African LanguagesHausa

Obi bai yi nasara kan Tinubu da Shettima a kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa kamar yadda wata jarida ke zargi ba

Zargi: Obi ya yi nasara kan Tinubu, Shettima a shari’ar zaben shugaban kasa. 

Sakamakon Bincike: Babu cikakkiyar gaskiya. Jaridar ta dauki wani bangare ne na abun da ya faru a kotu ta bayyana ba tare da yin matashiyar da ya kamata ba. Kuma yin hakan na iya yaudarar jama’a su ga kamar gaskiya ne alhali ba haka ba ne. 

Cikakken bayani

Yayin da ake sauraron shari’ar da ke gudana dangane da korafe-korafen da aka gabatar dangane da zaben shugaban kasa a Abuja (Laraba 6 ga watan Satumba) domin bayar da labarin da kowa ke jiran ji, jaridar P.M News a shafinta na X(wanda ake kira twitter daa) ta yi zargin cewa jam’iyyar LP ta yi nasara kan Bola Tinubu da mataimakinsa Shettima a PEPC (Wato shari’ar zaben shugaban kasa) 

“Labari da dumi-dumi: Peter Obi ya doke Tinubu, Shettima a PEPC,” taken labarin na su ya bayyana.

Alkaluman yawan lokutan da aka kalla labarn ya kai 42,000 views, akwai mutane 211 likes wadanda suka latsa alamar like, 46 sun sake raba labarin, yayon da 70 suka yi amfani da labarin wasu uku kuma suka adana.

Masu amfani da X sun yi suka sosai dangane da yadda suka yi amfani da irin wannan taken. Presh (@IamPresh90) ya rubuta, “ Kuna neman jama’a ne kawai a shafinku da irin wannan taken,” yayin da YettyO (JP) (@YettyO_jp) lkuma dariya ya yi yana kiran batun ba’a

Sarkakiyar da batutuwan shari’ar ke da shi da ma shakkun da masu amfani da shafin suka bayyana ne ya sa muka dauki nauyin tantance batun.

Tantancewa

Mun fara da zuwa shafin dan karanta cikakken labarin, wanda ya yi bayani dangane da batutuwa biyu dangane da Obin da kwamitin alkalan ya nuna rashin gamsuwar shi da su.

Na farko shi ne matsayin Mr Obi na mamba a jam’iyyar LP, na biyu kuma dangane da ko korafin na da sahihanci ganin yadda bai hada kai da dan takarar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ba.

Yadda aka kira bayyana rashin gamsuwa nasara ba wani abu ba ne illa shakiyanci.

Kafofin yada labarai sun watsa zaman kotun kai tsaye kuma kafafen da suka yi hakan sun hada da Premium Times, The Cable, da Channels Television. Duk wadanda suka kalla sun ga cewa kotun ta bayyana rashin gamsuwarta da yadda dan takarar na jam’iyyar LP ya shigar da kararsa daban da na Atiku Abubakar wanda shi ne ya zo na biyu a zaben, ta kuma ce karar ba za ta iya tsayawa da kanta ba.

Dangane da batun hada kai da dan takarar PDP din ne, daya daga cikin alkalai biyar din da suka kasance a kwamitin, Abba Mohammed ya ce ba dole ba ne dan mai korafin ya hada kai tare da dan takara irinsa wanda shi ma ya rasa zabe kamarsa wajen shigar da kara.

Mr Mohammed ya kara da cewa abun da ya zama tilas shi ne mai korafin ya hada kai da mutumi ko jam’iyyar da ta yi nasara a zaben da hukumar da ta gudanar da zaben a matsayin bangarorin korafin da ya ke shigarwa

Dangane da batu na biyu wanda ya shafi kasancewar Mr Obi mamba a jam’iyyar LP, Mr Mohammed ya ce jam’iyya ce kadai ke da hurumin bayyana mambobinta kuma babu wani mutun ko hukuma da zai iya kalubalantar wannan.

A karshe

Rahotannin da muka samu daga dandaloli masu sahihanci wadanda suka rika wasa zaman kotun kai tsaya sun nuna cewa taken da aka sa a labarin na iya yaudarar jama’a comin ba’a bayyana cikakken gaskiyar ba.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button