African LanguagesHausa

Reshe guda na cocin RCCG, ba cocin baki daya ya kaddamar da shafin da ke taimaka ma masu sha’awan samun saurayi ko budurwa ba

Zargi: Wani labarin da ya bulla a shafin twitter na zargin wai cocin RCCG ya kadamar da shafin yanar gizon da ke taya maza da mata samun masoya.

Wani hoton da ya fara bulla a shafin today.ng na zargin wai cocin Redeemed Christian Church of God ya kaddamar da shafin da zai taimaki maza da mata su sami masoya.

Wannan labarin ya janyo cece-kuce a shafin twitterinda wasu suka fada yin rajista a shafin sun rubuta rahotannin barkeanci.

Wani mai mai mafani da shafin tiwita Daniel Regha (@DaniekRegha) ya soki wannan mataki yana cewa da matsalar rashin tsaron da ake fa ma da ita wannan matakin ba shi da hikima. Ya kuma yadda cewa za’a yi amfani da wannan kafa a yaudari mutane da yawa dan ba kowa ne zai kasance salihi ba.

Wata mai amfani da shafin tiwita kuwa mai sun a Omotara Akanni (@_theladymo) sunanta da shekarunta da lambar wayarta ta rubuta ta wallafa.

Cece-kucen da ya biyo bayan wannan batu ya sa muka yanke shawarar binciken gaskiyar lamarin

Tantancewa

Dubawa ta fara da binciken tushen labarin inda ta gano cewa jaridar Today (@todayng) ce ta fara wallafa labarin ranar alhamis 2 ga watan Disemba 2021 da karfe 1:37. Wannan ya nuna mana cewa jaridar Today ce mafarin labarin.

A shafin tiwita an sake wallafa labarin har sau 819, wasu 1,234 sun yi amfani da labarin sun yi tsokaci a yayin da wasu 1,422 suka nuna alaman gamsuwa da labarin wato “like”. Today ta kuma sanya adireshin inda mutun zai iya karanta cikakken labarin a jaridar ta. 

Da muka yi binciken mahimman kalmomi, binciken ya sake kai mu shafin jaridar Today, zuwa labari mai taken RCCG ya kaddamar da dandalin masoya a yanar gizo.” A cewar wannan rahoton. Reshen City of David, a karkashin jagorancin Pastor Idowu Iluyomade ya kaddamar da shafin da zai taimakawa wadanda suka manyanta wajen samun masoya.

Sauran shafuka irin su Channels da jaridar Punch su ma sun wallafa labarin. Sai dai gidan talbijin na Channels ya yi amfani da take daban mai cewa, “Babu aure a sama: Cocin RCCG ya kaddamar da shafi mai sadar da masoya”

Rahoton ya kuma buba cewa daya daga cikin cocunan RCCG ne ya kaddamar da shafin ba dungun cocunan da ke kasar ba.

Domin wannan yawan banbancin na kanu, Dubawa ta tafi shafin RCCG amma ba mu ga wani abu mai kama da haka ba. Dan haka sai muka tuntubi lambar wayar da muka gani a shafin ta whatsapp wanda ya tabbatar mana cewa lallai daya daga cikin cocunan da ke Legas ya yi haka

“Ina kwana? Wannan gaskiya ne?” sakon ya fada

Daga nan mun sake zuwa shafin da jaridar Punch ta ambata sai mu ka ga cewa an sanya wata sanarwar da ke cewa an daina rajista a shafin samun mosayan.

A karshe

BIncikenmu ya nuna mana cewa daya daga cikin rassan cocin RCCG ya kaddamar da shafin da zai sada masoya sai dai ba duka cocin ne ta yi haka ba. Dan haka kanun labaran sun yaudari jama’a tunda ba su bayar da cikakken labarin ba.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button