suke zuwa siyan kayayyaki su kuma siyar da nasu kayayyaki da suka zo da su daga kasashen su. Har yanzu a wannan kasuwa za ka samu kaya na gargajiya ga misali kayan kore da kayan hawan dawaki da kayan kamshi da karo da tafarnuwa da citta da kayan rubutu na Kur’ani da kayan sawa irin na gargajiya da na zamani da sauransu.

Mulkin mallaka

A lokacin da Turawa suka shiga Kano a 1903 jihar Kano ta kasance lardi mai karfin fada aji a wasu yankuna kamar Daura da Katagum da wasu yankuna na jihar Jigawa da Bauchi da Kaduna da Katsina.

A lokacin na Turawan mulkin mallaka wannan Dutsen Dala ya kasance muhimmin waje kasancewar ya zama wani waje da sojoji suka girka cibiyarsu ana kuma gudanar da harkoki na mulki.

Ala’adu da addini

Dutsen Dala a samansa akwai wurin bauta da asalin mazauna Kano wadanda Maguzawa ne ke taruwa suna gudanar da bautarsu ta Maguzanci. Duk da cewa wurin na zaizayewa tsawon shekaru har yanzu baki da masu bin tarihi na zuwa bakin wajen su ga yadda kogon yake.

Muhimmancin Dutsen Dala a tarihin birnin Kano

Malam Idris Dala a bakin Kogon Tsumburbura saman Dutsen Dala inda Barbushe ke karbo sako Hoto: Yusuf Nayaya

Har ila yau wannan dutse na Dala ya ci gaba da rike kambunsa na gudanar da abubuwa na al’adu kuma har gobe mutane daga sassa daban-daban na duniya kama daga Turawa zuwa bakar fata na zuwa ziyara wannan dutse saboda muhimmancin tarihinsa a Kano. 

A kowace shekara lokacin Mauludi wato bikin Tunawa da ranar da aka haifi Annabi Muhammadu S.A.W, wanda ke zuwa duk ranar 12 ga watan Rabi’ul Auwal,  idan ranar ta zagayo wato bayan kwanaki bakwai daga waccan rana ana kiranta da ranar suna kuma wannan rana ce ake kiranta da sunan ranar Takutaha  a wannan rana har gobe za ka ga dubban mutane na yin kwalliya su kai ziyara kan Dutsen Dala a je da abinci da abin sha ayi wasanni da wake-wake zuwa yamma a sauko kowa ya kama gabansa.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Translate »